'Yan sandan Kenya sun hana zanga-zangar adawa da gwamnati a Nairobi

'Yan sandan Kenya sun hana zanga-zangar adawa da gwamnati a Nairobi

'Yan sanda sun ce gungun masu aikata laifuka ne suka jagoranci zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
'Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Nairobi babban birnin Kenya da kuma wasu biranen ƙasar. / Hoto: AFP      

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta haramta gudanar da zanga-zanga a tsakiyar Nairobi babban birnin kasar har zuwa wani lokaci.

Matakin hakan ya biyo bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka shafe makwanni ana yi, wadda rundunar ta ce wasu gungun masu aikata laifuka ne suka kutsa shi.

Wasu masu fafutuka sun yi kira ga jama'a da su hallara a ranar Alhamis dauke da kayayyakin da za su kafa sansanoni don ''mamaye" dandalin shaƙatawa na Uhuru da ke daura da tsakiyar birnin duk kuwa da kasancewar 'yan sanda a fadin Nairobi.

Akalla mutum 50 ne aka kashe a zanga-zangar adawa da shirin ƙara haraji da matasan Kenya suka jagoranta a fadin ƙasar wata guda da ya gabata.

An ci gaba da zanga-zangar duk da matakin janye dokar da kuma korar kusan dukkan ministocin ƙasar da Shugaban William Ruto ya yi.

Masu fafutukar dai suna son Shugaba Ruto ya yi murabus, sannan sun ɓukaci a yi gyara domin tsaftace cin hanci da rashawa da kuma magance rashin shugabanci nagari a Kenya.

Kutsen laifuffuka

''Muna da sahihan bayanan sirri da ke nuna cewa gungun ƙungiyoyi masu aikata laifuka na shirin amfani da zanga-zangar da ake ci gaba da yi wajen samun damar aiwatar da shirinsu na kai hare-hare da sata da kuma ƙwace,'' in ji shugaban 'yan sanda Douglas Kanja Kiricho a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

"Ba za a ba da izinin yin zanga-zanga a Babban Cibiyar Kasuwanci ta Nairobi da kewayenta ba har sai nan gaba don tabbatar da tsaoron al'umma."

Zanga-zangar wadda aka shirya ta intanet ba tare da nuna wani goyon bayan 'yan adawar siyasa ba, ta haifar da riciki mafi girma a shekaru biyu na mulkin Ruto a Kenya.

A wani sabon mataki da ya ɗauka kan buƙatun masu zanga-zangar, a makon da ya gabata ne Shugaba Ruto ya yi alkawarin kafa wata sabuwar gwamnati, sai dai gamayyar jam’iyyun adawa a ranar Larabar da ta wuce sun yi watsi da matakin, inda suka yi kira kan a yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.

Kutsa kai cikin majalisa

An fara zanga-zangar ne cikin lumana kafin daga baya ta rikiɗe zuwa tashin hankali da rikici.

A ranar 25 ga watan Yuni ne wasu daga cikin masu zanga-zangar suka mamaye majalisar dokokin ƙasar lamarin da ya sa ‘yan sanda suka bude musu wuta.

Ofishin Ruto ya shirya tattaunawa da “bangarori da dama” a wannan makon don magance korafe-korafen masu zanga-zangar, sai dai ya zuwa ranar Alhamis babu wata alama da ta nuna an fara.

Galibin jiga-jigan masu zanga-zangar dai sun yi watsi da gayyatar, a maimakon haka sun yi kira da a ɗauki matakan gaggawa kan batutuwan da suka shafi cin hanci da rashawa.

"'Yan sanda da Shugaba Ruto ba su da ikon dakatar da hakkokin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba da," kamar yadda wani mai fafutuka Boniface Mwangi ya wallafa a shafinsa na X a yayin da yake mayar da martani kan haramta yin zanga-zangar.

Gargadi ga kafofin yada labarai

Hukumar kula da harkokin sadarwa ta Kenya (CA) ta gargadi kafafen yada labarai da su kauce yada rahotannin da za su iya haifar da tashe-tashen hankula da tarzoma a ƙasar a cikin labaran da suke gabatarwa kan zanga-zangar. "

Wasu kafafen yada labarai suna ''kauce bin ka'idoji da rashin samar daidaito a rahotannin sa suke gabatarwa kan laifuka da tsaro a yanayin da ake ciki,'' in ji sanarwar da CA David Mugonyi ya fitar a ranar 17 ga yulin 2024 ga wani babban ma'aikacin kafar yada labarai da kamfanin dillancin kabarai na Reuters ya samu damar gani.

Reuters