'Yan sandan Ghana sun ce ana ci gaba da neman sauran mutanen da ke da hannu a lamarin. Hoto/Rundunar 'yan sandan Ghana

Rundunar 'yan sandan Ghana ta kama mutum hudu da take zargi da yi wa wata Bafulatana tsirara bayan sun lakada mata duka.

Lamarin ya faru ne a yankin Kupelga da ke lardin Upper East na kasar.

Wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta a kasar ya nuna matar tsirara – ana lakada mata duka kuma ana cin zarafinta. Wannan abu ya tashi hankalin al'ummar kasar.

Mutane da dama a kasar sun yi kira da a kama sannan a hukunta wadanda ke da alhakin duka da yi wa matar tsirara da ma daukarta a bidiyon tsawon minti biyu da dakika 19.

Hakan ne ya sa rundunar 'yan sandan kasar ta kaddamar da farautar mutanen.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, rundunar ta ce ta kama mutanen hudu da ake zargi da "cin zarafin" matar.

Mutanen su ne Awizore Amolt, Akolbila Asorwogo, Atibila Aladago da kuma Akolbila Ben, kuma an kama su ne "a wani samame na 'yan sandan sirri" bayan binciken farko da aka yi a kan bidiyon.

Mutanen sun taimakawa wajen gudanar da bincike a yayin da ake "ci gaba da neman sauran wadanda suka aikata" laifin.

A nata bangaren, ma'aikatar da ke kula da jinsi da yara da kare hakkokinsu ta kasar Ghana ta yi Allah-wadai da al'amarin.

"Bai dace a karfafa wa masu cin zarafi da wulakanta mata gwiwa ba, musamman idan aka yi la'akari da yadda hakan yake shafar lafiyar lafiyarsu da tunaninsu. Mun yi Allah-wadai da wannan. Yin hakan take hakkinsu ne da mutuncinsu kuma doka ta tanadi hukunci ga masu aikata hakan," in ji wata sanarwa da ta fitar .

TRT Afrika