Daga Abdulwasiu Hassan
A ranar 27 ga Yuli, majalisar zartarwa ta Ghana ta yanke hukuncin hana fitar da danyen sinadarin lithium da ba a sarrafa, bayan da wasu kasasen Afirka da dama suka dauki irin wannan mataki da manufar kara yawan ribatar albarkatun kasar da suke da su.
Wannan sabuwar manufa ta Ghana, wadda ake sa ran za ta zama doka bayan amincewar majalisa a karshen 2023, na da manufar ‘sai an sarrafa kayayyaki’ kafin a fitar da su zuwa kasashen waje, in ji ministan kasa da albarkatun kasa na Ghana, Samuel A. Jinapor.
Majalisar ministocin Namibia ta dauki irin wannan mataki wata guda kafin Ghana ta dauka. “Za a iya barin fitar da irin wadannan albarkatun kasa da ba su da yawa zuwa kasashen waje idan ministan albarkatun kasa da makamashi, da kuma amincewar majalisar ministoci,” in ji Emmerson Theofelus, mataimakin ministan yada labarai da fasahar sadarwa na Namibia.
A watan Disamban 2022, Zimbabwe ta dauki irin wannan mataki game lithium din da ba a sarrafa ba.
Wata sanarwar da ma’aikatar albarkatun kasa da makamashi ta kasar da ke kudancin Afirka ta bayyana cewa wannan mataki na da manufar dabbaka shirin shugaba Emmerson Mnangagwa na ganin kasar ta zama mai kudaden kashewa da dama.
Karkata ga makamashin mai sabuntuwa
Ba arashi ba ne samun kasashen Afirka da albarkatun kasa irin su lithium, babban sinadarin hada batira, suna sake nazarin dabarun fitar da albarkatun kasa da suke da su zuwa kasashen waje, a lokacin da su kuma kasashen da suka ci gaba suke sauya wa zuwa amfani da makamashi mai sabuntuwa.
Hakan yana sa manyan kamfanunnukan samar da ababan hawa ke mayar da hankali kan kera masu aiki da lantarki.
Misali Ingila, ta yanke hukuncin daina sayar da motoci masu aiki da lantarki ko man diesel nan da shekarar 2030. A shekarar 2035 kuma kasashen tarayyar Turai ma za su hana sayar da motoci masu fitar da hayaki.
Tuni wasu kamfanunnuka suka fara sanar da lokacin da za su daina samar da injina masu aiki da mai, inda za su mayar da hankali gaba daya ga samar da motoci masu aiki da lantarki.
Baya ga lithium, wadannan batira na bukatar cobalt wand shi ma ake da arzikinsa sosai a Afirka.
Gogayya da China
China ce babbar mai taka rawa a duniya wajen sarrafa lithium, kuma sauran kasashe masu taso wa na ganin yadda za su yi gogayya da ita.
Zimbabwe na da kaso 1.2 na adadin lithium din da ake da shi a duniya, kamar yadda almakuman BP suka fitar, inda amurka da China kuma suke da kaso 4.0 da kaso 7.9.
Ana ci gaba da gano ma’adanin lithium a kasashen Afirka. A 2022, Nigeria ta sanar da gano lithium mai inganci sosai a jihohin kasar da dama.
“lithium din da ke Nigeria abu ne da ake bukata sosai a yau. An gano wannan abu mai daraja a jihohi da daman a kasar, a yayin wani shiri na nemowa da binciko albarkatun kasa da aka gudanar,” in ji Abdulrazak Garba, Darakta janar na Hukumar Binciken Yanayi da Albarkatun Kasa ta Nijeriya.
Ya ce “Ingancin lithium da ake so a duniya yana fara wa ne daga 0.4 daga cikin dunkulensa. A lokacin da muka fara aikin bincike da hako shi, mung a har zuwa kaso 13 na lithium a cikin dutsen da ake ciro wa.”
