Daga Coletta Wanjohi
Ana cikin yanayin zafi da ba a saba gani ba da wata safiya a karshen watan Janairu a birnin Nairobi na kasar Kenya.
Zafin ya kai matakin digiri 26 a ma’aunin salshiyas, lamarin da ya sanya mutane neman mafaka a karkashin duk wata inuwa da suka samu a gefen hanya, ko zama a cikin gidajensu don kauce wa zafin ranar.
Sai dai wannan yanayi na zafi bai damu Esther Gaceke ba, don kuwa tafiyarta kawai take a wata tsukakkiyar hanya da ke tsakanin kananan gidajen da dubban mutane ke zaune a yankin Kibagare, wata unguwa da ke wajen birnin Nairobi.
Ta daure falmaran dinta tamau a kugunta, a kokarinta na boye cikin da ke jikinta wanda ya fara girma – da ke nuna cewa ya kusa wata uku.
Esther, ‘yar shekara 15, na daga cikin dubban yara matan Kenya da ke nemar wa kansu mafita daga cikin da aka yi musu yayin da suke da karancin shekaru, su kuma dauki ragamar rayuwarsu.
An kiyasta cewa yara mata 330,000 ne suke daukar ciki duk shekara a Kenya, kamar yadda bayanan Asusun Kidayar Jama’a na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna.
Yawancin wadannan matsaloli sun fi faruwa a yankunan da babu ci-gaba sosai, inda yara mata suka fi samun kansu cikin tasku saboda tsananin talauci, da rashin samun abubuwan more rayuwa da ma rashin ingantattun makarantu.
Kazalika cin zarafin da mata ke fuskanta yana taka rawa wajen uzzura wannan lamari.
“Na san na jawo miki abin kunya, amma nan da wata shida zan haifi jariri, zan koma makaranta kuma za ki yi alfahari da ni… don Allah ki yi hakuri da ni.”
Neman nasara
A bara, gwamnatin Kenya ta kaddamar da wani kamfe a fadin kasar na neman “kawo karshen barazana uku” da suka hada da yi wa yara mata ciki, da cutar HIV, da cin zarafi a tsakanin ‘yan shekara 10 zuwa 19.
Daidaikun mutane da kungiyoyi ma na goyon bayan ganin yara mata sun ci gaba da rayuwarsu cikin nutsuwa.
A yammacin Kenya alal misali, matar gwamnan gundumar Kakamega ta kaddamar da wani shiri na mayar da yara mata makaranta. Zuwa yanzu yara 60 ne suka amfana da shirin.
Ita dai Esther ta san me take son yi sarai. Da yake tun tana karama take da sha’awar abin da ya shafi harkar gasa abincin fulawa, shi ya sa take burin bude shagon sayar da kayan kwalam na fulawa a birnin Nairobi nan gaba a rayuwarta.
“Na san na jawo miki abin kunya, amma nan da wata shida zan haifi jariri, zan koma makaranta kuma za ki yi alfahari da ni… don Allah ki yi hakuri da ni,” ta gaya wa mahaifiyarta, wacce ke zaune cikin kunci da bacin rai a gidansu mai daki biyu da aka yi da langa-langa.
Esther ta ce ta ji takaici sosai a lokacin da ya zame mata tilas ta bar makaranta saboda cikin da take dauke da shi. Sannan a gefe daya ga mahifinta babu lafiya, hakan ya sa nauyin iyalin duka ya koma wuyan mahaifiyarta.
Esther ta gaya wa TRT Afrika cewa: “Kwana da yunwa ya zame mana jiki ni da ‘yan uwana maza biyu. Da kyar da sidin goshi mahaifiyarmu ke iya ciyar da mu ukun. Ta dogara ne da neman aikin da ma bai dace da ita ba wanda ba ma kullum ake samu ba.
“Yanzu kuma ga shi na kusa haifar wani karin dawainiyar. Sai dai kuma ban fitar da ran samun ingantacciyar rayuwa ba a gaba.”
“Ki samu kwarin gwiwa”
“Hodiii hapa, nani yuko? (Gafara dai, ina masu gidan?),” wata murya ta rangada kira daga can waje cikin harshen Swahili.
