Kasar Afirka ta Kudu ta yi bikin ranar al'adu ta 2023 wadda ake yi shekara-shekara. Ranar Al'adu ta fado a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba, kuma an yi bikin cikin tufafin kwalliya. Biki ne na nuna arzikin al'adun kasar.
Jami'ai sun nemi 'yan Afirka ta Kudu su girmama al'adunsu mabambanta. Bikin na shekara-shekara ranar hutu ce, kuma wata dama ce ta kulla alaka da al'adunsu, don inganta hadin-kai da kare Afirka ta Kudu a matsayin mallakin al'ummarta.
A jawabinsa, wani dan kasar, David Mabuza ya bayyana bikin a matsayin wani "tarihi na musamman da yake karfafa al'ummomi da dama su rungumi hadin-kai, da nuna cewa bambancin al'ada wata dama ce mai kawo cigaba, ba rabuwar kai ba.''
A tarihi, ana kiran ranar da Ranar Shaka, saboda mutane suna tunawa da sarki Zulu, Shaka, na kudancin Afrika, a ranar da ake ganin ita ce ranar da ya mutu a shekarar 1828.
Wani kudurin dokar kafa Ranakun Hutu na kasar da aka gabatar a majalisar dokokin Afirka ta Kudu, bayan mulkin wariyar launin fata a shekarar 1996, bai hada da ranar 24 ga Satumba ba.
Jam'iyyar Inkatha Freedom Party (IFP), wata jam'iyya a kasar da take da mambobi daga kabilar Zulu masu yawa a majalisar dokokin Afrika ta Kudu, ta yi watsi da kudurin dokar.
Bayan tattaunawa da gwamnati, an yi wa kudurin kwaskwarima kuma aka zartar da shi ya zama doka, inda daga ake kiran ranar da "Ranar Al'adu", wadda aka ayyana a matsayin ranar hutu.