Damuwa da ke ta daɗuwa game da walwalar yara a Turai ta bayyana Birtaniya a can baya a matakin walwalar yara, a lokacin da ake fama da abin da ƙwararru ke kira "durkushewar farin ciki" a tsakanin matasa 'yan kasa da shekaru 20 a Birtaniya.
Rahoton baya-bayan na Yarinta Mai Inganci na 2024, wanda kungiyar 'The Children Society" ta fitar, ya bayyana cewa kashi 25.2 na yara 'yan shekaru 15 sun bayyana rashin gamsuwarsu, inda a Turai gaba daya ake da matsakaicin kashi 16.6.
Matasa a Holland ne suka fi kowadanne farin ciki a duniya inda kashi 6.7 ne kawai suka nuna rashin jin dadin rayuwar yau.
"Kararrawa na kadawa," in ji Mark Russell, shugaban zartarwa na kungiyar 'Children Society'.
Matsalolin kudi, talaucin yara da rasa abinci
Daya daga cikin manyan dalilan da suka janyo rashin farin ciki a tsakanin yaran Birtaniya shi ne talauci. Rahoton ya yi tsokaci cewa Birtaniya ce ta hudu a duniya a tsakanin kasashen da yara ba sa samun abinci sosai, inda kashi 11 na yara 'yan shekaru 15 ba sa cin abinci sau uku saboda rashin kudi.
Kungiyar ta gano iyaye da dama na gwagwarmayar samar da muhimman bukatun yaransu, inda daya cikin biyar na iyaye ne kadai ke iya samun damar bai wa yaransu abinci mai zafi a kowacce rana, kusan kashi daya cikin hudu ba sa iya sayen rigar sanyi, kumsa sama da kashi daya cikin hudu ne ke iya bai wa yaransu kayan marmari kullum.
Yara mata a Birtaniya ne matsalolin suka fi shafa, inda wadanda suka fito daga gidajen talakawa, da suke talaucin abinci suka kasance mafi yawa a tsakanin wadanda ba sa farin ciki da rayuwarsu.
Talaucin yara, da aka bai wa ma'anar yaran da ke rayuwa a gidajen da suke rayuwa da kudaden da suke kasa da kashi 60 na matsakaicin kudaden da 'yan kasa ke samu, ya zama batu mai girma a Ingila.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa daduwar talaucin yara na Ingila ne a kan gaba a tsakanin kasashe 43 na OECD.
Daga 2012 zuwa 2014, da kuma daga 2019 zuwa 2021, talaucin yara ya karu da kashi 20, a gidajen da ake da yara matalauta a farkon wadannan shekaru.
Yau, rabin dukkn yaran Ingila ba sa iya zuwa tafiye-tafiyen makarantu ko irin wadannan abubuwa saboda matsalolin kudi.
Wannan yanayi na ta ƙara yin muni a cikin shekaru da ake daukar matakan kashe kudade da gwamnatocin 'yan ra'ayin riƙau suka dinga aiwatarwa.
A 2013, wani nazari na Oxfam ya gano cewa yanke kasafin kudi ya sanya an dakatar da ayyukan walwalar jama'a da dama kamar su cibiyoyin matasa, wanda ya dinga kebantar da matasa da hana su samun wajen zama su shakata su huta da abokansu.
Tsohon wakilin MDD kan yaki da talauci, Philip Aiston, ya sha bayyana irin illar da yanke wadannan kudade ke janyo wa, wana ya kawar da ayyukan muhalli a ke zaunar da jama'a lafiya, aka bar yara da yawa cikin halin rauni.
Tabarbarewar tattalin arzikin ta kara munana saboda tsadar rayuwa, wanda suka sanya iyalai da dama gaza samun muhimman kayan bukatun yau da kullum.
Kashi 20 na gidaje mafiya talauci a Turai a yau suna cikin yanayi mafi muni sama da na Gabashin Turai. Biyu cikin biyar na yara na bayyana damuwa kan tashin farashin kayayyaki da yadda tattalin arziki ke tabarbarewa a kasar.
Kwararru na bayyana cewa domin kamo sauran kasashen da suka ci gaba, dole ne Ingila ta kara yawan kudaden da take kashe wa yara kanana da iyalai.
Rikicin rashin lafiyar kwakwalwa
Baya ga gwagwarmayar tattalin arziki, lafiyar kwakwalwar matasa a Ingila na lalacewa cikin sauri. A kowacce rana a Ingila ana aika yara sama da 500 zuwa asibitin kwakwalwa saboda damuwa, adadin da ya ninka sama da wanda aka gani a kafin annoba ta bulla.
Rahoton ya bayyana tsawon lokacin jira na neman a duba kwakwalwar yara, inda yara sama da 270,000 ke jiran a duba su bayan sun je asibitin farko.
Makarantu da ya kamata su zama wuraren girmama da neman mafaka, na kara ta'azzara lamarin. Kusan kashi 15 na dalibai ba sa jin dadin kasancewa a makarantu, inda suke bayyana yawan karatu da matsalolin zamantakewa kamar su cin zali.
Yadda abin yake karara
A yayin da a Ingila ake ta samun kara durkushewa, walwalar yara a dukkan Turai na munana sosai a 'yan shekarun nan.
UNICEF ta bayyana cewa, adadin yara kanana da ba sa jin dadin rayuwa a Turai ya ragu daga kashi 74 a 2018 zuwa kashi 69 a 2022.
Girmamar tazarar da ke tsakanin 'ya'yan talakawa da na masu kudi na nuni da tasirin talauci d arashin adalci d akuma rashin daidaito wajen lafiyar kwakwalwa.
Duk da haka, kasashe irin su Netherlands da Finland na ci gaba da zama a kan gaba da tsare-tsaren da ke kyautata rayuwar yara tare da bayar da tsari mai karfi.
Idan ba a samu sauyin manufofi masu muhimmanci a Ingila ba don amfanar matasanta, kwararru sun yi gargadin cewa jin dadinsu zai ci gaba da raguwa.