Hukumar tsaro ta Nijeriya DSS ta ce ta gurfanar da shugaban Babban Bankin kasar da aka dakatar Godwin Emefiele a gaban kotu.
DSS ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis da daddare.
Sanarwar, wadda kakakinta Peter Afunanya ya sanya wa hannu, ta ce "bayan umarnin wata babbar kotun Abuja a yau, 13 ga watan Yuli, Department of State Service (DSS) ta tabbatar da cewa an tuhumi Mr Godwin Emefiele a gaban kotu kamar yadda kotu ta bayar da umarni."
Ta kara da cewa tun shekarar 2022 ta nemi izinin kotu domin ta tsare shi bisa zargin aikata laifuka.
"Ko da yake ya samu umarnin kotun Abuja na hana kama shi, amma hukumar ta kama shi a watan Yunin 2023 bisa sabbin zarge-zargen aikata laifuka, daya daga cikinsu shi ne wannan tuhuma da ake yi masa," in ji DSS.
A watan jiya ne shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele daga mukaminsa.
Wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan sadarwa a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, ta ce an dakatar da shi ne bayan an gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
Daga bisani ne hukumar tsaro ta DSS ta ce Godwin Emefiele yana hannunta.
Sai dai ya kai ta kotu inda ya bukaci ta sake shi.
Sauye-sauye
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa 'yan kasar cikin mawuyancin hali sannan 'yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da zummar cin zarafinsu.
An nada Emefiele a matsayin shugaban Babban Bankin Nijeriya a 2014 bayan an dakatar da Sanusi Lamido Sanusi.