Hukumomin Rwandan sun gano gawarwakin yara 10 da suka nutse a Kogin Nyabarongo da ke yankin kudancin kasar a ranar Litinin.
Alice Kayitesi, gwamnan yankin Kudancin kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa daliban sun gamu da ifitila'in ne kwanaki kadan bayan da suka koma gida yin hutu daga makaranta, kuma lamarin ya faru da su ne a kan hanyarsu ta raka wani mutum unguwa.
Lamarin ya faru ne a Mushisiro da ke gundumar Muhanga da misalin karfe 5 na yamma agogon kasar. Yaran 'yan tsakanin shekara 11 zuwa 15 ne, kuma a ranakun Talata da Laraba ne aka tsamo gawarwakin nasu.
Mutum 14 ne suke cikin kwale-kwalen da ya kife da su din, ciki har da wani babba mai shekara 41 da ke tukawa.
Kai kayan gini
Tun a ranar Talata aka samu ceto babban mutumin mai suna Jean-Pierre Ndababonye da wasu yaran uku, kamar yadda 'yan sanda suka fada.
Mai magana da yawun 'yan sanda John Bosco Kabera ya ce Nbababonye ya yi hayar kwale-kwalen ne ya kuma ce wa yaran 13 su raka shi wani kauye mai makwabtaka da nasu da ke tsallaken kogi, inda suka taimaka masa kai wasu kayan gini da zai sayar.
Jirgin ruwan ya kife ne a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa kauyen Ndaro a gundumar Ngororero.
"Yara hudu, ciki har da Ndababonye ne suka tsira," a cewar Kabera, inda ya kara da cewa: "Ndababonye yana tsare a hannun 'yan sanda don fuskantar tuhuma."