Oscar Korbla Mawuli Awuku, mai shekara 23, da ke karatu a Jami’ar Takoradi a yankin Yammacin Ghana, ya shafe shakara biyar yana zane-zane a jikin masu tallar kayan kawa.
Aiki ne da yake bukatar matukar kwarewa da himma da jajircewa don fitar da basirarsa.
A cikin kasa da sa’a daya yake iya yin zane a jikin masu tallar kayan kawa a sura dabam-dabam a hoto mai motsi da marar motsi.
Oscar ya shaida wa TRT Afrika cewa “idan da hali ana so zane a jikin masu tallar kayan kawar ya zanu radau – idan da hali ma su dauke numfashinsu.
Batu ne na yin sa yadda ya kamata, don haka ba zan yi gaggawar yin kuskure ba,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
A karni na 18 da 19 da na 20, zane a jikin mutane daidai yake da bayyana yanayin kayan gwaraza ko wata alama ta mazantaka da mulki da suke hade da kyau da bayyana al’adar mutum.
Oscar ya fara bincike a kan zane a jikin mutanen Afrika a shekarar 2018 bayan da ya yi waya da wani mai bayar da umarni na bidiyoyin waka, wanda yake neman mai zanen da zai kirkirar masa zane a jikin masu tallar kawa da za su bayyana a matsayin ‘yan gidan sarauta da kuma masu gadi, a wata waka ta bidiyo da mawakiyar nan ‘yar Ghana, Becca ta yi.
“Daraktan wakar, Abbas ya nemi na sauya mutanen cikin wakar ta fito da su a matsayin ‘yan gidan sarauta ta hanyar yi musu fenti sosai. A lokacin ne na fara yin bincike kan wannan lamarin sosai,” ya ce.
“Abin ya burge ni gaya sannan kuma na ji takaicin yadda yayinsa yake gushewa. Bayan kammala nadar bidiyon, sai na yanke shawarar sadaukar.
Asalin zanen jiki a Afirka
Tarihi shi ne shaidar da ke bayyana cewa ana yin zane-zane a jiki sosai a Afirka. Wasu misalan su ne na kabilun Khosa da ke yankunan gabashin Afirka ta Kudu, wadanda aka shafe fuskokinsu baki daya da farin fenti (saboda farauta da ibadar addininsu).
Sannan akwai na yankin Igbo a gabashin Nijeriya, wadanda ake yi wa jikinsu fentin baki mai suna “uli”.
Karin wani misalin shi ne na kabilun da suke Arewacin Afirka kamar Aljeriya da Moroko da Libiya da suke yin kunshi a hannu da kafa musamman ga amare.
“Yin zane a jiki na nufin abubuwa da dama ga al’adu daban-daban,” in ji Elijah Sofo, wani malami a fannin zane-zanen fasaha na Jami’ar Takoradi.
A tarihance a kasar Ghana alal misali, zane a jiki a al’adance yana nuna alamar cewa yara mata sun fara hawa matakin balaga zuwa zama manyan mata.
“Muna kiran hakan al’adar dipo. Zanen hanya ce ta yi wa jikinsu ado da kuma kare su daga bala’i.
Amma a yanzu yawancin al’adun Afirka ba sa bai wa zanen muhimmanci saboda sauyawar zamani. A misali a gabashin Nijeriya, da wuya a yanzu ka ga yarinya matashiya da zanen “uli”.
Wannan koma baya ne sosai ga al’adu a fadin duniya,” in ji Elijah. “Zuwan intanet da sauran abubuwan da ke yi wa al’ada kutse sun sa muna rabuwa da asalinmu da abubuwan da muka gada.
“Abin yana mana ciwo sosai. Ba matsala ba ce don al’adu sun cakuda, amma abin haushi ne a ce al’adun sun bace bat.”
A wannan zamanin kuwa zanen jiki da ake kira tattoo shi ne abin yayin. A yayin da ake fargabar gushewar al’ada, Oscar na fatan ba kawai a kare zanen jiki zai tsaya ba, har ma da tabbatar da cewa hakan ya zama abin tattaunawa a tsakanin matasa.
“Mafi yawan ayyuka ne a kan ‘yan uwantaka ne da goyon baya da kuma bukatar ‘yan Afirka su zama masu kare muradun junansu,” ya ce.
A ta bakin Oscar, matasan Afirka na cikin yanayi daban-daban. Tattalin arzikin kasashe da dama ya tabarbare, sannan ana yawan samun karuwar kashe kai. “Ina son zanena ya zama silar kawo gyara da fata na gari.”
Akwai zane-zanen Oscar da dama a cibiyar Melrose da ake baje kolin zane-zane a Afirka ta Kudu, da suka hada da Esther Mahlangu da Farfesa Pitika Ntuli da Mam Noria Mabasa da kuma Willie Bester.
Shafin inatent na Melrose ya yi Magana a kan muhimmancin ajiye zane-zanen nasa a wajen, yana cewa “suna wakiltar masu zane-zane masu tasowa ne da suke amfani da aikinsu wajen bayyana muhimmancin batutuwan a nahiyar Afirka da ma duniya baki daya.
“Na ji matukar dadi a lokacin da cibiyar ta tuntube ni. Har yanzu na kasa gaskata hakan,” in ji Oscar.
Baya ga zane-zanen jiki, Osacr ya yi ayyuka da dama da suke bayyana basirarsa sosai musamman a kan bidiyon mawaka kamar su Davido dan Nijeriya.
Sai dai duk da irin nasarar da ya samu, Oscar y ace da shi da masu tallar kayan kawarsa har yanzu da aiki a gabansu na shawo kan dumbin kalubalen da suke fuskanta.
“Abin takaici ne yadda har yanzu wasu matasan bas a iya fahimtata da aikina, abin da ke saka su cin zarafina a intanet.
“Ana cin zarafi da wulajanta masu tallar kayan kawata, inda da yawnsu kan kira ni suna kuka tare da rokona kan na cire hotunansu saboda sukar da ake musu.”
Oscar ya sha alwashin zai ci gaba da Magana da yaren da shi kadai ya iya duk da matsalolin. “Ina son ‘yan Afirka su dinga yabon kansu da godiya ga yadda suke a matsayinsu na ‘yan Afirka,” ya ce.
Matashin mai zanen yana tattaunawa da wani wajen bake kolin hotuna a AFirka ta Kudu don yin wani biki na nuna kimar bakar fata.
Daga ganin irin zane-zanen fenti da ya yi a jikin wasu masu tallar kayan kawa, z aka gane cewa lallai wannan matashi Osacr zai ajiye tarihi sosai a fannin zane-zane.