Daga Kudra Maliro
Yayin da shugabannin duniya suke kokarin samun matsaya guda daya don magance matsalar dumamar yanayi, daidaikun mutane a nahiyar Afirka suna nasu kokarin wajen ganin sun yaki matsalar a kullum.
Daga Maroko zuwa Afirka ta Kudu, daga Kenya zuwa Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, akwai wasu matasa masu fafutikar yaki da sauyin yanayi da shekarunsu suke tsakanin 20 zuwa 26, wadanda suke gagarumin aiki a cikin nahiyar don ceto al'ummomi daga wani bala'i da ke gab da fada wa nahiyar.
Sun karkasu a kungiyoyi, babban aikin da suka saka a gaba shi ne ceto nahiyar. TRT Afrika ta tattaro bayanan wadannan 'yan gwagwarmayar.
Guillaume Kalonji daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo
Wannan wani dan shekara 25 ne daga garin Bukavu a kudu maso gabashin kasar kuma ya kafa kungiyar "Rise up Congo" a watan Fabrairun 2022 bayan ya samu kwarin gwiwa daga Vanessa Nakate, wata 'yar Uganda.
"Muna wayar da kan dalibai a kan dalibai fiye da 1,500 a biranen Kinshasa da Bukavu kan aikace-aikacen da ba su da illa ga muhalli," kamar yadda Kalonji ya shaida wa TRT Afrika.
"Mun bayar da gudunmuwa wajen yaki da sare itatuwa a kewayen kogunan Kongo ta hanyar shirye-shirye a intanet da taimakon kungiyoyin kasashen waje da kuma kungiyar Greenpeace," in ji shi.
Kalonji da tawagarsa suna shirye-shiryen wayar da kan jama'a kan daina sare itatuwa wanda ake yi saboda samun gawayin girki. Saboda rage wannan al'ada sun fita da hanyoyin kare gurbatar muhalli.
Sun kuma shuka daruruwan bishiyoyi a makarantu a kewayen Bukavu yayin wani taro kan sauyin yanayi na duniya a 2022.
Yanzu haka kungiyar tana tattara ra'ayoyin mutane kan shirin "27BP3BG project", wato wani shirin hako mai wanda a ganinsu zai jawo matsala ga kogunan Kongo, wasu abubuwa da ke taimaka wa muhalli.
Aqlila Alwy daga Kenya
Tana daga cikin masu fafutikar yaki da sauyin yanayi da ta shahara a garinsu na Malindi a kudu maso gabashin Kenya.
Tana da shekara 21, ta kafa wata kungiya da ake kira Blue Earth, wadda take aiki don gyara wuraren da sauyin yanayi ya fara lalatawa.
Aqlila ta fara babban aiki da ta sanya a gaba ne a watan Julin 2021, abin ya fara ne bayan da ta ga barnar da ambaliyar ruwa ta jawo a garinmu mai suna Malinda a shekarar 2015. Masana sun dora alhakin hakan ne ga sare itatuwa.
"Itatuwan da ake bukata a shuka don gyara muhallin mutanen yankin ne suka samar, wanda hakan yake taimaka musu wajen samun karin kudin shiga. Wannan ya sa daruruwan matasa suna sha'awar aikin kuma ya kara nuna jama'a muhimmancin yaki da sauyin yanayi," in ji ta.
Tana yawan kai ziyara tsohuwar makarantar sakandarensu don wayar da kan 'yan mata kan matsalar sauyin yanayi da samun daidaiton jinsi, da kuma yadda hakan ke shafar karatunsu da al'ummarsu da kuma ikon da Allah Ya ba su a hannunsu don kawo sauyi.
"Ina farin ciki dangane da ci gaban da aka samu a Malinda. Na fahimci cewa 'yan mata yanzu suna son batun sauyin yanayi, kuma yanzu muna bakin kokarinmu dangane da wannan batu da a baya mutane ba sa kaunar tattaunawa a kansa," in ji Aqlila.
Abu guda da yake yawan sa mata fargaba shi ne batun cewa mutanen Malinda za su sake fadawa fari wanda zai jawo matsalar abinci da kashe dabbobin da ake kiwo. "Saboda wannan dalilai ne na ce zan ci gaba da abin da nake yi," kamar yadda Aqlila ta shaida wa TRT Afrika.
Regina Magoke daga Tanzaniya
'Yar shekara 21, wannan matashiyar mai fafutika 'yar Tanzaniya, an fara yi mata kallon jagora a al'ummarta dangane da yaki da dumamar yanayi. Kungiyarta mai suna Green Sphere tana aiki ne don kare muhalli ta hanyar share dazuka a Mwanza, wato wani gari a kusa da iyakar Tafkin Victoria.
"Ina aiki da tawaga wacce ta kunshi mutum 15 da ke tsakanin shekara 14 zuwa 15 maza da mata," in ji Regina.
Green Sphere tana shuka bishiyoyi kuma tana koyar da yadda za a kare muhalli a makarantu a garinsu Regina. Har ila yau kungiyar ta kaddamar da shirye-shirye kan kare muhalli don amfanin mutane nan gaba.
"Yanzu haka tawagarmu tana aiki ta shafin sada zumunta da talabijin da rediyo da jaridu," in ji ta.
Yayin da Green Sphere take kokarin kawo sauyi har ila yau akwai sauran kalubale. Regina da mambobin kungiyarta suna fuskanci kalubale masu yawa da suka ba su wahalar magancewa a yanzu haka.
Babban kalubalen da suke fuskanta shi ne matsalar kudi wadda ta sa dole suka rage yawan aikace-aikacensu.
