Wata kotu a Kenya ta bai wa gwamnati izinin kwace kudin saboda matashiyar ta gaza bayanin yadda ta same su / Hoto: AFP

Wata Kotu a Nairobi babban birnin kasar Kenya ta bayar da umarni cewa gwamnati ta kwace kudi dala 873,660 wato daidai da kudin kasar Ksh miliyan 102, na wata mata 'yar kasar da aka ba ta kyauta.

Mai Shari'a kan yaki da cin hanci Esther Maina ce ta yanke wannan hukunci ranar Alhamis saboda an kasa bayani a kan kudaden wadanda aka tura asusun banki biyu na Kenya da Felista Nyamathira Njoroge ke ajiya.

Nyamathira ta samu kudin ne daga wajen wani saurayinta dan kasar Belgium Marc De Mesel, da ya raba su biyu ya aika daban-daban a watan Agustan 2021.

De Mesel, wanda mai amfani da shafin YouTube ne, ya tabbatar da cewa ya aika wa masoyiyar tasa kudaden, wadanda ya ce ya same su ne ta harkar kasuwancin crypto.

Mai Shari'a Maina ta bai wa gwamnatin Kenyan izinin ajiye kudin a wajenta, inda ta ce Nyamathira mai shekara 23 ta kasa yin bayani kan yadda saurayin nata ya samu kudi lakadan haka.

Mai Shari'ar ta ce kotu ta bukaci De Mesel ya je ya yi mata bayanin yadda ya samu makudan kudi haka, amma bai amsa gayyatar tata ba.

“Na gano cewa kudaden da suke cikin asusun ajiyar Nyamathir kudade ne na haram, don haka gwamnati ta kwace su," in ji Maina.

Hukumar Kwato Kadarori ta Kenya (ARA) ce ta shigar da karar inda ta nemi kotu ta kwace kudaden, tana mai cewa, matar, wadda dalibar jami'a ce a Kenya ta gaza yin bayani kan yadda ta zama miloniya a dare daya.

ARA ta zargi Nyamathira da cin gajiyar halasta kudin haram.

TRT Afrika