Bayan ‘yan dakiku sai wata yarinya doguwa ta shiga gidan, fuskarta dauke da murmushi. Grace Wambui mai shekara 16 ta zauna kusa da Esther tana share mata hawaye.
Ba sai an gaya mata ba, ta riga ta san halin bakin cikin da Esther ke ciki – da yake ita ma ta haihu da karancin shekarun nata, sarai ta san takaicin da ke tattare da “cikin shege.”
Amma bayan shekara daya da rabi da haihuwar danta, tuni Grace ta shirya wa tunkarar sabuwar rayuwarta.
“Maman Esther, na zo ne na yi wa Esther ban kwana. Zan koma makaranta,” ta gaya wa mamar Esther, sannan ta juya ga kawarta.
“Kar ki damu Esther. Na san abin akwai wahala…amma kar ki ji tsoro, kar ki karaya, ki nutsu ki samu kwarin gwiwa kamar yadda kullum muke maganar, kin gane?”
Sabuwar rayuwa
Grace ta fita tana tafiya gaba gadi cikin nutsuwa da alfahari.
Ta daina damuwa da tsokana da cin fuskarta da wasu mutanen kauyen ke yi.
Duk inda ta ga mutanen da ta sani a kan hanya sai ta daga musu hannu, wasu kan yi mata fatan alheri kan komawa makaranta da za ta yi. Ga wadanda kuma ta lura ba su sani ba, takan gaya musu cewa za ta koma makaranta fa.
Duk inda ka zagaya a titi da lungu na kauyen Kibagare, babu komai sai zakwadi da murnar fara sabon zangon karatu.
Yara daga makarantun sakandare daban-daban suna ta kai kawo, wasu suna hanyar tafiya makaranta yayin da wasu kuma ke gaggawar komawa daga aiken da aka yi musu a gida.
Grace ta hadu da wasu ‘yan ajinta, kuma sun yi wasa da dariya sosai, suna tunawa juna cewa ya kamata karfe 3 na yamma ta yi musu a makaranta.
Tana isa gida sai ta samu har mahaifiyarta ta kammala hada mata jakarta.
“A lokacin da ‘yata ta samu ciki na yi matukar jin kunya da takaici,” ta shaida wa TRT Afrika. “A hankali dai yanzu hankalina na kwanciya, amma gaskiya na dandani takaici.”
Mahaifin Grace ya rasu shekara shida da suka wuce, kuma a yanzu duk dawainiyar Grace da ta ‘yan uwanta shida na wuyan mahaifiyarsu ne. Sannan a yanzu ga nauyin dan Grace da shi ma ya karu.
“Na yanke shawarar komawa makaranta, kuma na ji dadin daukar wannan matakin. Ina so na nuna wa mahaifiyata cewa zan iya komawa makaranta kuma zan gyara kuskurena na koma turbar tarbiyyar da ta dora ni a kai,” in ji Grace.
Ta zana jarrabawar kammala karamar sakandare kuma sakamakonta ya yi kyau sosai. Shekara daya bayan nan, sai ta samu gurbin karatu a wata makarantar sakandare ta kwana a kusa da gidanta.
Mahaifiyar Grace ta ce “da da da uwar tasa duka jarirai ne. Ta ci jarrabawarta sosai, ta yi kokari matuka a darasin Bayoloji. Na sha gaya mata cewa dole ne ta yi kokari ko don ta samu nasara ita da danta.”
A lokacin da ta gama kintsawa don tafiya, Grace ta rungume danta tsawon lokaci tana ce masa za ta yi nasara don shi.
“Burina shi ne na zama malama a Jami’ar Kenyatta a nan Kenya. Na san labarina zai zama mai cike da nasara,” ta fada a lokacin da ta mika wa mahaifiyarta dan.
A lokacin da ta dauki jakarta, sai mahaifiyarta ta tuna mata cewa ilimi shi ne kawai hanyar fita daga talauci da kunci, kuma dole ne ta jajirce ta yi nasara.
A lokacin da Grace ta samu kwarin gwiwar farko na komawa makaranta, sai labarinta ya zama cikakke – labarin wata yarinya mai son gyara kuskurenta da kuma cimma burinta.
Sannan labarinta irin na sauran yara mata ne da dama da suka haihu da karancin shekaru, amma a yanzu suka jajirce wajen gyara kuskure da inganta rayuwarsu.