Kasashe shida a Afirka na asarar akalla dala biliyan 2.3 a duk shekara saboda kamun kifi ba bisa ka'ida ba. Hoto: Getty

Daga Brian Okoth

Wani rahoto da Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta fitar kan yadda ake kamun kifi ya bayyana cewa kasashe shida suna asarar akalla dala biliyan 2.3 duk shekara sakamakon kamun kifi ba bisa ka'ida ba.

Kasar Gambia da Mauritania da Senegal da Guinea Bissau da Guinea da kuma Sierra Leone na asarar kudaden a duk shekara, a cewar rahoton.

A wani bincike da kungiyar ta gudanar a Gambia daga watan Yunin 2021 zuwa Afrilun 2022 ta gano cewa wasu kamfanoni na kasashen waje da ke amfani da na'urori na zamani suna yin kamun kifi ba bisa ka'ida ba a cikin ruwan kasar.

"Dole ne gwamnatin Gambia da wasu kungiyoyin kasashen waje da ke aiki a yankunan da abin ya shafa su tabbatar cewa jiragen ruwa na kasashen waje da masana'antun kifi suna mutunta dokokin kamun kifi na kasar da kuma na kasa da kasa," in ji Amnesty.

“Yana da muhimmanci al'ummomin yankin su ci gaba da samun damar kama kifi ta amfani da hanyoyin da za su dore.”

Kauyen Sanyang da ke gabar teku a kudu maso yammacin Gambiya, shi ya fi fama da wannan matsala ta kamun kifi ba bisa ka'ida ba, inda rahoton ya nuna cewa halin da ake ciki a wajen ya "tsananta".

A 2017 ne aka gina wata masana'antar sarrafa kifi ta kasashen waje a kauyen kuma bayan ta fara aiki a shekarar 2018, al'ummar yankin sun ce ayyukan raya tattalin arzikinsu sun yi kasa sosai.

Masu gidajen cin abinci da wuraren shakatawa da ke gabar tekun sun ce sun yi asarar kwastamominsu saboda warin da ke fitowa daga masana'antar.

Kazalika masunta a kasar sun ce manyan jiragen ruwa da kamfanonin kasashen waje ke aiki da su, sun matukar taimaka wajen rage yawan kifayen ruwan.

Amnesty ta ce "dole" hukumomin Gambia da kasashen duniya su dauki matakia yanzu don kare hakkin al'ummomin da ke kamun kifi da kuma kiyaye muhalli.

TRT Afrika