Babbar motar tana gudu sosai lokacin da lamarin ya faru, a cewar ganau.  /Hoto: @ntsa_kenya

'Yan sanda da ganau a Kenya sun ce akalla mutum 48 ne suka mutu yayin da wata babbar mota ta kauce daga kan hanya sannan ta turmushe kananan motoci da dama da mutanen da ke tafiya a kasa a wani wuri mai cunkoson jama'a a yammacin kasar.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a a yankin Londiani da ke lardin Kericho.

Shugaba William Ruto ya bayyana hatsarin a matsayin wani abin takaici yana mai cewa cikin wadanda lamarin ya rutsa da su har da "matasa".

"Kawo yanzu mutum 48 sun mutu kuma ana fargabar cewa har yanzu akwai mutum daya ko biyu da suka makale a karkashin motar," a cewar wani jami'in 'yan sanda a yankin mai suna Geoffrey Mayek a hira da kamfanin dillancin labarai na AFP.

Ya kara da cewa fiye da mutum 30 ne suka samu munanan raunuka sakamakon hatsarin kuma an ruga da su asibiti, yana mai gargadin cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa.

"Muna zargin cewa wata babbar mota ce da ake tukawa... wacce ta nufi Kericho birki ya tsinke mata inda ta fada kan kananan motoci a wurin tsayawar motoci," in ji Mayek.

Collins Kipkoech, wani babban likita a asibitin Kericho, ya ce an kai musu gawar mutum 45 ya zuwa lokacin da yake magana, yayin da aka tafi da wasu gawarwakin wasu asibitocin "kuma har yanzu ana ci gaba da aikin ceto".

Hukumar kiyaye hadarurruka a Kenya ta sha gargadin masu manyan motoci su daina tukin ganganci./Hoto: @ntsa_kenya

Hotunan da gidajen talabijin na kasar suka fitar sun nuna yadda babbar motar ta make kananan motoci a fitacciyar mahadar ababen hawa ta Londiani.

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya ya rika kawo cikas a yunkurin ceto mutanen da hatsarin ya rutsa da su, a cewar kafafen watsa labaran kasar

"Babbar motar tana gudun wuce-sa'a ne lokacin da lamarin ya faru. Ta yi kokarin kauce wa motoci da dama amma ta fada cikin kasuwa," a cewar wata ganau mai suna Maureen Jepkoech.

TRT Afrika da abokan hulda