Daga Gaure Mdee
Duk da cewa Afirka na da mafi karancin adadin marasa aikin yi a duniya a rubuce a tsakanin matasa masu shekaru tsakanin 15 zuwa 24, wanda a 2021 yake kaso 10.6 cikin 100, kamar yadda alkaluman Hukumar Kwadago ta Duniya suka bayyana.
Akwai matasa da dama da ba su da aikin yi ko talauci ya yi musu katutu, saboda karancin albashi da rashin tsarin tallafawa jama'a.
Wannnan kalubale ya sanya kasashen Afirka gaza zama tsaran kasashen yamma game da alkaluman rashin aikin yi.
A 2024, ana hasashen kashi 11.2 na matasan Afirka da ke da shekara 15 zuwa 24 za su zama marasa aikin yi. A yayin hakan bai sauya ba a alkaluman ILO tun 2021, amma asalin adadin na iya fin haka.
Idan aka sake bude wannan batu, sama da mutum daya daga ciki kowanne mutum hudu a Afirka - kusan mutane miliyan 72 ba su da aikin yi. Biyu cikin uku na wannan adadi mata ne matasa.
An tsara Afirka ta zama nahiya mai habaka cikin sauri da mutane masu karancin shekaru.
Wannan na bayar da damarmaki da dama, amma kalubalen ayyukan yi na iya illata wannan dama ta yawan jama'a.
Dalilan janyo daduwar rashin aikin yi
Rashin aikin yi a Afirka a tsakanin matasa na tasirantuwa da matsalar da ta dade tana damun nahiyar, da kuma rashin ayyuka masu kyau.
Yawaitar jama'a cikin sauri ne ke kara munana halin rashin ayyukan yi din.
Bambancin da ake nunawa wajen daukar matasa ayyuka duba da iliminsu na daga cikin matsalolin da ake fuskanta.
A wasu lokutan, matasa masu ilimi na iya fuskantar kalubalen samun ayyuka da suka dace da fannin da suka karanta, ko kuma yadda suka mayar da hankali kan sai sun samu ayyukan yi a birane.
"Ba a samar da tsare-tsaren da z asu taimakawa mutane su dinga samun hanyoyin cin abinci ba. Yanayin tattalin arzikin da ake ciki ba shi da kyau ga fara kasuwanci," in ji Fidelis Yunde, wanda ke da wata kungiyar Gwagwarmayar Matasa Don Sauyi yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Wani abun mamaki shi ne a Afirka matasa na fara fuskantar kalubale da zarar sun kammala jami'a ko babbar makarantar gaba da sakandire. Wasu na yin dabarar fara kasuwanci a lokacin da suke makaranta.
Esther Pallangyo, wadda ta karanta cigaban karkakara a jami'ar Aikin Noma ta Sokoine, na da ra'ayin cewa ya kamata a dinga bayar da ayyuka duba da karatun da matasa suka yi.
"Akwai matasa da suka gama jami'a da dama amma ba su da ayyukan yi," ta shaida wa TRT Afirka.
'Yar asalin yankin Mwanza ta dawo gida inda ta fara neman aikin yi tun a kan hanya.
Kwararru sun yi amanna da cewa rashin aikin yi na janyo aikata muggan laifuka a tsakanin jama'a a yayin da mutane suke gwagwarmayar rayuwa.
Daukar matakan gyara
Gwamnatocin Afirka da kungiyoyin cigaba da suke aiki da su na ta kokarin magance wannan matsala ta rashin ayyukan yi ta hanyar kawo shirye-shiryen koyar da sana'o'i a bangarorin da suke da muhimmanci kamar ayyukan noma, kera kayayyaki da sana'o'in hannu.
Fidelis ya bayar da shawarar a dinga koyawa daliban jami'a sana'o'i. Wani batu da ya kawo kuma shi ne na cewar a mafi yawancin lokuta matasan ba sa shirya kawunansu don ba su ayyukan yi.
Matasan da suka shiga ayyuka na musamman na koyon sana'o'i da sauran dabarun gudanar da rayuwa don taimakawa kawunansu samun ayyukan yi da gudanar da kasuwancinsu.
"Mutane na yawan jin tsoron fara kasuwanci. Yi tunani a ce in saka 'yan kudadena gaba daya a wani kasuwanci, sannan su lalace. Wannan ne abun tsoron," in ji Fidelis.
Esther na duba yiwuwar fara wani kasuwanci amma na bukatar samun tabbacin cewa zai dore.
Tunani ma wata babbar matsala ce. Iyaye da dama a Afirka na karya gwiwar 'ya'yansu daga yin ayyukan da suke sha'awa kar su zane, sana'o'in hannu, wakoki da kade-kade, da suke wa kallon ayyukan jin dadi.
Har manyan marubuta a Afirka irin su Chinua Achebe na Nigeria si da ya karanta likitanci sannan ya koma rubuce-rubuce.
Kwararru na cewa, ya kamata magance matsalolin zamantakewa da akidu na gargajiya da suka hana mutane samun damarmaki ya zama abu da za a sanya a gaba.
Ana tsammanin makarantu za su samar da horo da dabarun zamani don karasa wannan aiki.
Ya kamata a fahimci karfafawa matasa d ake da ilimi da kaifin basira na da amfani sosai wajen samun cigaban zamantakewa da tattalin arziki mai dorewa, da kuma rage hatsarin shiga aikata muggan laifuka.