Mohamed El-hajji daga Morocco
Wani mai nazari a Jami'ar Sidi Mohamed Ben Abd Allah a Fez, Mohamed El-hajji, mai shekara 21, ana saka shi a cikin jerin 'yan Maroko da suka shahara kuma shugabanni a arewacin Afirka, kuma daya daga cikin mutanen da suka kirkiri fafutikar yaki da sauyin yanayi.
El-hajji ya yi nasarar hada kan matasa a yankinsa don shigowa tafiyar kwato wa muhalli hakkinsa.
Bayan darussan da yake bayarwa a aji, El-hajj ya kafa reshen kungiyar FridaysForFuture a Maroko a shekarar 2020.
"Ya kafa kungiyar don wayar da kan jama'a kan sauyin yanayi da kawo ayyukan ci-gaba da sauransu," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
El-hajji ya shafe tsawon yarintarsa a yankin karkakara da ke arewacin Maroko inda ya ga tasirin sauyin yanayi, ciki har da raguwar amfanin gona sakamakon fari a yankin.
Mutanen kauyen sun dogara ne kacokan a aikin gona, kamar noman olive da alkama. Yayin da ake samun rashin isasshen ruwan sama, kasar yanzu babu albarkar noma sosai kuma mutane na wahala, in ji shi.
"Na kuma fahimci cewa dalibai da dama sun bar makarantarmu saboda gurbatacciyar iska da wasu doyi daga rukunin masana'antu."
Tafadzwa Kurotwi daga Zimbabwe
Nan kuma wata 'yar shekara 23 wanda shi da hadin gwiwa da wasu suka kafa kungiyar Emerald Climate Hub, wata kungiyar sa-kai wadda ke yaki da dumamar yanayi.
Tafadzwa tare da abokan aikinta suna aiki don samar da hanyoyin magance matsalar sauyin yanayi ta hanyar fasaha da kirkire-kirkire.
Har ila yau kungiyarsu tana kokarin samar sa daidaito wajen raba damarmaki tsakanin matasa da mata. Tafadzwa ta fara tunanin zama mai fafutikar yaki da sauyin sanayi ne bayan da ta zama wakiliya a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi COP27 wanda aka yi a Masar.
"Na karfafa wa dalibai 600 gwiwa a Zimbabwe ta yadda za su gano hanyoyin magance matsalolin muhalli da kuma magance matsalar sauyin yanayi," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
"Kazalika mun yi nasarar shuka bishiyoyi 300 a al'ummarmu. Kungiyarmu ta yi nasarar tattaro wasu kungiyoyin kare muhalli 10 daga makarantu daban-daban don su rika wayar da kan jama'a kan sauyin yanayi da kuma damawa da mata da kuma matasa."
Tafadzwa ta samu lambar yabo ta aikin jinkai na The African Mirror Awards saboda gudunmuwar da yake bayarwa wajen kawo ci-gaba da kare muhalli.
Tana yawan magana a kafafen yada labarai kanana da na kasashen ketare kan yadda al'ummomi za su kare kansu daga matsalolin sauyin yanayi. Ta ce babban abin da take son cimma shi ne wayar da kan jama'a da kuma bukatar daukan matakan da suka dace a Afirka.
Yosimbom Yania daga Kamaru
'Yar shekara 18, ita ce shugabar kungiyar karfafa wa matasa gwiwa a Kamaru, kungiyar ta kunshi masu fafutika fiye da 80 wadanda suke yaki kan dumamar yanayi a yankuna biyar na nahiyar Afirka.
"Daya daga cikin abubuwan da nake alfahari da su shi ne tasirin da aikina yake a zukatan matasa a al'ummata a bangaren yaki da sauyin sanayi. Ba kawai Ina shigo matasa tafiyar ba ne, amma kuma muna ankarar da su kan yadda za su gyara dabi'unsu don dacewa da manufofin yaki da sauyin yanayi da ci gaban kai," kamar yadda Yosimbom ta shaida wa TRT Afrika.
An kafa kungiyar karfafa matasa gwiwa ta Kamaru wato Youth Empowerment Cameroon a watan Mayun shekarar 2023 don taimakawa "a gyara duniyarmu kuma a alkintata don mutanen da su zo nan gaba."
"Mun shuka bishiyoyi da 'ya'yan itace a makarantu. Suna daga cikin manyan ayyukanmu har kawo yau kuma malamai da dalibai da dama sun bayyana mana yadda suka ji dadin aikinmu," in ji Yosimbom.
Mariem Jradi daga Tunisiya
Mariem wata mai fafutikar kare muhalli ce mai shekara 24, ta kafa kungiyar Stop Pollution a birnin Gabès, wacce take yaki da gurbatar muhalli da ake samu daga sinadarai da masana'antu da ke yankin ke amfani da su.
Mariem ta fara tunanin kafa wannan kungiyar ne wadda yanzu take da mambobi fiye da 57, bayan ita da kawayenta sun gano irin tasirin sauyin yanayi ga yankin Gabes na Tunisiya saboda samun bunkasar masana'antu.
"Abin da aikinmu ya fi mayar da hankali shi ne wayar da kan jama'a sosai kan sauyin yanayi da karancin ruwa a Tunisiya. Har ila yau mun kaddamar da wani shiri ta intanet ke ilmantar da mutane kan rage amfani da leda da robobi," kamar yadda Mariem ta shaida wa TRT Afrika.
Kungiyar Stop Pollution ta riga ta hada gwiwa da asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da kungiyar RET inda ake bincike kan sauyin yanayi da matsalar karancin ruwa.