Wani bincike ya gano cewa kashi biyu cikin uku na mata matasa na fuskantar cin zarafi da ya hada da neman yin lalata da su da hantara da kuma zagi a wuraren aiki a Birtaniya.
Sai dai galibinsu ba sa kai rahoton lamarin saboda fargabar cewa ba za a yarda da kalamansu ba ko kuma hakan yana iya shafar dangantakarsu da wurin aiki da kuma shi kansa aikinsu, a cewar gamayyar kungiyoyin kwadago ta Birtaniya a wani rahoto da ta fitar ranar Juma'a.
Ta fitar da rahoton ne a wani mataki na neman goyon bayan gwamnatin Birtaniya game da sabbin dokokin da ke son kare ma'aikata daga fuskantar cin zarafi da gallazawa.
A binciken da ta yi kan mata 1,000, kungiyar kwadagon ta ce ta samu uku cikin biyar na dukkan rahoto kan lamarin a wurin aiki -- inda ta kara da cewa kashi biyu cikin uku ya shafi mata da ke tsakanin shekara 25 zuwa 34.
Binciken ya nuna cewa mata matasa sun fi fuskantar barazanar musgunawa, inda fiye da rabin mata da ke da shekara 18 zuwa 34 suka ce sun sha fama da cin zarafi a wuraren aiki.
Ya kara da cewa kasa da kashi daya cikin uku na matan da suka fuskanci musgunawa ne suka kai korafi ga wuraren ayyukansu.