An yi bikin nadin Charles III a matsayin Sarkin Ingila a karon farko tun 1953, bayan mutuwar mahaifiyarsa Sarauniya Elizabeth II.
An yi masa nadin ne ranar Asabar da misalin karfe 11:02 a agogon GMT a cocin Westminster Abbey inda Acibishof na Canterbury Justin Welby ya dora masa kambin gwal a matsayin alamar sarauta.
An rika yi masa addu'ar "Allah Ya kiyaye Sarki" a cikin cocin mai dauke da mutum 2,300 sannan an rika rera sarewa da yin addu'oi a yayin da ake nadin nasa.
A wajen cocin, an rika harba bindigogi na ban girma da suka karade dukkan kasar yayin da aka kada kararrawa a coci-coci da ke Ingila.
Charles, mai shekara 74, zai sanya kambin St Edward's sau daya kawai a yayin mulkinsa. Matarsa, Camilla, mai shekara 75, an nada ta a matsayin sarauniya kawai.
Gabanin Charles da Camilla su bar Fadar Buckingham a cikin jerin gwanon motoci yayin da ake ruwan sama zuwa coci, 'yan sanda sun kama mutane da dama da ke zanga-zangar adawa da masarautar Ingila.