A farkon wannan watan, Majalisar Dokokin Afirka ta Kudu ta amince da gyara kundin tsarin mulkin kasar domin amincewa da bebanci a matsain yaren kasar na goma 12.
Dokar za ta iya bai wa yaren bebaye din matsayi daya da sauran yarukan gwamnatin kasar – Sepedi da Sesotho da Setswana da siSwati da Tshivenda da Xitsonga da Afrikaans da English da isiNdebele da isiXhosa da kuma isiZulu.
Rabin al’ummar kasar na amfani da harshen isiZulu da isiXhosa da kuma Afrikaans a matsayin harshen uwa, yayin da Ingilishi ya kasance na hudu duk da cewa shi ne aka fi amfani da shi a harkar gwamnati da kuma birane.
“A halin yanzu an amince da al’ummar kurame a matsayin daya daga cikin kananan kabilu a Afirka ta Kudu.
Wannan wani mataki ne wanda zai bude kofar abin da suka kwashe shekaru suna nema,” kamar yadda Claudine Störbeck, daraktan cibiyar nazari kan kurame a birnin Johannesburg, ya shaida wa TRT Afrika Hausa.
Idan Shugaba Cyril Ramaphosa ya rattaba hannu kan dokar, kamar yadda ake tsammani, zai kasance sakamakon kokarin shekaru na masu fafatuka da masana da masu bincike da kuma masu tsare-tsare.
Samun Karin karbuwa
Akalla ‘yan Afirka ta Kudu 400,000 suna amfani da yaren bebenci, amma adadin mutanen dake fama da matsalar ji a hukumance ka iya fin hakan don a da an saka masu larurar ji cikin masu nakasa ne.
Kundin tsarin mulkin Afirka ta Kudu ba ta tilasta wa gwamnati amfani da dukkan harsunan hukuma wajen gudanarwa ba. Ta takaita harsunan zuwa akalla uku.
Amma matsayi na harshen kasa a hukumance zai bai wa yaren bebaye damar sake neman samun karbuwar masu lalurar.
“A halin yanzu mutanen suna da wata madafa a hukumance ta cewa ba su gamsu da irin ayyukan gwamnati da ake musu ba su kuma kara buri kan abubuwa musamman wajen samar da ilimi ga kurame,” in ji Farfesa Störbeck.
Makarantun kurame 43 ne kawai ake da su a kasar.
‘Yan majalisar dokoki sun shaida hakan a lokacin da suke amincewa da gyran dokar, inda wata sanarwa daga majalisar ta ce gyaran zai “taimaka wa yaren bebaye samun karbuwa” kuma zai ba da kariyar bai daya ga mutanen da ke fama da larurar ji.
Matsayin da yaren bebayen ke da shi a hukumance zai “tabbatar da cewa ko wani dalibi yana da dama na daukar darasi tare da rubuta jarabawa ba tare da fuskantar bambanci ba”, in ji Umalusi, hukumar da ke kula da tabbatar da inganci a fannin ilimi.
“Wannan na nufin cewa a harkar koyarwa da daukar darasi, dole a bai wa harshen kayayyakin aiki yadda ya kamata,” in ji ta a sanarwa da ta fitar jim kadan bayan majalisar dokokin kasar ta amince da gyaran dokar.
Karya shingaye
Afirka ta Kudu, ana fassara labarai da sanarwar gwamnati a talabijin kai tsaye ne da yaren bebaye.
Amma babu masu tafinta na yaren bebaye a yawancin ofisoshin gwamnati. Alal misali a shekarar da ta gabata, hukumomi a lardin Western Cape Province sun tabbatar da cewa basu da tafinta ko daya dake aiki a matsayin cikakken ma’aikaci.
Bayan an kashe wani mataimakin shugaban makaranta a makarantar sakandaren kurame a shekarar 2015, an yi ta daga sharia’ar saboda rashin tafintan yaren bebaye.
An kwashe shekara shida kafin a yanke wa wadanda ake tuhumar, wadanda suka kasance kurame, hukunci.
“Ya kamata kurame su iya samun shari'a ta gaskiya kuma su iya shigar da kara kan cin zarafin saboda ana yawan cin zarafinsu.
“Ana yawan tsawaita shari’a a kotu saboda rashin tafinta,” in ji Farfesa Störbeck.
Ta kara da cewa: “Da wannan sanarwar a hukumance, ya zama wajibi ga gwamnati ta fara koyar wa wasu ma’aikatanta amfani da yaren bebaye.”
Duk da cewar masu fafatuka na yaba wa ci gaban da aka samu wajen samun daidaito wa mutane masu nakasa, sun ce ana bukatar a kara aiki wajen tabbatar da cewar masu larurar ji sun taka rawa wajen aikin gwamnati.
Wasu na cewa wurare kamar ofishin ‘yan sanda da cibiyoyin kiwon lafiya na iya samun karin iganci wajen tinkarar lamurar da suka shafi masu larurar ji domin hakan zai kawar da wasu shinge na sadarwa.
Suna kuma son kamfanoni masu zaman kansu su kara kasance masu karbar wadanda ke da larura ta hanyar saka yaren bebaye cikin yaren da za su yi aiki da su a lokacin daukar aiki da kuma gudanarwa ta yau da kullum.
“Yarda da yaren bebaye a hukumance ba shi ne karshen lamarin ba, akwai bukatar kara matsa kaimi wajen kaddamar da dokar,’’ a cewar Farfesa Störbeck.