Birtaniya ta sanar da cewa za ta ayyana rundunar sojojin haya ta Rasha wato Wagner a matsayin haramtacciyar kungiyar ‘yan ta’adda inda ta ce rundunar ta kasance barazana ga zaman lafiyar duniya duk da cewa shugabanta Yevgeny Prigozhin ya mutu.
Gwamnatin Birtaniyan a ranar Laraba ta bayyana cewa za a kawo kudiri a majalisa domin ayyana rundunar a matsayin ta ta’addanci karkashin dokar ta’addanci.
Ayyanawar wadda a baya ‘yan majalisa suka taba amincewa da ita, za ta haramta goyon bayan Wagner wadda ta taka muhimmiyar rawa wurin kutsen da Rasha ta yi cikin Ukraine.
Haka kuma rundunar ta yi ayyuka a Syria da kasashen Afirka da dama. Sakatariyar Harkokin Cikin Gida Suella Braverman ta bayyana cewa Wagner “na da hannu a sata da kisa na rashin imani.
"Ayyukan da take yi a Ukraine da Gabas ta Tsakiya da Afirka barazana ce ga tsaron Afirka.
“A takaice ‘yan ta’adda ne – kuma wannan ayyanawar za ta zama a bayyane a dokar Birtaniya,” in ji ta.
Haramcin zai bayar da dama ga hukumomin Birtaniya su kwace kadarorin kungiyar, duk da cewa damar za ta kasance tamkar hoto sakamakon Wagner ba ta aiki a Birtaniya.
Wannan matakin ya biyo bayan shawarwari daga kwamitin majalisa kan harkokin waje a watan Yuli kan cewa a haramta Wagner.
Kwamitin ya ce hukumomin Birtaniya ba su dauki barazanar da rundunar take yi da muhimmanci ba.
Kwamitin ya bayyana cewa makomar Wagner ba ta da tabbas bayan Prigozhin ya yi kokarin yin tawaye ga manyan sojojin Rasha a watan Yuni.
‘Yan majalisa sun bayyana cewa akwai bukatar Birtaniya ta yi amfani da rikitaccen halin da ake ciki domin “lalata” Wagner.
Watanni biyu bayan tawayen watan Yuni, an bayar da rahoton kashe Prigozhin a wani hatsarin jirgin sama wanda ya faru a ranar 23 ga watan Agusta.
Wani bincike na wucin gadi da hukumar leken asiri ta Amurka ta kammala ya gano cewa an harbo jirgin ne a cikin gida.
Sai dai gwamnatin Rasha karkashin jagorancin Vladimir Putin ta musanta wannan zargin.