Mista Tedd Josia dan kasuwa ne a masana'antar fata a Nairobi./ Hoto: Tedd Josiah/shafin Twitter

Daga Coletta Wanjohi

‘Fata’ abu ne mai kyau da karfi da juriya da daukar ido, kuma daya ce daga cikin abubuwan farko da dan adam ya soma amfani da shi a rayuwa.

Sai dai wani abin mamaki shi ne yadda yawancin kayayyakin da ake samarwa da fata ke da wahalar samu a Kenya, kasar da ke da arzikin dabbobi, da aka alakanta wajen samar da arziki da wadata.

Farashin ‘yar karamar jaka ta wallet na kusan kai wa shilling 4,000, yayin da jakar hannu irin ta mata kan kai kusan shilling 42,000, kwatankwacin dala 300.

"Fatar leda ta masu kudi ce, idan aka yi la’akari da farashin yadda ake sayar da wadannan kayayyaki, a zahiri dai akwai wadanda aka kebe su don su saya,"a wata hira da TRT Afrika ta yi da Camila Njeri wata ‘yar kasar Kenya.

“Ban san dalilin da ya sa kayayyakin fata da ake samarwa a Kenya ke da wuyar samu ba; duk da cewa muna da shanu masu yawa a kauyukanmu!"

Da alamu dai Shugaba William Ruto ya fi kowa sanin irin albarkatu da kasarsa ke da su na yawan dabbobi da kuma rashin habaka masana'antar fata da ke barin kasar ta dogara da shigar da kayayyakin da ake yin su da fata cikin farashi mai tsada.

Shugaba William Ruto ya ce samar da ledar fatan a cikin gida zai ta sa kayayyakin fata su yi sauki a kasar. Hoto: Reuters

"Nan da shekaru biyu, zan hana shigo da takalma da ake hadawa da fatar leda daga wasu kasashen waje.

"Manufar ita ce mu tabbatar da cewa mun samar da takalma ta hanyar amfani da fata daga shanunmu na cikin gida" bayanan hakan na kushe ne cikin wani jawabi da Shugaba Ruto ya yi a kwanan baya.

“Mu a nan muna bai wa karnuka fatun da aka fitar daga jikin dabbobinmu, a gefe guda kuma muna ci gaba da shigowa da wadannan takalma masu tsada, kusan dala 200 ko ma dala 400 farashin kowanne,” Shugaban ya koka.

A cewar shugaban na Kenya, za a samu sauyi saboda "babu wata dabara ko sihiri a hanyoyin samarwa - fata ce ta shanu da aka sani tun da can.

Arzikin Kenya

Wani rahoto na shekarar 2019 da Ma'aikatar Harkokin Noma da Kiwo da kuma Kamun Kifi ta fitar, ya nuna cewa Kenya na da shanu sama da miliyan 18, da awaki miliyan 27, da tumaki sama da miliyan 17, da kuma rakuma miliyan uku da ake kiwonsu don samun nono da nama.

Ba a wani amfani da kayayyakin jikin dabbobi a Kenya yadda ya kamata. Hoto: Reuters

Fata na daga cikin abubuwan da ake samu daga jikin dabbobin bayan an yanka an kuma cire naman jikinsu wadanda ake bukata, sai dai ga dukkan alamu ba a cika amfani da fatar ba kamar yadda ya kamata a halin yanzu.

Wani bincike da kungiyar masu masana'antau ta Kenya ta yi ya nuna cewa a shekarar 2019, an shigar da takalman fata da sauran kayayyaki da farashinsu ya kai sama da dala miliyan 89.

Adadin da ya yi matukar tasiri, idan aka kwatanta da dala miliyan 70 da aka samu wajen fitar da makamantan kayayyakin a shekarar da ta gabata.

Wani bincike na daban da Cibiyar Bincike Kan tsare-tsaren kasa ta Kenya ta yi ya nuna cewa "duk da kasancewarta a matsayi na biyar a fannin kiwon shanu a Afirka, bayan Habasha da Chadi da Sudan da kuma Tanzaniya, darajar kudin da Kenya ke samu a cinikin fata na kasa sosai".

Yawancin kayayyakin fata da ake amfani da su a Kenya ana shigo da su ne daga waje. Hoto: Reuters

Shugaba Ruto ya yanke shawarar cewa a kasafin farko na shekara farawa daga ranar 1 ga watan Yulin 2023, masana'antar fata za ta samu kason kusan dala miliyan 14.

“Mahauta da ke sayar da faya a farashi kasa da dala daya ko kuma su jefar da su, yanzu za mu sanya musu farashi mai kyau na nama da fata,” in ji shi.

Kurarren lokaci

Tedd Josia, daraktan kamfanin kirkire-kirkire na Jokajok Luxury Leather, ya dukufa wajen hada kayayyaki iri daban-daban daga fatun dabbobin da ake samu daga Kenya da wasu kasashen Afirka.

"Za a iya samar da takalma da jakunkuna da sauran kayayyakin na fata a kasarmu don rage shigo da irin kayayyakin, sannan za a iya samar da daidaito a kasuwanci da kuma samar da ayyukan yi," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Masana'antun cikin gida sun ce suna bukatar karin tallafi daga gwamnati. Hoto: Tedd Josiah/Twitter

A yayin da samar da kayayyaki na Afirka ke da muhimmanci wajen samun ci gaba, Josia na ganin matakin da gwamnati ta yanke na mayar da hankali kan habaka masana'antar ya kure.

"Wadannan ne abubuwa da suka kamata a yi su - gina hanyoyin da za su karfafa tattalin arzikin kasa, hakan na nufin samar da sunaye masu karfi 'yan asalin Afirka mallakin 'yan Afirka don kafa tarihi," in ji shi.

Ya kara da cewa "Idan aka samar da samfuri mai kyau, zai iya rage farashin takalman makaranta.

"Sai dai takalman roba sun fi kwari kuma za a dinga shigowa da su daga kasashen waje, amma idan aka hada ko aka shigo da masana'antun da ke sarrafa roba ciki za a iya samun biyan bukata".

Rashin samun kasuwa

Beatrice Mwasi, daraktar Cibiyar kirkirar dabarun Kasuwanci da Horaswa, ta ce ci gaban masana'antar na fama da koma baya ta fuskar tsare-tsaren manufofi da aiwatarwa.

Darajar kason Kenya a kasuwar fata ta duniya, ya kai kusan dalar Amurka biliyan 150,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Habaka hanyoyin samar da kayayyaki na cikin gida zai taimaka wajen samar da karin ayyuka yi daga masana'antar fata ta Kenya. Hoto: Reuters

Mwasi ta ce babban kalubalen da ke gurgunta ci gaban da ya kamata a samu shi ne gazawar matsakaita da kanana masana'antu wajen su shiga gadan- gaban a dama da su cikin harkokin kasuwanci.

"Masana'antar ta na mamaye ne da wasu manyan kamfanoni da ke samar da mafi yawan kudaden shiga da ake samu sannan suna karfin tcusa kai cikin kasuwanni da ake da su," in ji ta.

Mwasi ta kara da cewa, "A bangare guda, kananan 'yan kasuwa da dama na fama da tasirin karancin kasuwanci. Kuma ya zuwa yanzu, mayar da hankali kan wasu manyan kamfanoni bai haifar da gasa a fannin ba."

TRT Afrika