Daga Abdulwasiu Hassan
Sabon shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, yana shan rantsuwar kama mulki a yau Litinin 29 ga watan Mayun 2023, don gadar Muhammadu Buhari wanda ya kwashe shekara takwas a kan mulki.
Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Nijeriya da aka yi a watan Fabrairu a karkashin jam’iyyar APC mai mulki.
Ya zama shugaban kasar na 16 kuma shugaban kasar na biyar tun bayan da Nijeriya ta koma tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
Shugaban, wanda ya dade a fagen siyasar kasar, ya yi yakin neman zabensa ne kan nasarorin da ya samu a lokacin da yake gwamnan Jihar Legas, inda aka yabe shi bisa habaka tattalin arzikin jihar tare da rubanya kudin shigarta da kuma ci-gaban masana’antu da harkokin sufuri.
Ya kuma gina ababen more rayuwa a babban birnin kasuwancin Nijeriya, ciki har da hanyoyi da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya.
Wannan ne yake bai wa wasu ‘yan Nijeriya irin su Nasiru Ringim kwarin gwiwa kan gwamnatin sabon shugaban kasar.
‘’Muna fatan cewar zai yi amfani da wannan damar wajen inganta abin da ya yi a baya,’’in ji Ringim a hirarsa da TRT Afrika Hausa.
‘’Ina yi wa wannan gwamnatin fatan alheri kuma muna yi mata kyakkyawan zato," a cewarsa.
Habaka tattalin arziki
Babban aikin da ke gaban Bola Tinubu bayan ya karbi mulkin kasa mafi karfin tattalin arziki da yawan jama'a a shi ne yadda zai magance matsalar tsaro da kuncin rayuwa da ke addabar 'yan kasar.
Sabon shugaban Nijeriyar ya shaida wa manema labarai cewa zai iya aikin da ke gabansa.
"Na huta kuma na shirya wa aikin da ke gaba,” a cewar Tinubu, bayan dawowarsa daga tafiyar da ya yi zuwa kasar waje kimanin mako biyu kafin a rantsar da shi.
Aikin da ke gaban Bola Tinubu "na bukatar tunani mai yawa da kuma daukar mataki," in ji Zuhumnan Dapel, wani dan Nijeriya mai bincike kan tattalin arziki a Cibiyar Nazarin Ci-gaba da ke kasar Canada.
"Aikin da ya fi dacewa ga sabon shugaban kasar shi ne ya bai wa ‘yan Nijeriya ingantaccen tattalin arziki," in ji Mista Zuhumnan a hirarsa da TRT Afrika.
Ya ce Nijeriya na bukatar kara yawan hanyoyin samun kudin shiga ga tattalin arzikinta ta hanyar kara zuba jari a fannoni daban da na man fetur irin su noma, wanda zai rage abincin da kasar ke shigowa da shi tare da kara kudin shiga ga gwamnati.
Amir Muhammad Harbo, wani mazaunin Jihar Jigawa da ke arewacin Nijeriya ya ce yana tsammanin gwamnatin Bola Tinubu ta dora daga inda gwamnatin Muhammadu Buhari ta tsaya.
‘’Sabuwar gwamnatin na bukatar daukar matakai na daidaita tattalin arziki tare da samar da ayyukan yi,’’ kamar yadda Harbo ya shaida wa TRT Afrika.
Ya yi imanin cewar idan aka ci gaba da samun ayyuka irin na matatar mai ta Dangote da aka kaddamar a makon jiya, kawar da rashin aikin yi tare da habaka tattalin arziki, to babban ci-gaba zai iya samuwa a Nijeriya.
Ya yi kira da a samar da ginshiki mai karfi ga fannin ilimi.
‘’Tsarin ilimin Nijeriya na bukatar garambawul, musamman ilimi a matakin farko,’’in ji shi.
‘’Sabuwar gwamnatin na bukatar zuba jari don inganta ilimi ga dukkan ‘yan Nijeriya,’’ in ji Amir. Yana ganin wannan zai sa kasar ta kasance ‘’ingantancen wuri ga daukacin ‘yan Nijeriya.’’
Dokta Isa Abdullahi, shugaban Sashen Koyar da Ilimin Tattalin Arziki a Jami’ar Tarayyar Nijeriya da ke Kashere a Jihar Gombe ya yarda da wannan shawarar.
Dokta Abdullahi ya ce sabuwar gwamnatin Nijeriya na bukatar ci gaba da yunkurin farfado da masana’antun kasar tare da tallafa musu don su taya gwamnati wajen samar wa mutane ayyukan yi.
Wannan, a cewarsa, zai taimaka wa tattalin arzikin kasar mai dagaro kan danyen man fetur.
“Hanya daya tilo da gwamanati ko al’umma za ta iya samar da ayyukan yi shi ne ta hanyar sarrafa abubuwa,” kamar yadda Abdullahi ya shaida wa TRT Afrika.
“Idan ba a sarrafa abubuwa, babu tattalin azriki. Idan ba a kera abubuwa, babu ayyukan yi. Idan babu sarrafa abubuwa, babu kudin shiga ga gwamnati,” a cewarsa.
Mabudin kyakkyawan aiki
Wata matsalar a Nijeriya kuma ita ce ta tsaro.
A wata hira da ya yi kwanan nan, Bola Tinubu ya yaba wa Muhammadu Buhari kan rage karfin ‘yan Boko Haram da suka kwashe sama da shekara 10 suna kai hare-hare a sassan kasar da kasashen Nijar da Kamaru da kuma Chadi masu makwabtaka.
Akwai kuma matsalar sace mutane don neman kudin fansa da ta ‘yan bindiga masu kai hare-kare da hukumomin Nijeriya ke neman shawo kansu.
“Ya kamata a samu hadin kai tsakanin hukumomin tsaro bakwai a cikin kasar don inganta tsaro,” in ji wani mai sharhi kan lamuran tsaro Kabiru Adamu yayin da yake hira da TRT Afrika.
Masana sun bayyana bukatar da ke akwai ta samar da hadin kai tsakanin al’umomi masu harshe da addinai daban-daban tare da inganta sauran fannoni da suka hada da kiwon lafiya da kuma samar da wutar lantarki.
Ana yawan kiran Nijeriya kasa ‘mafi girma a Afirka’ domin yawan mutanenta tare da karfin tattalin arzikinta da kuma jagorancin da take yi kan lamuran da suka shafi nahiyar.
Wannan, a cewar masu sharhi, wata manuniya ce ga kalubalen da ke gaban Bola Tinubu domin za a yi tsammanin cewar zai taka muhimmiyar rawa a cikin Afirka da ma wajen nahiyar baya ga lamuran cikin gida.
Mai bincike, Zuhumnan Dapel, ya ce sabon shugaban Nijeriyar na bukatar "sa masana" su yi aiki "da gaskiya" a ko wane fanni. "Idan ya yi wannan, zai yi nasara," in ji Dapel.