A kalla mutum bakwai ne suka mutu a arewa maso gabashin Kenya a wasu hare-haren bam biyu da suka faru.
Mutum hudu sun rasa rayukansu ne bayan da motar da suke ciki ta taka nakiya a kan titin Banisa zuwa Mandera, kamar yadda 'yan sanda suka ce a ranar Laraba.
Sannan mayakan Kungiyar Al-Shabaab suka kai wa jami'an tsaron da suka kai dauki kan lamarin na farko hari.
Hukumomi sun ce hanyar da ke hada Banisa zuwa Mandera na da hadari saboda yadda Kungiyar Al-Shabaab ke yawan kai hari musamman ma kan motocin fararen hula.
Mutum uku ne suka mutu a harin na biyu, sannan biyar suka jikkata a kusa da iyakar Kenya da Somaliya bayan da su ma motarsu ta taka nakiya a ranar Laraba, in ji 'yan sanda.
Ba a gano wadanda ke da hannu cikin lamarin ba.
Amma Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Al-Shabaab, wacce ta shafe gomman shekaru tana kai hare-hare a kasashen Kenya da Somaliya, ta sha daukar alhakin kashe-kashe irin haka, saboda yadda take fafutukar ganin an janye dakarun kasashen waje daga Somaliya.