Ana wakiltar mutanen da makamashi mai gurbata muhalli ya illata daga sassan nahiyar a taron. Hoto: AP

Ana kallon taron sauyin yanayi na farko a Afirka wanda aka soma a Kenya babban birnin Nairobi a ranar 4 ga watan Satumba a matsayin wata nasara, ba wai don shi ne na farko a nahiyar ba, amma kan abubuwan da ke faruwa a wurin taron.

Kusan kungiyoyi masu zaman kansu 500 ne daga Afirka kan sauyin yanayi suka saka hannu kan abin da suka kira “The African People's Declaration 2023”, inda suke taruka daban-daban.

Ana wakiltar mutanen da makamashi mai gurbata muhalli ya illata daga sassan nahiyar a taron.

Daina amfani da makamashi mai gurbata muhalli na daga cikin ginshikin taron wanda hakan ya sa ya bambanta da wasu tsare-tsare na baya.

“Dole makamashi mai gurbata muhalli ya ci gaba da zama a cikin kasa. Muna bukatar cikin gaggawa a daina tono shi, da kuma kawar da samar da fetur da gas da gawayi a ko ina,” kamar yadda aka bayyana.

Wasu wakilai sun ce shugabannin sun san abin da ya kamata a yi, amma ba sa yi a kan lokaci kan batun iska mai gurbata muhalli. Hoto: Others

Makamashi mai gurbata muhalli makamashi ne wanda ba a sabuntawa kamar danyen man fetur da gawayi da sauransu.

Jagorantar kawo sauyi

“Muna sa ran shugabannin kasashe za su saurari muryoyinmu. Ba wai su ne kadai ba – muna son jama’ar Afirka su ji muryoyinmu,” kamar yadda Tasneem Essop wanda shi ne daraktan kungiyar Climate Action Network CAN, ya bayyana.

Muhammed Lamin Saidykhan, wanda jagora ne a CAN, na ganin lokaci ya yi da za a jagoranci sauyi maimakon a jira shi.

“Kimiyya a bayyane take. Ta bayyana cewa babban abin da ke jawo sauyin yanayi shi ne dakatar da zuba jari a bangaren makamashi mai gurbata muhalli; idan ba mu dakatar da hakan ba, wanda hakan ke nufin muna saka rayuwarmu a cikin hatsari, muna saka damarmu ta rayuwa a cikin hatsari,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Gidauniyar Green strategy Greenpeace wadda ita ce ke jagorantar tsarin amfani da makamashi mara gurbata muhalli, na gudanar da wani kamfe domin neman taron sauyin yanayin na Afirka ya tabbatar da cewa ba za a ci gaba da zuba jari kan makamashi mai gurbata muhalli a nahiyar ba.

Dama ga Afirka

Kalubalen na Kungiyar Tarayyar Afirka ce, wacce tana daya daga cikin wadanda suka shirya taron domin su dauki mataki mai tsauri kan daina amfani da makamashi mai gurbata muhalli.

Fari na daga cikin abin da sauyin yanayi ke jawowa Afirka. Hoto: OTERS

“Ko dai AU ta bayar da karfin gwiwa domin tabbatar da Afirka ta koma kashi 100 bisa 100 kan makamashi wanda ba ya gurbata muhalli, da samar da makamashi mai sauki ko kuma ta bar manyan kamfanonin mai da kuma masu hakar ma’aidinai ci gaba da jefa duniya cikin bala’i bayan bala’i,” in ji Moses Wemanya, mai bayar da shawara ne kan makamashi mara gurbata muhalli wanda shi ma yana cikin kamfe din.

"Fetur da isakar gas sun ta'azzara matsalar sauyin yanayi. Muna bukatar mafita kan akan, kuma ba za mu iya samo mafitar ta hanyar fadada masana'antar fetur da gas a Afirka ba. Muna bukatar gano hanyar zuba jari a sabon tsarin makamashi wanda zai samar da bukatun al'ummar Afirka."

Lamin na kungiyar CAN International ya yi bayani kan fuska biyun nahiyar da kuma yadda abin zai shafi jama'arta.

"Afirka ce take kaso 40 cikin 100 na albarkatun kasar da duniya take bukata wajen daina fitar da iska mai gurbata muhalli. Duk da haka fiye da 'yan Afirka miliyan 600 ne ba sa samun makamashi," in ji shi.

