Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin cewa shirin Birtaniya na mayar da masu neman mafaka Rwanda bai halatta ba.
Manyan alkalan kotun guda uku a ranar Alhamis sun ce "bai halatta a mayar da masu neman mafakar ba har sai an gyara matsalolin da ke dabibaye da tsarin neman mafaka na Rwanda.
A karkashin shirin wanda gwamnatin masu ra'ayin rikau ta samar, za a mayar da masu neman mafakar da suka shiga Birtaniya ba da izini ba zuwa Rwanda.
Alkalan uku sun amince da 'yan cirani da masu fafutukar da suka gabatar da bukatar cewa gwamnatin Birtaniya ba za ta iya tabbatar da cewa ba za a mayar da masu neman mafakar da aka aika Rwanda zuwa kasashen da suka tserewa din ba.
"Mayar da mutane Rwanda ka iya karya wata doka ta Kare Hakkin Dan Adam ta Turai" wacce ta ce babu wanda za a azabtar ko a kaskantar ko kuma a wahalar da shi, in ji alkalan.
Martanin Rwanda
Gwamnatin Rwanda ta ce tana nan kan aniyarta ta bin yarjejeniyar masu neman mafaka duk da hukuncin kotun.
"Rwanda na nan kan aniyarta ta tabbatar da yiwuwar wannan hadin gwiwa," a cewar mai magana da yawun gwamnatin Yolande Makolo, a hirarta da kamfanin dillancin labarai na AFP.
"A yayin da wannan batu ya kasance wani mataki na tsarin shari'ar Birtaniya, muna da matsala da hukuncin cewa Rwanda ba kasa ce da masu neman mafaka da 'yan cirani za su samu tsaro ba."
Tsohon Firaministan Birtanyia Boris Johnson ne ya kawo kudurin shirin don magance matsalar yawan 'yan ciranin da suke tsallake kogi don shiga kasar daga Faransa a kananan kwale-kwale.
Amma lamarin ya jawo jerin zanga-zanga daga kungiyoyin kare hakkin dan adam da na masu ba da agaji, yayin da kotu ta yanke hukuncin dakatar da mayar da rukunin farko na 'yan ciranin a watan Yunin bara.