Tinubu  ya ce za a kara yawan jami'an tsaron da ake da su kuma za a kara ba su horo /Hoto: Buhari Sallau

Daga Umar Rayyan

Bayan rantsar da Sabon Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu a dandalin Eagle Square da ke Abuja, ya gabatar da jawabinsa na farko a matsayin shugaban kasa, inda ya gode wa Allah, ya kuma yaba wa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Tinubu ya ce zai tafiyar da mulkinsa bisa bin doka da oda kuma ya yi alkawarin bunkasa tattalin arzikin kasar da samar da tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa da sauransu.

Ga wasu daga cikin manyan abubuwan da ya yi magana a kansu yayin jawabin nasa:

Magance matsalar tsaro

Sabon shugaban ya ce zai sauya fasalin tsaro a kasar, inda ya ce "wajibi ne mu kare kasarmu daga ayyukan 'yan ta'adda da duk wasu tashe-tashen hankula da ke barazana ga zaman lafiya da dorewar kasarmu."

"Samar da tsaro shi ne babban abin da za mu mayar da hankali a kai. Saboda babu yadda za a yi a samu ci gaba da adalci, idan akwai rashin tsaro da kuma tashe-tashen hankula," in ji shi.

Ya ce za a kara yawan jami'an tsaron da ake da su kuma za a kara ba su horo.

Sauya fasalin tattalin arzikin kasar

Shugaba Tinubu ya yi alkawarin cewa cikin 'yan kwanaki masu zuwa gwamnatinsa za ta fito da bayanai dalla-dalla kan sabon shirin sauya fasalin tattalin arzikin kasar.

Ya ce zai yi hakan ne don samar da ci gaba da kuma habbaka tattalin arzikin kasar. Ya ce hakan zai samu ne kawai ta hanyar samar da ayyukan yi da wadata jama'a da abinci da kuma kawo karshen matsanancin talauci.

Ya kuma yi alkawarin bunkasa samar da wutar lantarki.

Ya ce ma'aunin karfin tattalin arziki (GDP) na Najeriya zai samu ci gaba da akalla kaso 6 cikin 100.

Tinubu ya yi wa 'yan Nijeriya manyan alkawura bakwai /Hoto: Buhari Sallau

Game da masu zuba jari daga kasashen ketare kuwa, Tiinubu ya yi musu alkawarin rage jerin haraji barkatai da ake karba daga wurinsu. Ya kuma ce za a saukaka musu hanyoyin fitar da ribar da suka samu a kasar zuwa kasashensu.

Har ila yau ya yi alkawarin fito da sabbin tsare-tsaren aikin gona don samar wa manoman kasar kudin shiga yayin da kuma al'ummar kasar za su wadata da abinci cikin farashi mai rahusa, kamar yadda ya ce.

Zai rika bin doka da oda

Ya ce ba zai taba kasancewa mai mulkin kama karya ba. Ya ce zai yi mulki ne ta hanyar tuntubar kowane bangare da kuma bin doka da oda.

"Mun kawo wannan mataki ne don mu gyara al'amura, amma ba don kara bata su ba," in ji shi. Ya ce tun sake dowawar kasar turbar dimokuradiyya a shekarar 1994, ba a taba samun zabe mai sahihanci irin wanda ya kawo shi karagar mulki ba.

A cewarsa sakamakon zaben ya nuna abin da mutane suka zaba. "Sai dai hakan ba ya nuna cewa na fi abokan takarata zama dan Nijeriya fiye da su," in ji shi.

Ya ce wasunsu sun garzaya kotu don kalubalantar zaben. "Suna da hakkin yin haka. Kuma abin da suka yi shi ne abin da doka ta tanada," in ji sabon shugaban.

Zai samar da ayyuka miliyan daya

Kamar yadda ya yi alkawari lokacin yakin neman zabe, sabon shugaban ya ce gwamnatinsa za ta cika alkawarin samar da guraben ayyuka miliyan daya ga matasa a bangaren fasahar zamani.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi aiki da Majalisar Dokokin kasar don samar da dokoki da tsare-tsare da za su samar da ayyuka yi da taimaka wa talakawa da marasa karfi.

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta bai wa mata da matasa damarmaki sosai.

Cire tallafin mai

Game da cire tallafin man fetur ya ce kasafin kudin da aka yi kafin ya kama aiki a yau, daga abin da ya ji, an ce masa ba a yi tanadin kudin tallafin mai ba a ciki.

"Saboda haka babu sauran batun tallafin man fetur - tallafin mai ya kare. Babu dalilin da zai sa a ci gaba da kashe kudin tallafin mai wanda yake ci gaba da karuwa a daidai lokacin da ake karancin kudi," in ji shi.

Ya ce za a mayar da kudin tallafin ga wasu bangarori kamar ayyukan more rayuwa da samar da ilimi da kiwon lafiya da kuma samar ayyuka, wanda hakan zai inganta rayuwar al'ummarmu, a cewarsa.

Yaki da cin hanci da rashawa

Dangane yaki da cin hanci da rashawa, a jawabinsa sabon shugaban ya ce gwamnatin za ta ci gaba da yaki da matsalar ta hanyar karfafa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar. Ya ce "wannan aiki ne da ba za a iya gama shi ba."

Zai samar da farashin dala daya da kuma rage kudin ruwa

Shugaban ya ce ya zama dole Babban Bankin Kasar (CBN) da ya samar da farashin musayar dalar Amurka kwaya daya tal wato ba kamar yadda ake da farashi biyu ba a yanzu – farashin gwamnati da kuma na kasuwar bayan fage. Ya ce wannan zai canja a karkashin gwamnatinsa.

Tinubu ya sha rantsuwar kama mulki a Dandalin Eagle Square da ke Abuja /Hoto: Buhari Sallau

Dangane samar da yanayin yin kasuwar mai sauki, ya ce sabuwar gwamnatinsa za ta rage kudin ruwa.

"A halin yanzu kudin kuwar ya yi yawa, ba ya taimakon mutane, ba ya taimakon kasuwanci. Dole mu yi aiki a kansu duka," in ji shi.

Daga nan, sabon shugaban ya ce yana ba 'yan Nijeriya tabbacin cewa ba za su yi da-na-sanin zabensa ba.

Ya kuma gode wa wadanda suka zabe shi da ma wadanda ba su zabe ba. Ya ce zai yi adalci ga kowa da kowa ba tare da nuna bambanci ba.

TRT Afrika