Yawancin 'yan wasan kwallon kafa na Afirka suna kaura zuwa Turai don samun rayuwa mai kayu da kuma sana'a. Hoto: Wasu  

Daga Omar Abdel-Razek

Gasar kwallon kafa na Afirka AFCON a 2023 shi ne wasa mafi girma a duniyar kwallon kafa a nahiyar.

Ga miliyoyin magoya bayan kwallon kafa a fadin nahiyar, wannan lokacin ba wai na nuna goyon baya ga kungiyoyin kasashensu ba ne kawai, lokaci ne da za su kalli irin gudunmawar da fitattun ‘yan wasansu wadanda suka bar kungiyoyinsu na cikin gida don taka leda a kungiyoyin Turai suka bai wa kasashensu na asali.

’Yan wasa irinsu Sadio Mane na Senegal da Mohamed Salah na Masar sun zama misalai na nasarori da kuma akasin haka a duniyar kwallon kafa a Afirka.

Shin za a iya cewa suna wakiltar nasarorin da 'yan wasan kwallon kafar Afirka a duniya ke samu ne ko kuma tsamin jiki suke tarawa?

Yayin da kwallon kafa ya kasance wasa mafi shahara a Afirka, ci gabansa a shekarun baya-bayan nan ya yi kasa idan aka kwatanta da yadda ya shahara.

Rashin zuba jari da cin hanci da rashawa da kuma "tara tsamin jiki" wa fitattun 'yan wasa masu ƙwazo sun ba da gudunmawa ga halin da ake ciki.

Masu sharhi da dama ba za su iya daina kwatanta kwallon kafa na Afirka da na Turai: ko me yasa wasan ke ci gaba da raguwa a Afirka yayin da a bangare guda yake zama wani muhimmin tushen samun aikin yi da zuba jari tare da kari a ma'aunin tattalin arzikin Turai GDP?

Kungiyoyin kwallon kafa na Afirka da Turai duk suna da kusan shekaru iri daya da aka samar da su.

An kafa kungiyar kwallon kafa ta Turai (UEFA) a shekarar 1954 kuma tana da kungiyoyi 55 a karkashin inuwarta a halin yanzu.

An kafa Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) a shekara ta 1957, inda aka yi gasar farko a Khartoum tsakanin Sudan da Habasha da Masar bayan da Afirka ta kudu ta fice sakamakon kin amince wa ta shiga gasar da wata tawaga da ke da bambancin launi da al'adu.

Hukumar tana da kasashe 54 amatsayin membobinta, CAF ta sanar a shekarar 2023 cewa kudaden shigar ta ya kai dala miliyan 125.2.

A gefe guda kuma, rahoton Deloitte na shekara-shekara kan harkokin kudi na kwallon kafa ya nuna cewa darajar kasuwar kwallon kafa ta Turai ta kai Yuro biliyan 29.5 a shekarar 2022, inda manyan kungiyoyin kwallon kafa biyar na Turai ke samun kudin shiga da suka kai Euro biliyan 17.2.

Wannan bambancin da ke tsakanin kwallon kafa na Afirka da na Turai na zama dalilan da yawancin matasa 'yan wasan Afirka su ke daukar matakan guje wa rashin tabbas da suke tsintar kansu a kasashensu, ba tare da la'akari da samun nasara ko akasin haka ba.

A cewar rahotanni da dama, akwai 'yan wasan kwallon kafa na Afirka sama da 500 a kungiyoyin nahiyar Turai, adadin da ke wakiltar sama da kashi 35 cikin 100 na 'yan wasan kasashen waje a cikin manyan kungiyoyin.

Wasu na iya dagewa kan cewa wadannnan 'yan wasa sun kafa tarihi ga kasashensu kuma sun zama abin koyi da alfahari ga yara da matasa masu burin zama kamarsu, ta fuskar samun suna da kuma arziki.

Babu wanda zai musanta irin tasirin da Mo Salah ya samar, alal misali, wajen ciyar da martabar al'adu da addinai daban-daban a Biritaniya.

A lokacin da magoya bayan Liverpool ke rera wakar "Mohamed Salah, kyauta daga Allah" tare da watsa labarai da dama game da kyawawan dabi'un Musulmin Masar, lamarin ya kara karfafa zaton cewa fitattun 'yan wasan kwallon kafa irin su Salah na iya sauya duniyar da ke kewaye da su.

Wani bincike da Jami’ar Stanford ta gudanar a shekarar 2021 ya nuna yadda Salah ya taka rawar gani a Liverpool tare da addininsa na Musulunci ba tare da nuna wan bambanci ba, ya sauya tunanin da magoya bayan Liverpool ke yi wa Musulunci da Musulmai.

Irin wannan muhawarar da ke kare kwararar 'yan wasan kwallon ƙafa na Afirka zuwa Turai na zama matsayin wani bangare da ke habaka tsare-tsare hadin gwiwar duniya.

A tattalin arzikin duniya, ba a daukar kwallon ƙafa da 'yan wasa a matsayin wasa zalla, kasuwanci ne da a bi dokoki da ka'idojin kasuwa.