Dabbaka manufofi
A lokacin da kasashen Afirka da ke da arzikin lithium da yawa suke zama wajen da kasashen yamma suke amfani da su wajen cimma Rasha kan sarrafa lithium da fitar da shi, shin hana fitar da danyen lithium zai taimaka?
Nazari da binciken da aka yi na da ra’ayoyi daban-daban. A yayin da wasu ke ganin hakan zai taimaka wajen habakar kamfanunnuka a cikin Afirka, wasu na ganin wannan mataki zai rage yawan kasuwancin lithium da ake yi.
“Masu zuba jari na kasashen waje za su zama dole su kafa masana’antun sarrafa lithium a Afirka. Wannan zai samar da ayyukan yi ga ‘yan Afirka.” In ji Abdullahi Lawal, wani babban jami’in binciken yanayin kasa da ke Nijeriya.
Amma abun lura kuma shi ne yadda kasashen Afirka da ke fama da matsalolin tsaro za su gaza amfana da wannan dama.
Abdullahi ya yi tsokaci da cewa “Masu zuba jari na kasashen waje ba za su so su zuba kudadensu a kasashen Afirka da ke fama da matsalolin tsaro ba.”
Wasu masana tattalin arziki na cewa wannan abu zai nakasta kasuwanci da sauran kasashen Afirka, saboda za a daina kai lithium kasashen Afirka da suke da masana’antun sarrafa sinadarin.
“Kasashen Afirka da za su hana fitar da sinadaran samar da makamashi mai sabuntuwa, za su gaza kai kayayyakin nasu zuwa sauran kasashen Afirka,” in ji idakolo Gabriel Gbolade na kamfanin SD & D capital yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Wasu kwararru kuma na da fata nagari kan wannan tsari da ka’ida za su samu nasara a nan gaa, matukar dai masu kula da su ba su nuna son zuciya ba.
Abdullahi ya ce “zai dauki dan lokaci, amma tattalin arziki zai habaka matukar shugabanni suna yin abun da ya dace.”
Yana da ra’ayin cewa saka dokoki game da ama’adanan samar da makamashi mai sabuntuwa za su habaka matsayin Afirka game da bukatar da yammacin duniya take da ita na makamashi.
“Mafi yawan ma’adanan da ake amfani da su don habaka fasahar samar da makamashi mai sabuntuwa na nan a Afirka. Nahiyar da ke kokarin saka dokoki kan fitar da ma’adananta, za karfafi kanta.”
Duba ga kai
Maimakon kawai a dinga duba ga masu samar da ababan hawa a kasashen waje, wasu kwararru na a ra’ayin cewa ya kamata kasashen Afirka su yi duba ga kawunansu don samar da hanyoyin ci gaban makamashi ma sabuntuwa a nahiyar.
“Na yi amanna cewa kasashen Afirka za su iya habaka kawunansu da albarkatun da suke da su.” In ji Idakolo.
Ya bayar da shawara ga gwamnatocin Afirka kan su yi amfani da bukatar Yammacin duniya ta makamashi mai sabuntuwa wajen habaka masana’antunsu.
Matsalolin zartarwa Kasashen Afirka ba wai manufofi ne ba su da su ba, babbar matsalar ita ce aiwatar da manufofin.
Ga dukkan wani tsari na habaka fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, masana na ganin wasu matakai da za a dauka na yadda ‘yan Afirka za su amfana da arzikinsu.
Za su iya fara wa da tirsasa masu zuba jari na kasashen waje su samar da masana’antunsu a kasashen Afirka.
Za su kuma iya sanya hannu kan yarjeniyoyi na fitar da kayayyakin ya zama biyan basussukan da kasashen ke bukatar kayan ke bin su.
“Misali, China na bin Nijeriya bashin kudade da yawa, kuma China na bukatar lithium. Nijeriya za ta iya sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da China da za ta zayyana yadda za a biya bashin da lithium da ake fitarwa,” in ji Abdullahi.