Babban jami'in kamfanin Nigeria Air ya ce an aro shi ne daga Ethiopian Airlines don a kaddamar da shi. Hoto/OTHER

'Yan Nijeriya na tafka muhawara kan kalaman da mukaddashin Manajan Daraktan kamfanin jirgin sama na Nigeria Air Capt. Dapo Olumide ya yi cewa jirgin da aka gabatar wa 'yan kasar a matsayin sabon jirgin saman kamfanin a Abuja, sun dauko hayarsa ne daga kamfanin Ethiopian Airlines.

Mr Olumide ya bayyana haka ne ranar Talata a gaban 'yan kwamitin da ke sanya ido kan sufurin jiragen sama na Majalisar Dattawan Nijeriya.

Ya kara da cewa sun yi hayar jirgin ne don kawai su kaddamar da shi kafin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mika mulki ga sabuwar gwamnati.

A watan Yulin shekarar 2018 ne tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Nijeriya Hadi Sirika ya sanar da shirin sake dawo da kamfanin jirgin saman kasar wanda a shekarun baya ya durkushe.

Lokacin wani taro kan jiragen sama a birnin Landan, ministan ya bayyana suna da tambarin sabon kamafanin Nigeria Air.

Tun bayan hakan ne 'yan kasar suka ci gaba da sanya ido don ganin ranar da sabon jirgin zai fara aiki, amma sai abin ya ci gaba da jan kafa.

Abin da ya sa wasu 'yan Nijeriya sanya shakku kan shirin musamman ganin yadda suka yi fiye da shekara hudu ba su yi tozali da jirgin ba.

A kwanakin karshe na mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ne aka kaddamar da sabon jirgin Nigeria Air a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da sunan zai fara daukar fasinja bayan 'yan kwanaki.

Sai dai tun a lokacin wasu 'yan kasar suka fara sanya alamar tambaya kan batun musamman a kafofin sada zumunta.

Hakan ne ya sa kalaman da Mr Olumide ya yi suka tayar da kura a tsakanin 'yan kasar inda suka ce da ma an kaddamar da jirgin ne a matsayin wata "damfara"

Sai dai Malam Bashir Ahmad, tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce babu wata yaudara game da kaddamar da jirgin.

'Na cika da mamaki'

'Yan Nijeriya da dama sun rika tsokaci a shafukan intanet game da batun, inda suka bayyana mabambantan ra'ayoyi musamman a Twitter.

Wani mai amfani da Twitter, Kebuud Tyrant @yrnehh cewa ya yi: "Ni da ma zan yi mamaki sosai a ce wai mun sayo jirgin ne da gaske."

Akwai Always Humble @chinomsoOrakwu2 wanda ya ce: "Shin wadannan mutanen suna jin tsoron Allah kuwa. Idan aka tona asirinsu, sai su ce an tsane su ne, to me ya sa su ba sa kaunar gaskiya? Kalli irin abin kunyar da ya biyo baya."

Shi kuwa Muhammad Abubakar @mohamme39845158, wanda ya kare tsohuwar gwamnatin kasar, ya ce "Nigeria Air ba zamba ba ce. Ministan sufuri ya yi sosai don ganin an samar da shi. An kaddamar da sunansa da abokan hulda an kuma sanya hannu a yarjejeniya, an karbi shaida amincewa ya fara aiki kuma an bude ofisoshinsa. Nigeria Air zai fara aiki kuma zai sa Nijeriya ta yi alfahari," in ji shi.

Sai dai Olapoju Maxwell @pjmaxwell1905 ya mayarwa Muhammad martani. "Idan kamfanin Nigeria Air ba zamba ba ne, amma amfani da wani jirgin sama na wata kasa da sunan nasu ai zamba ce ko," in ji shi.

Lawal Ishaq @lawishaq: "Wannan mutumin ba shi da kunya kuma ya kamata ne a kore daga aiki idan ba zai iya ajiye aikinsa. Shirme!"

A karshe akwai Ibrahim Dembo @ibrahim_ud wanda shi ma ya tofa albarkacin bakinsa. "'Yan Nijeriya na bukatar cikakken bincike kan wannan al'amari."

Amma a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bashir Ahmad ya ce "NigeriaAir ba damfara ba ce, Ma'aikatar Sufirin jiragen sama ta samu gagarumin ci-gaba wajen tabbatar da shi...NigeriaAir zai yi aiki domin ya kasance abin alfahari ga Nijeriya."

TRT Afrika