Gwamnatin Zimbabwe tana da burin samar da megawatt 1,100 da makamashi mara gurbata muhalli nan da shekarar 2050. Hoto: AP 

Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo tana da shirin samar da tsarin noman rani a fili hekta miliyan daya nan da shekarar 2030.

Da wannan kasar tana fatan rage sare itatuwa da bunkasa aikin gona da kuma rage adadin iska mai gurbata muhalli.

Kongo tana aiki a halin yanzu don bunkasa amfani da makamashi daga hasken rana da iska da kuma ruwa.

A Tunusiya, Hukumar da ke Kula da Sauyin Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya (UNCC) ta ce ana samun karuwar bukatar makamashi.

Kalubale

Mozambique tana aiki wajen samar da lantarki daga makamashin hasken rana da iska ga gidaje 5,000 a wurare masu nisa daga gari.

A Habasha, gwamnati tana da shirin amfani da dam don samar da megawatt 600, wanda zai samar da isashshiyar lantarki daga ruwa wadda za ta biya mutanen kasar fiye da kaso 65 cikin 100.

Wannan ne Babban Taron Afirka ka Sauyin Yanayi na farko na Afirka. Hoto: Reuters

Yayin Babban Taron Afirka kan Sauyin Yanayi, wasu sun nuna shakku kan daina amfani da makamashi mai gurbata muhalli saboda yadda kamfanoni masu fitar da iskar da ke gurbata muhalli za su yi tasiri kan hakan yiwuwar hakan.

"Mun hadu a nan Nairobi, mun yi amannar cewa kamfanonin da ke fitar da iska mai gurbata muhalli suna tasiri sosai kan batun da ake tattaunawa da matakan da za a dauka yayin taron," in ji Stephen Kariuki, babban darakta a Kenya Network Forum, wato hukumar da ke sanya ido kan muhalli a kasar.

A dauki mataki cikin hanzari

“'Yan Afirka ba sa magana kan yadda za a shawo kan matsalar da ke shafarsu. Muna samun masu yi mana kutse kan iska mai gurbata muhalli wato masu zuba jari da ke daukar nauyi ko goyon bayan irin wadannan tarukan.

Wannan abin damuwa ne saboda wasu daga cikin shugabanninmu ba sa daukar nauyin da ya rataya a wuyansu kan abin da suke magana a kai," in ji Kariuki.

Wasu wakilai sun ce shugabannin sun san abin da ya kamata a yi, amma ba sa yi a kan lokaci kan batun iska mai gurbata muhalli.

Masu fafutikar kare muhalli suna ci gaba da wayar da kan jama'a kan sauyin yanayi yayin Babban Taron Afirka kan Sauyin Yanayi. Hoto: AFP

"Babu niyyar daukar matakai da gaske. Kasashen Yamma ba sa bayar da goyon baya, kuma kasashen da ke arewacin duniya ba sa taimakon Afirka wajen samar da makamashi mai tsafta ga mutanenta.

"Abin da ke faruwa shi ne suna kara taimaka wa wajen amfani da makamashi mai gurbata muhalli a wasu wurare," in ji Lamin.

Kamfanoni za su yaki abin

Kungiyar CAN, wadda ta kunshi kungiyoyin fararen hula tana shirin wani shirin yaki kan amfani da makamashi mai gurbata muhalli daga ranar 15 zuwa 17 ga Satumba.

"Kamfanonin da ke fitar da iska mai gurbata muhalli sun kaddamar da yaki kan dan Adam kuma idan muna so mu yake su, to ya kamata mu ci gaba da wannan taron na duniya har zuwa karshen shekara. Wannan zai karfafa bukatun mutanen Afirka," in ji Lamin.

Kamar yadda Tasneem ya bayyana "babban sakon" da ya kamata mutane su rike shi ne "galibin matsalar da za a fuskanta sanadin sauyin yanayi za ta faru ne a Afirka."

Wannan sako ne da zai karade ko ina kuma zai dauki tsawon lokaci bai bace ba, ko bayan an kammala Babban Taron Afirka kan Sauyin Yanayi, kuma bayan an manta da alkawuran da shugabanni suka dauka.

TRT Afrika