Hukumar takaita aukuwar bala’o’i a Ghana NADCO ta shawarci al’ummar kasar da su daina yin gini ko kafa shagunan kwantena a karkashin fal-wayar wutar lantarki.
Babban Daraktan hukumar na gundumar Kadjebi, Nana Obaoka Joseph ne ya bayyana haka a yayin hirarsa da kamfanin dillacin labarai GNA a yankin Oti.
Ya ce igiyoyin wutar lantarkin da ake hada fal-wayar da su suna da nauyi don haka akwai yiwuwar su iya fadowa kasa ko kuma gobara ta auku a kowane lokaci idan wayoyin suka hade da juna.
Ya gargadi mazauna garin da kuma sauran al'ummar Ghana da ke zaune a karkashin wayoyin lantarki da su daina domin "rayuwar mutanen da ke zama a ire-iren wannan wuri na cikin hadari" da ka iya kai wa ga rasa rayukansu.
Nana Obaoka Joseph ya kara da cewa ya kamata a yi gini ko kafa shagon kwantena a wurin da ke da nisan mita 5.5 daga inda fal-wayar lantarki take don gudun mummunan abin da ka iya faruwa.
''Abu ne mai matukar hatsari yin gine-gine a kusa da fal-wayar lantarki, yin hakan na iya haddasa gobara da za ta nakasa ko kashe mutane da haddasa asarar dukiyoyi," in ji shi.