“Tsamin jiki”

La'akari da cewa hijirar neman aiki daga kasashen nahiyar (Afrika da Asiya, da Latin Amurka) zuwa tushen masana'antu na tsarin tattalin arzikin duniya ya kasance ba sabon abu ba ne (ya dada zama gama gari bayan yakin duniya na biyu daga wadanda suka yi mulkin mallaka zuwa cibiyoyin mulkin mallaka a Turai). Kwararar kwararrun 'yan wasan kwallon kafa sabon abu ne.

A farkon shekarun 1990, kungiyoyin Turai sun sassauta takunkumin hana yawan 'yan wasa daga kasashen waje a kungiyoyinsu bayan hukuncin kotun Turai a 1995 (Hukuncin Bosman) wanda ya sauya ka'idojin FIFA a hukumance game da musayar 'yan wasan kasashen waje da adadinsu a wasanni ko kuma biyan kudaden canja kungiya ga ’yan wasa ba tare da amfani da kwantiraginsu da kungiyoyinsu na asali ba.

Tun bayan hukuncin, "Kungiyoyin Afirka suka fada cikin wani yanayi mai matukar wahala wajen rike gwanayen 'yan wasansu ta fuskar gwaggwaɓan tayin da kungiyoyin Turai ke musu, wanda hakan ya rage yawansu zuwa matsayin kungiyoyin fitar da hazaƙa," a cewar wani bincike da Iwebunor Okwechime da Olumide A. Adetiloye suka fitar a shekarar 2019.

Wannan yanayin ya ba da hanya ga kungiyoyin Turai su kafa hanyoyin sadarwa don "bincike da janyo" masu ƙwazo da baiwar kwallon kafa daga Afirka don shiga kungiyoyinsu.

Wadannan cibiyoyin sadarwa sun hada da masu daukar 'yan wasa da wakilai da masu ba da shawara da makarantun kwallon kafa da wadanda yawancinsu ba sa bin ka'idoji da aka tsara a Afirka kuma suna cin gajiyar cin hanci da rashawa a bangaren wasanni.

Tabarbarewar tsare-tsare

Wani abin lura a nan shi ne yadda hijirar ‘yan wasan kwallon kafa zuwa Turai ya kai kololuwar wani yanayi na tashin hankali ga galibin kasashen Afirka.

A shekarun 1990 ne lokacin da aka tilastawa galibin kasashen Afirka aiwatar da sauye-sauyen tsarin tattalin arziki da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasashen duniya suka gindaya.

Hakan na nufin bangarori kamar na wasanni da al'adu sun zama wata hanyar samun kudi ga gwamnatocin Afirka, lamarin da ya sa ƙwararrun 'yan wasa da sauran su neman wuraren samun rayuwa mai kyau a Turai.

Wannan sakaci da ya hadu da cin hanci da rashawa da son kuma zuciya, ya taimaka matuka gaya ga halin da ake ciki a harkar kwallon kafar Afirka.

Yawancin kungiyoyin kwallon kafa a Afirka gwamnatoci ne suke tafiyar da harkokinsu da karancin kudade, ga rashin filayen wasanni da horo ko kuma takaitaccen makarantu da aka tsara don goge kwararrun 'yan wasa.

Kazalika wasu 'yan wasan suna karafin cewa ba a basu albashinsu akan kari.

Daukar 'yan wasa a kungiyoyin cikin gida baya bin ka'idojin da suka cancanta sai na shawarar da wakilan 'yan wasan suka yanke da kuma nawa suka biya jami'ai.

A cikin 'yan shekarun nan, wasannin gasar Turai sun sami yawan masu kallo daga nahiyar fiye da wadanda ake bugawa a cikin gida.

Yawan 'yan kallon gasar lig na Afirka na ci gaba da raguwa, abin da ke hana kungiyoyin cikin gida samun muhimmiyar hanyar samun kudin shiga idan aka kwatanta da takwarorinsu na Turai.

Duk da kasancewar 'yan wasan Afirka a duniya, wasan kwallon kafa na Afirka ya fuskantar koma baya wajen karawa da irin ka'idoji da kungiyoyin Turai ko na Latin Amurka suka gindaya.

Idan ban da 'yan kadan daga cikin su kamar Afirka ta Kudu da Masar, kwallon kafa a Afirka ba shi da wani tsari na kwararru, yanayin da ke kara haifar da "tsamin jiki" da ake fama da shi.

Magance wadannan koma baya da suka shafi tsarin ya zama wani abu muhimmi ga bunkasar wasan kwallon kafa na nahiyar a fagen kasashen duniya.

La'akari da cewa kwallon kafar Afirka ba shi da tsarin kwararru da zai iya daukaka shi zuwa matsayin na Turai ko Latin Amurka.

Idan har ba a warware wadannan kalubale ba, to Afirka ba za ta iya cika burinta na kara yawan wakilcinta na kungiyoyi 5 zuwa 9 a gasar cin kofin duniya mai zuwa na shekarar 2026 ba, kuma batun "tsamin jiki" zai ci gaba da gudana.

Marubucin,Omar Abdel-Razek, masanin ilimin zamantakewa ne kuma tsohon Edita a sashin Larabci na BBC. Yana zama da aiki a London.

Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko manufofin dab'i na TRT Afirka ba.

TRT Afrika