Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da shugaban Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele nan take.
Wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan sadarwa a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta ce an dakatar da shugaban Babban Bankin Nijeriya ne bayan an gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
Zai mika ragamar tafiyar da bankin a hannun mataimakinsa Mr. Folashodun Adebisi Shonubi.
"An umarci Mr Emefiele da ya yi gaggawar mika harkokin ofishinsa ga Mataimakin Gwamna (Bangaren Gudanarwa), wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Banki na rikon kwarya kafin a kammala bincike da sauye-sauye," in ji sanarwar.
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa 'yan kasar cikin mawuyancin hali sannan 'yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da zummar cin zarafinsu.
An nada Emefiele a matsayin shugaban Babban Bankin Nijeriya ne a 2014 bayan an dakatar da Sanusi Lamido Sanusi.