Gwamnatin Kenya na son kungiyoyi masu zaman kansu su rinka bayyana ayyukan da suke yi./ Hoto:AA

Daga Dayo Yussuf

A watan jiya, gwamnatin Kenya ta gargadi kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ta ce ba su bin ka’idar da kasar ta shimfida wurin gudanar da ayyukansu.

Babban sakataren harkokin tsaron cikin gida da gudanarwa na kasar Raymond Omollo ya nuna damuwarsa cewa wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu ba sa fitowa suna bayyana yadda suke samun kudinsu da yadda suke kashe su.

Omollo ya yi wannan batun ne a lokacin da ake kaddamar da rahoton shekara-shekara kan kungiyoyi masu zaman kansu a Nairobi inda ya ce ya yi mamaki kan adadin kungiyoyi masu zaman kansu da suka gaza bayar da rahoton kudaden da suke samu kamar yadda doka ta tanada.

“Wannan ya isa a sani cewa akwai wadanda suke da hannu a wasu abubuwa da suka shafi daukar nauyin ta’addanci,” kamar yadda ya yi zargi. Bai fito fili ya bayyana sunan wata kungiya ba.

Wuce gona da iri

A tsawon shekaru, an rinka samun rashin jituwa tsakanin gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje da kungiyoyin da ke bayar da agaji a wasu kasashen waje.

Wasu daga cikin kungiyoyin na cikin gida da kuma na waje, ba shakka suna bayar da muhimmiyar gudunmawa wurin tallafawa ci-gaban tattalin arziki da kuma siyasar kasashen.

Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu suna taimakawa wurin habaka tattalin arzikin kasashe inda suke taimakon kananan sana'o'i./Hoto; Reuters

Amma wasu daga cikin kungiyoyin musamman na kasashen waje ana zarginsu da wuce gona da iri, inda suke yin katsalandan kan harkokin cikin gida na kasashen da suke yin aiki da kuma goyon bayan wasu tsare-tsare da gwamnatocin kasashen ke adawa da su.

Da gaske ne wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu suna da hannu idan ana batun rashin girmama dokokin kasa, kamar yadda shugaban majalisar kungiyoyi masu zaman kansu ta Kenya Steve Cheboi ya bayyana.

Duka kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suke da rajista a Kenya na karkashin inuwar wannan majalisa. “Muna bayar da kwarin gwiwa ga mambobinmu da su rinka bayar da rohoton shekara-shekara.

Su rinka bayyana nawa suke samu a duk shekara su kuma bayyana yadda suka kashe wadannan kudade,” kamar yadda Mista Cheboi ya shaida wa TRT Afrika. “Idan ba su bayar da hadin kai ba, abu ne da za a iya cewa wani zai zarge su,” kamar yadda ya kara da cewa.

Tambayar siyasa

Sai da Robert Muigai, wanda mai kare hakkin bil adama ne kuma lauya da kuma tuntuba a Kenya ya shaida cewa a wani lokacin jami’an gwamnatin na kokarin yin katsalandan kan harkokin kungiyoyi masu zaman kansu domin su goyi bayansu musamman a lokutan siyasa.

“Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu musamman wadanda suke aiki ta bangaren siyasa, sun sha fuskantar katsalandan daga gwamnatoci lamarin da ya kai su ya baro,” in ji shi.

A arewa maso gabashin Nijeriya, kungiyoyi da dama masu zaman kansu na aiki ne kan bayar da agaji ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa. Hoto/Reuters

Amma lamarin bai tsaya a Kenya ba. Tun da farkon watan Maris din bana, gwamnatin Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta dakatar da ayyukan duka kungiyoyi masu zaman kansu a jihar – na cikin gida da na waje – inda ta zargi wasu daga cikinsu da katsalandan a siyasa gabannin zaben gwamnan jihar.

“An gano cewa kungiyoyi da dama na shiga siyasa da sunan bayar da taimakon jin kai ga mutane,” kamar yadda gwamnan jihar Ahmadu Finitiri ya bayyana a wani jawabi da ya yi.

Saba wa al’adu

“Gwamnati ba za ta iya nade hannu tana ganin wadannan kungiyoyi masu zaman kansu suna kokarin karkatar da hankalin jama’a ba,” kamar yadda ya kara da cewa.

Gwamnatin Tanzania na da matsala da kungiyoyi masu zaman kansu inda hukumomi suka kwace lasisin sama da kungiyoyi masu zaman kansu 4000 kan abin da gwamnati ta kira “rashin bin ka’idar hada-hadar kudi.”

Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya sha sukar batun dokokin luwadi da madigo a kasar. Hoto/Reuters

A Uganda da Kenya, an ta ikirarin cewa akwai wasu kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje da ake zargi da tunzura batun yin dokokin amincewa da luwadi da madigo duk a karkashin shirin tallafa wa lafiya.

Gwamnatoci da dama da al’ummomi a fadin Afirka sun sha sukar duk wasu masu goyon bayan kungiyoyin LGBTQ inda suke cewa sun saba wa al’adunsu da addinai da harkokin rayuwa.

Kungiyoyi bara-gurbi

Duk da gargadin baya-bayan nan da gwamnatin Kenya ta yi kan “rashin bin ka’ida” da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suke yi, Steven Cheboi na ganin cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin hukumomi da kungiyoyin.

Wasu daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu na aiki ne ta bangaren kiwon lafiya domin inganta lafiyar al'umma. Hoto/Reuters

“Kenya ce kyakkyawar misalin yadda kungiyoyi masu zaman kansu ke aiki lafiya da gwamnati.

Akwai yiwuwar akwai wasu bara-gurbi ‘yan kadan amma akasarinsu suna da nagarta,” in ji shi.

“Mun san akwai abubuwan da ba su zo daidai da al’adunmu na Afirka ba. Akwai bukatar kungiyoyin sun rinka yin abubuwa daidai da al’adu da rayuwar kasashe,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Lauya Muigai ya ce duk da ba a goyon bayan saka takunkumi ga kungiyoyi masu zaman kansu, amma a cewarsa su ma akwai bukatar kungiyoyin su su girmama dokoki.

Duk da cewa akwai bukatar kungiyoyi masu zaman kansu su gudanar da ayyukansu ba tare da katsalandan ba, akwai bukatar a rinka duba ayyukansu kamar yadda ake duba na wasu bangarorin domin tabbatar da cewa akwai gaskiya a cikin lamuransu,” in ji shi.

TRT Afrika