Wani faifan bidiyo da yadu a shafukan internet ya nuna yadda wasu 'yan daba suka yi wa wasu mata tsirara, tare da cin mutuncinsu a yankin arewa maso gabashin jihar Manipur ta kasar Indiya lamarin da ya harzuka alummar kasar.
Indiyawa dai sun bukaci a gaggauta daukar mataki a kan wadanda suka aikata wannan mummunan laifi.
Matan biyu ‘yan kimanin shekara 20 da kuma 40 da haihuwa, 'yan kabilar Kuki ne mabiya addinin Kirista, wadanda ke zaune a kan tsaunuka.
Lamarin ya faru da su ne a ranar 4 ga watan Mayu a gundumar Thoubal na jihar mai fama da rikice-rikice, kamar yadda kafafen yada labarai na Indiya suka bayyana ranar Laraba.
A bidiyon mai ban tsoro, an ga yadda gungun mazan ke jan matan biyu a kasa zuwa wani fili suna lallasa su da iya karfinsu.
Shafin yada labarai na intanet na Scroll, ya bayyana korafin da aka kai wa 'yan sanda kan cewa ‘yan daban sun hadu ne suka yi wa matar ‘yar shekara 21 fyade.
“Da muka ki ba su hadin kai, sai suka ce min: ‘Idan ba ki cire tufafinki ba, za mu kashe ki’,” matar ‘yar shekara 40 ta shaida wa Scroll.
Kamfanin yada labaran ya ambato wani jami'in 'yan sanda yana cewa, an tuhumi "'yan ta’addan" kusan 800 zuwa 1,000 da ba a tantance su ba da laifukan fyade da kisan kai, da dai sauransu.
Wadanda mummunan lamarin ya shafa sun shaida wa kafar yada labarai ta intanet ‘The Wire news’ cewa ‘yan sanda a Manipur sun kasance a wurin da aka aikata laifin amma ba su kawo musu dauki ba.
'Yan sandan Manipur sun ce a ranar Laraba "sun yi iyakacin kokarinsu wajen ganin sun kama wadanda suka aikata laifin da wurin."
Kira a dauki mataki
"Mummunan al'amarin da ya faru a cikin faifan bidiyon na cin zarafin mata biyu da suka fito daga Manipur rashin imani ne da kuma abin Allah-wadai," a cewar Ministar Gwamnatin Indiya Smriti Z Irani.
Ta ce jami'an jihar sun ba ta tabbacin cewa "ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta wadanda suka aikata laifin."
Jam’iyyar adawa a Indiya ta kai wa jam'iyyar hannun dama ta Firayim Minista Narendra Modi na BJP hari bayan faifan bidiyon ya yadu a intanet.
"Gwamnatin Modi da Jam‘iyyar BJP sun canza tsarin dimokuradiyya da bin doka zuwa tsarin zamantakewar jama'a wanda ya lalata al’amura a jihar," a cewar Mallikarjun Kharge, shugaban majalisar, yana mai kari da cewa "Indiya ba za ta taba yafe wa shirun" da Firaiminista Modi ya yi ba.
Rikice-rikice a Manipur
An samu karuwar tashe-tashen hankula a yankin Manipur.
A watan Fabrairu wata kotu ta ce gata na musamman da aka bai wa mutanen Kuki Kiristoci - da ke rayuwa a tsaunuka, suke amfana da romon tattalin arzikin gwamnati da kwatankwacin kashi 16 cikin 100 na al'ummar jihar, a mai da shi kan Hindu Meiteis, wadanda ke da rinjaye a jihar, a kuma damka kula da mafi yawan wurare masu wadata da ke yankin jihar.
Kusan mutum 120 ne aka kashe a rikicin da ya barke tsakanin kabilun biyu, yayin da wasu mutum 50,000 suka rasa muhallansu cikin watanni biyun da suka gabata.
A cewar Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta EU, sama da gidaje 1,700 da majami'u 250 ne aka lalata.
Tattaunawar zaman lafiya da dama da aka yi ta yi tsakanin kungiyoyin ta ci tura, sannan yawaitar tashe-tashen hankula da rikike-rikice da aka yi ta samu sun kara dagula lamura a jihar da ke karkashin jagorancin mulkin Firaiminista Modi na Jam’iyyar BJP.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun ce gwamnatin Modi da jam'iyyarsa sun gaza daukar matakin kawo karshen rikicin na kabilanci.
A yayin zawarcin hadin kai na diflomasiyya da Modi ya kai Amurka da Faransa a 'yan kwanakin nan, wani kudurin EU na makon jiya ya yi tuni kan yadda manufofin Modi na kishin Hindu suka jawo wa kasar suka a gida da waje.
'Yan majalisar EU dai sun amince da wani kudiri da ya bukaci Indiya ta kawo karshen tashin hankalin da ke afkuwa a arewa maso gabashin jihar Manipur tare da kare tsirarun mutane da ke wurin.
Da take mayar da martani kan kudurin, Ma'aikatar Harkokin Wajen Indiya ta ce irin wannan "shisshigi ne" a harkokin cikin gida na Indiya "ba za a amince da shi ba" kuma " hakan na bayyana tunani irin na mulkin mallaka."