Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya biyu sun yi gargadi kan karuwar matsalar rashin abinci da ya haifar da matsananciyar yunwa a Sudan, sakamakon barkewar yaki a kasar da kuma a Haiti da Burkina Faso da Mali, saboda takaita zirga-zirgar mutane da kayayyaki.
Kasashen hudu sun bi sahun Afghanistan da Nijeriya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Yemen, wajen kaiwa kololuwar mataki a cikin jerin kasashen da tuni ke fuskanta ko kuma aka yi hasashen za su fuskanci yunwa ko fadawa cikin mawuyacin yanayi.
Rahoton kungiyar samar da abinci da ayyukan noma FAO da kuma shirin samar da abinci na duniya WFP, sun yi kira da a mayar da hankali wajen ceto rayuka da samar da ayyukan yi.
Baya ga kasashe tara da matakin da suke ciki ya matukar nuna damuwa, hukumomin sun ce an bayyana kasashe 22 da matsayinsu ya kai “kololuwa” wajen fuskantar barazanar matsalar rashin abinci.
"Hanyoyin kasuwanci kamar yadda aka saba ba za su zama wani zabi ba a wannan yanayin da ake ciki, idan har muna son cimma burin samar da wadataccen abinci wa duniya tare da tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba." A cewar Qu Dongyu, Darakta Janar na hukumar FAO.
Qu ya yi kira da a dauki matakin gaggawa a fannin noma don fitar da mutane daga fadawa kangin yunwa tare da taimaka musu wajen sake gina rayuwarsu da kuma samar da dauwamammiyar mafita ga matsalar karancin abinci.
Rahoton ya ba da misali ga rikicin da aka yi a Sudan da ka iya bazuwa wajen kara tabarbarewar matsalar tattalin arziki a kasashen da dama can suna fama da talauci.
Sannan akwai fargaba a hasashen yanayi na El Nino na tsakiyar shekarar 2023 da ya yi nuni da cewa akwai yiwuwar a fuskanci matsanancin yanayi a kasashe masu karamin karfi.
Rahoton ya kuma yi gargadi kan cewa, mutum miliyan daya ake sa ran za su tsere daga Sudan, yayin da wasu karin mutum miliyan 2.5 a kasar ke cikin hadarin fuskantar matsananciyar yunwa a 'yan watanni masu zuwa.
Hakan na faruwa ne sakamokon tsaikon matsalolin tsaro a hanyoyin shigowa da wasu kayayyaki kasar
Babban Darakta na hukumar WFP Cindy McCain ya yi gargadi kan fadawa cikin "mummunan bala'i", sai dai idan an dauki wani takamaiman mataki da za a bi wajen samar da sauyin yanayi da kuma takaita matsalar yunwa.
"Ba wai ana karin da ake samu na mutane daga wasu gurare ba ne kawai, duniya na fama da yunwa, kuma tsananin yunwar da suke fuskanta na dada muni fiye da kowane lokaci," in ji McCain
A watan Disamba, asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ya kuma yin gargadi kan cewa adadin yaran da ke fuskantar hadarin fari a kasashen Habasha da Kenya da kuma Somaliya ya ninka fiye da mutum miliyan 20.2.
Lamarin na ta'azzara ne sakomokon matsalar sauyin yanayi da rikice-rikice da hauhawar farashin kayayyaki da kuma karancin albakatun hatsi da ke mayar hannun agogo baya a yankin Gabashin Afirka.
"Yayin da duniya ke shirin maraba da 2023, hukumar UNICEF ta bukaci al'umma da su sadaukar da kansu a yanzu ga abin da ka iya riske yankin na Gabashin Afirka a shekara mai zuwa," in ji Daraktan UNICEF na Gabashi da Kudancin Afirka Mohamed Fall.
UNICEF ta nemi tallafin dala miliyan 759 don agazawa ayyukan ceton rai na yara a shekarar 2023.