Jama'a sun taru a wani wuri da ake zargin an samu tsiyayar iskar gas mai guba./ Hoto: Reuters

Akalla mutum 16 ne suka mutu ciki har da kananan yara uku sakamakon shakar iskar gas mai kunshe da sinadari mai guba na nitrate.

Masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne suke amfani da nitrate wajen gyara zinare, kamar yadda rundunar 'yan sandan Afirka ta Kudu da hukumomin kasar suka bayyana.

Tun da farko, hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce mai yiwuwa mutum 24 ne suka rasu sakamakon lamarin a lardin Gauteng da ke wajen gabashin birnin Johannesburg.

Amma 'yan sanda da Firimiyar lardin Gauteng Panyaza Lesufi daga bisani sun ce an tabbatar da cewa mutum 16 ne suka mutu bayan an kirga gawarwakin da aka gano.

"Abin babu kyawun gani…yana da tayar da hankali, yana da sosa rai da damuwa," in ji Lesufi, wanda ya ziyarci inda lamarin ya faru, kamar yadda aka ambato shi yana magana da manema labarai.

Masu aikin ceto sun ci gaba da neman wadanda abin ya shafa har zuwa ranar Laraba da daddare.

"Ba mu dauko kowace gawa ba. Har yanzu gawarwakin suna wurin da abin ya faru," in ji kakakin hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar William Ntladi.

An ga masu bincike suna rufe gawar wani karamin yaro da wani bargo. An kuma hango wata gawa da aka rufe da wani farin kyalle.

'Yan sanda sun kewaye wajen da abin ya faru da wani kyalle mai ruwan dorawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

A birnin Boksburg ne mutum 41 suka rasa rayukansu bayan wata mota da ke dauke da iskar gas ta makale a wata gada kuma daga bisani ta yi bindiga a jajiberin Kirsimeti.

Ntladi ya ce mace-macen ranar Laraba sun faru ne sanadin tsiyayar iskar gas mai dauke da sinadarin nitrate mai guba daga wata tukunyar gas da aka ajiye a wata baca.

TRT Afrika da abokan hulda