'Yan jaridar BBC sun soki kafar watsa labaran da ke Birtaniya da "nuna goyon baya ga Isra'ila da kuma rashin bayar da isassun rahotanni kan fararen-hula Falasdinawa idan aka kwatanta da Isra'ilawa a shirye-shiryenta game da rikicin Isra'ila da Falasdinawa," kamar yadda Al Jazeera ta rawaito.
"BBC ta gaza yin binciken kwakwaf game da ikirarin da Isra'ila ke yi, ba ta bayar da sahihin labari, don haka ba ta taimaka wa masu bibiyarta fahimtar keta haddin da ake yi a Gaza," a cewar wata wasika da ma'aikatan BBC takwas suka aika wa Al Jazeera ranar Alhamis.
A wasikar, 'yan jaridar na BBC sun zargi kafar watsa labaran da suke yi wa aiki da goyon bayan Isra'ila.
Sun yi zargin cewa a yayin da BBC ta nuna "babu sani babu sabo" a bayar da rahotanni kan zargin da ake yi wa Rasha na aikata laifukan yaki a Ukraine, a game da yakin Isra'ila da Falasdinawa tana "baki-biyu" musamman kan yadda take rawaito ukubar da fararen-hula a Gaza suke ciki.
Kazalika tana tantama kan yawan Falasdinawa da aka kashe tun da Isra'ila ta kaddamar da yaki a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba.
Wasikar ta ambato 'yan jaridar BBC suna cewa kafar watsa labaran tana amfani da kalmomi irin su "kisan kare-dangi" da "cin zarafi" ne kawai idan suka shafi Hamas, inda take bayyana kungiyar ta Falasdinawa a matsayin daya tilo da ta haifar da rikici a yankin.