Wani kwale-kwale dauke da dalibai ya kife a kogin Calabar-Oron a jihar Cross River da ke kudu maso kudancin kasar.
Gidan talbijin na Nigeria Television Authority, NTA, ya bayyana cewa kwale-kwalen yana dauke da daliban da ke karatun aikin likita 14 yayin da ya kife.
A sakon da NTA ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar da tsakar dare ya ce daliban, karkashin kungiyarsu ta NIMSA , sun je Calabar ne a wani bangare na bikin da suke yin shekara-shekara amma sai suka yanke shawarar shiga kwale-kwale don kashe kwarkwatar idanunsu a wurin shakatawa na Calabar Marina Resort.
Sai dai "abin takaici shi ne kwale-kwalen ya kife" amma dalibai 14 sun yi sa'a bayan da jirgin rundunar sojin ruwa na kasar, wanda ke kusa da su a lokacin, ya yi gaggawar ceto su.
Amma har yanzu ba a ga dalibai uku ba kuma ana ci gaba da nemansu, a cewar NTA.
Ana fuskantar hatsarin kwale-kwale lokaci zuwa lokaci a Nijeriya sakamakon sanya mutane fiye da kima da kuma rashin ingancinsu.
A farkon watan nan, wani kwale-kwale da ya kwaso fiye da mutum 300 ya yi hatsari a jihar Kwara da ke arewacin kasar lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 150.
Hukumomi sun sha cewa suna daukar matakan dakile wannan matsala amma lamarin ya ki ci ya ki cinyewa.