Duniya na taka-tsan-tsan da cututtuka masu yaduwa tun bayan cutar korona da ta bulla a 2020. / Hoto: Getty Images

Hukumomin lafiya a Birtaniya a ranar Litinin sun tabbatar da ganin wani sabon nau’i na wata mura a jikin bil adama mai kama da wadda ake gani a tattare da aladu.

Cutar mai suna Influenza A(H1N2)v na kama da wata mura wadda a halin yanzu take yaduwa a tsakanin aladu a Birtaniya.

Mara lafiyan da aka gano yana dauke da murar, ya warke sarai, amma tun da farko an gano yana dauke da ita ne bayan an yi masa gwaje-gwaje a kansa bayan ya yi ta samun matsalar numfashi.

Hukumomin lafiyar sun ce wannan ne karo na farko da suka gano irin wannan nau’in cutar a jikin dan'adam a Birtaniya duk da cewa cutar na kama da sauran cututtuka da aka taba ganowa a baya a jikin aladu.

Haka kuma sun tabbatar da cewa yanzu haka ana bibiyar wadanda mara lafiyar ya yi mu’amula da su domin yi musu gwaji da kuma ba su shawarwari kan matakan da za su bi idan suka ga suna ji alamu na cutar.

Fargabar kasashen duniya

Kasashen duniya na ci gaba da yin taka-tsantsan game da cututtuka masu yaduwa daga dabbobi zuwa mutane, musamman a daidai lokacin da duniyar ke ci gaba da farfadowa daga illolin da annobar korona ta yi.

Sama da mutum miliyan bakwai ne aka yi kiyasin cutar ta kashe a fadin duniya tun bayan bullar ta a farkon shekarar 2020.

AA