Daga Sophie Küspert-Rakotondrainy
“Yawan masu magana da harshen Mao yana raguwa!” Na ji wadannan kalamai a lokuta da dama daga masu nazari da 'yan siyasa a yammacin Ethiopia.
Idan na tambaye su me suke nufi, sai su ce min suna nufin yadda kananan kabilu a yankin suka daina amfani da harshen Mao, inda suka koma amfani da Oromo.
Yin amfani da harshe da kuma magana da shi abubuwa ne da suke bijiro wa mutum bayan fuskantar wani kalubale ko dama a rayuwarmu ta yau da kullum.
A lokuta da dama, ana yi wa harshen Mao kallon kaskanci da kyama. Magana da wannan harshe tana kara tabbatar da yadda ake ci gaba da ware masu magana da shi.
Ko da yake ba za mu iya cewa kai-tsaye rashin magana da wani harshe da wasu mutane suke yi da "asara" ce.
Sai dai yana kyau ka yi wa batun raguwar masu magana da harshen kallon fahimta, don bincike kan bambance-bambancen zamantakewar da ke tsakanin mutane da kuma bincike kan yadda mutane ke kimantawa da martaba harsuna mabambanta.
Kudin goro
Ana kallon kabilar Mao a matsayin kabila a tsakanin kabilun kasar Ethiopia, Mao sun kai kimanin mutum 43,500 a yankuna da dama da ke makwabtaka da yankin Yammacin Welega Zone na jihar Oromia da kuma yankin kudancin jihar Benishangul Gumuz.
Mutane da ake saka su sahu daya "Mao" suna iya magana da harsuna shida, sai dai akwai al'ummomi da dama da ke tafiyar da rayuwarsu daban kuma suke da al'adu daban-daban kuma suke matsayi iri-iri a zamantakewa yau da kullum.
Wannan yana nufin akwai Mao da ake martabawa akwai kuma wadanda ake dannewa.
Yanayin matsayinka a al'umma yana da alaka da kasancewarka Mao da yadda aka fassara hakan ta fuskar wasu abubuwa kamar asalinka da arzikinka da kuma siffar halittar mutum.
A wasu yankuna a jihar Benishangul Gumuz, ana martaba Mao a siyasance don akwai wasu alfarmomi da hakan ke zuwa da shi, ko da yake ba a amincewa da hakan a jihar Oromia.
Yayin da mutane suke fuskantar wadannan mabambantan kalubale, suna zabar abubuwan da za su ba muhimmanci wadanda suka bambanta su da sauran Mao.
Yayin wani nazari da aikin da na yi a Yammacin Ethiopia tun shekarar 2017, na ci karo da wasu yara wadanda iyayensu wadanda suka iya magana harshen Mao daya ko fiye daya, sai dai suna amfani da harshen Oromo ne wajen magana wanda hakan bincike ya tabbatar da hakan.
Gaurayewar asali
Iyalan da ba sa zaune a kauyuka wanda yaransu suke zuwa makaranta ba su da kwarewa a harsunan da ba na Oroma ba.
Sai dai "kasancewarka Mao" da kuma yadda kake bayyana hakan ya bambanta tsakanin mutane wadanda asalinsu yake daban-daban kuma suke rayuwa a yankuna daban-daban, wannan ikirarin ya sa ake ganin harshen "ya fara mutuwa" kuma saboda haka ake ganin "asalinsa" ya fara samun nakasu. Babu wata fassara kwaya daya da za ta iya fassara ma'anar Mao, kuma akwai harsunan Mao fiye da daya.
Yayin da asalinsu yake gaurayewa, yanayin zamantakewa da sauran bambance-bambance abubuwa ne "da ba za a iya rasa su ba kuma a same su."
Kodayake harshe yana da muhimmanci sosai wajen tabbatar da asalin mutum, amma hakan ba ya nufin sai mutum ya kware sosai wajen iya magana sosai da harshen sosai.
Wannan ke nuna cewa "mutuwar harshe" ya wuce gaban kawai rage magana da harshen.
Al'adun mutane 'yan kabilar Mao ko al'ummomi ba sa mutuwa don kawai sun zabi su rika magana da wani harshe bayan na iyayensu, ko kuma wani harshe da suka zaba da kansu.
Wasu al'ummomin Mao ba su taba magana da harshen da Mao ba, ko kuma suna magana da harshen da al'ummonin da suka wuce na baya ba sa kiransa da sunan "Mao".
Da kwararren mai nazari kan harsuna irinsu Saliko Mufwene, ba za mu iya cewa wani yadda harshensu zai kasance ba da kuma yadda ya kamata su raya "al'adu da asalinsu."
Akwai matsala idan aka cewa mutanen Mao cewa za su "rasa" wani abu idan suka yi magana da wani harshe bayan nasu, saboda hakan ba ya rasa nasaba da al'ada da asali kuma hakan yana hana kananan kabilu da suke da tsohon asali sauyawa.
Zolaya da tsangwama
Ya kamata mu kawar da kanmu daga batun mutuwar harshe zuwa ga batun nuna wariya da yadda ake danne wasu kuma wannan ne zai bayyana yadda tsare-tsaren zamantakewa yake a yankin.
Ba za mu iya tabo batun sauye-sauyen harshe ba, ba tare da tabo batun tsangwama da ake nuna wa kananan harsuna ba, da kuma batun yadda wasu mutane sun sani, ko ba su sani ba suke zabar yin magana da harshen da ya fi kima ko martaba.
A lokuta da dama, ana fifita harshen Oromo a kan harsunan Mao. Danniyar da ake nuna wa wasu al'ummomi da matsayi mara kima da ake ba su yana da alaka da kasancewarsu Mao.
Nisanta kanmu daga yadda ake yi wa Mao kallon da ake musu zai taimaka wajen guje wa tsangwama. Kodayake ana yi wa mutanen da suke magana da harshen da ba na Oromo ba da wadanda suke "koma baya", a wasu lokutan masu magana da Oromo suna zaulayar ko kuma tsangwamarsu.
Mutane suna zabar harsunan da za su yi magana da su bisa dalilan da suka hada da matsayi a al'umma da fifiko maimakon zabi kan abin da ya fi dacewa. Akasin haka, ana zabin ne bisa la'akari da wasu manufofi da karfin iko.
Sai dai a daina kallon cewa kabilar Mao "za ta samu raguwa" idan suka zabi su shigo al'umma a dama da su, ko suka zabi yin magana da harshen da suka koyi magana da shi a al'ummar da aka fi magana da Oromo lokacin da suke tasowa, hakan ba a yi wa abin adalci ba.
Mutane za su iya magana da harshen Mao ba tare da sun fuskanci tsangwama ba, kuma za su iya magana da Oromo kuma su fuskanci wariya.
Ya kamata mu mayar da hankali kan bambance-bambancen matakai a harshe da al'ummomi zai taimaka mana wajen fahimtar girman batun rashin daidaito da sauyin da harsuna ke fuskanta, maimakon ganin yin magana da wani harshe zai jawo wa naka harshe "nakasu" ko "rusa asalinka."
Marubuciyar Sophie Küspert-Rakotondrainy, mai sharhi ce a Fannin Nazari da Tarihin nahiyar Afirka a Jami'ar Birmingham da ke Birtaniya.
A kula: Wannan ra'ayin marubuciyar ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.