Shirin bayar da horon na kawo sauyi ga matan kudu maso-gabashin Senegal. / Photo: TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

Dindefelo, a yankin kedougou na kusu maso-gabashin Senegal, ta zama babbar inuwar inanta rayuwar mutane.

Dazukan da yankin ke da su, tare da tsaunuka, magangarar ruwa, da suka anyo wanzuwar namun daji da yawa, na daga abubuwan da ke kawata yankin.

Korran bishiyun yankin ne kashi 25 na dazukan Sanagal. Filin shakatawa na Nikolo-Koba, wanda ya samu damar shiga jerin Kyn Tarihi na Duniya na UNESCO da ke gabar tafkin Gambia, na karbar 'yan yawon bude ido, kuma hakan na daga abubuwan da ke habaka tattalin arzikin yankin.

To mene ne zai iya kasancewa ba daidai ba a wannan yanki mai ban mamaki?

Baya ga dadin kasnacewa a yankin, ana bayar da labaran gwagwarmayar mutane, musamman ma mata da ke ayyukansu a yankin kebantacce.

Yawon bude ido da ayyukan noma ne manyan masu habaka tattalin arzikin yankin, tare da zinare da ake haka, duk da dai jama'ar yankin ba su cika amfana da arzikin zinaren ba.

Rundunar matasa

A 2023, Kungiyar Matasa Mai Rajin Kawo Cigaba Mai Dorewa, ta fara aikin horas da mata 6,000 a kauyukan yankin da wani tsari na kudade, kula da kasuwancinsu da sarrafa kayan amfanin gona da abinci.

Shirin ya zama mai kawo sauyi ga matan yankin. Da yawan su na jin karfin gwiwa game da tallata wa da sayar da kayan nomansu da kula da kudadensu.

"Mun aiwatar da wannan a matsayin taimakon koyon sana'a tun bayan fara ayyukansu," in ji wanda ya samar da kungiyar, Hassan Sam, yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Wannan mai koyar da sana'o'i da sauran matasa daga Dindefelo, a koyaushe ya yi amman cewa al'ummarsu za su kawo cigaban tattalin arziki idan suka yi amfani da damarmaki sama da na yawon bude ido kawai.

A yanzu da ake iya ganin sauyin halayyar mutane, burin Hassan da 'yan tawagarsa a nan gaba shi ne cigaba mai dore wa.

A 2023, Kungiyar Matasa Mai Rajin Kawo Cigaba Mai Dorewa, ta fara aikin horas da mata 6,000 a kudu maso-gabashin Senegal. / Photo: TRT Afrika

Mayar da hankali kan mata

Duba ga alamomin farko, kwamitin gudanarwa na mutane biyar ya gamsu da cewa karfafa wa mata ne hanya mafi tasiri domin kawo sauyin tattalin arziki.

Mata ne kashi mafi yawa na wadanda suka fi amfanar da al'umma, inda mafi yawan su suke ayyukan noma da kananan kasuwanci.

"Da yawa daga ciki wadannan mata na yin noma, sarrafa wa da sayar da kayan noma da 'yan yawon bude ido ke bukata." in ji Hassan.

"Mun gano ta hanyar sanya idanu cewa akwai 'yar damuwa game da samarwa da kulle wadannan kayayyakin."

A yayin da mambobin kungiyar ke kara yawa, Hassan na isa ga daidaikun mutane da cibiyoyi na waje don neman gudunmowa da kwarewarsu. Tuni wata jami'ar Spaniya ta bayyana aniyar tallafawa wadannan mata karkashin kungiyar domin su habaka kasuwancinsu.

Hassan ya shaida wa TRT Afrika cewa "Horon da muke bayarwa na ga yawa sosai. Wadannan mata da mafi yawan su iyaye da 'yan uwanmu ne, suna koyon yadda za su sarrafa kudadensu. Suna koyon kasuwancin zamani da jan hankulan masu sayen kayayyaki. A yanzu suna da dabarun yadda za su kunshe kayayyaki tare da sayar da su bayan tallata su, kayan sun hada da gari, man kadanya da zuwa, da busasshen mangwaro da burodi."

Wasu kayayyakin irin su mangwaro, ana busar da su ko sarrafa su a lemuna don biyan bukatar abokan hulda.

Guguwar sauyi

Dioula Camara, da ke da shekaru arba'in da dan wani abu, na daya daga cikin wadanda suka amfana da wannan horo. Inganci da kyawun kayanta ya sauya, inda suke samar da riba mai yawa.

Camara ta fada wa TRT Afrika hausa cewa "Na fahimci cewa kwastomomi ba su damu da me aka rubuta kudin kaya ba. SUna son kaya na musamman da za su biya bukatunsu. Ina farin ciki suna sayen kayana sama da yadda suke yi a baya."

Alkaki, wanda a yaren yankin ake kira da "Bouye", ana sayar da shi a ledoji. Sannan yanayi da girman kwalbar da aka zuba su da irin zumar da aka barbada masa ne ke bayyana wanne iri ne.

"Tun da fari, 'yan yawon bude ido na tambayar abubuwa saboda kayan namu ba su da tambari. Muna sayar da zuma a kwalba mara rubutu. Da na duba, sai na ga me ya sa kwastomomi suke taraddadi," in ji Camara.

Wasu daga cikin jama'ar yankin da dama sun fahimci hakan su ma sun koma karbar horon.

"Mun samu horo kan yadda za a adana kayayyaki a hana su lalacewa, da yadda za a kare afkuwar gobarar daji. Koyon noman kifaye a kimiyyance da dogaro da kai wajen juya kudade na da alfanu sosai," in ji Amadou Sow, mazaunin daya daga cikin kauyukan yankin yayin da yake tattaunawa da TRT Afirka.

TRT Afrika