Wata kotun Birtaniya ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Ike Ikweremadu daurin kusan shekara goma a kurkuku.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan samun Ekweremadu da mai dakinsa da likitansu da laifin yunkurin cire kodar wani matashi domin sanya wa 'yarsa da ke fama da ciwon koda.
Kotun ta Old Bailey da ke Landan ta yanke wa mai dakinsa Beatrice hukuncin zaman gidan yari na shekara hudu da wata shida.
Haka kuma ta yanke wa likitansu Dr Obinna Obeta hukuncin daurin shekara goma a gidan yari bisa laifin hada baki da zummar cire kodar matashin.
A watan Maris ne kotun ta samu Mista Ekweremadu, da matarsa Beatrice, da kuma Dr Obinna da laifin hada baki wajen safarar matashin, mai shekara 21, da ke sana’ar tufafi a Jihar Legas zuwa Birtaniya don a cire kodarsa a sanya wa 'yarsu Sonia.
Ike Ekweremadu, wanda alkalin ya bayyana "a matsayin musabbabin faruwar komai," an yanke masa hukuncin daurin shekara tara da wata takwas.
Wannan shi ne karon farko da aka taba gabatar da tuhume-tuhume kan hada baki don a cire wani sashe na jikin dan adam a karkashin dokar bautar zamani ta 2015 a Birtaniya.
Dokar ta yi hani kan fataucin dan adam da cire duk wani sashe na jikin mutum inda ta tanadi hukuncin daurin rai-da-rai kan mutumin da aka kama da wannan laifin.