Daga Charles Mgbolu
Daya daga cikin asarorin da yakin da ake cigaba da fuskanta a Sudan ya haifar shi ne, koma baya wajen samun yalwar bishiyoyin karo da ake samu a kasashen nahiyar Afirka.
Karo na daga cikin muhimman sinadaran da masana’antu ke sarrafawa don amfanin duniya baki daya.
Sana'ar samarwa da kuma fitar da amfanin karo wanda ake hadawa cikin kayayyakin abinci da na sha da kayan kwaliyya da magunguna da kayyakin sawa da fenti da dai sauransu, kusan za iya cewa sun tsaya cak a Sudan, kasar da ta fi kowacce kasa samar da wannan sinadari.
Kimanin tan 120,000 na karo da darajarsa ta kai dala biliyan 1.1 ne ake samarwa a duniya a kowace shekara, a cewar kamfanin fasahar kayayyakin abinci masu gina jiki na MNC Kerry Group.
Kasashen yankin Sahel ke da tazara sosai daga gabas zuwa yammacin Afirka na da kashi 70% cikin abin da ake fitarwa a duniya, sai dai rikicin Sudan ya haifar da koma baya ga albarkatu da ake fitarwa da shi.
Karo wani sinadari ne da ake samu daga jikin bishiyar “Acacia”, ana shire shi bayan ya bushe ya yi tauri ya kuma dungule guri guda, muhimmi dai masana'antu ne suka fi amfani da shi wajen hada kayayyakin abinci.
A kowace rana, kazamin fadan da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin dakarun sojin Sudan da na Rapid Support Forces RSF masu gaba da juna, na dada zama barazana wajen kwace matsayin kasar wacce ta fi kowacce kasa a nahiyar Afirka fitar da amfanin karo zuwa kasashen waje.
Tuni dai aka karya logon kasuwancin karo a Sudan, inda masu samarwa da masu fitarwa har ma da kasar ke cikin yanayi na rudani.
Abin da ke gaba
Masu bukata ta musamman kan albarkatun ba su da wani zabi da ya wuce neman wasu hanyoyin da za su samu.
Nijeriya na iya ganin hakan a matsayin wata dama, la’akari da cewa ita ce ta fi samar da karo a kasashen yammacin Afirka, a cewar taron Majalisar Dinkin Duniya kan kasuwanci da ci gaba.
Sannan ita ce kasa ta uku a Afirka wajen sana’ar samarwa da fitar da albarkatun bayan Sudan da Chadi.
Wani masanin tattalin arzikin kasa a Najeriya Kevin Emmanuel bai musanta matsayin kasar wajen cike wannan gurbi ba, amma dai yana ganin cewa akwai bukatar a fara tunkarar wasu muhimman batutuwan cikin gida tukunna.
Emmanuel ya shaida wa TRT Afrika cewa, “Ana samun karo iri na Nijeriya daga jihohin Bauchi da Jigawa da Filato da Adamawa sai jihar Borno da ta fi ko wacce daga cikinsu.”
“Hakan bai zai wani taimaka sosai ba ganin wadannan jihohi da ke fama da kalubale ta fuskar tsaro. Kalubalen da ke tattare da ayyukan ta'addanci da 'yan fashi da makami a wadannan yankuna za su takaita yiwuwar cin amfanin damar," in ji shi.
Kungiyoyin masu dauke da makamai na yawan kai hare-haren ta hanyar satar shanu da garkuwa da mutane da kashe-kashe a wadannan yankuna, lamarin da ke shafar ayyukan noma da rayuwa baki daya.
Emmanuel ya ce ya san manoman da suka yi watsi da manyan gonakinsu na kasuwanci saboda tabarbarewar ayyukan yan ta’adda.
Kalubalen ba su tsaya kan matsalolin tsaro kadai ba. Kamar yadda Emmanuel ya yi nuni da cewa, yawan amfanin karo da ake samu daga bishiyoyin Acacia a Nijeriya “ba za su isa ba balle su kai matsayi na daya ba”.
Bishiyar Acacia na daukar tsakanin shekara hudu zuwa biyar kafin ta girma.
Hakan na nufin cewa dole itatuwan su kasance cikin yanayi mai kyau don su iya kai wa wadannan shekaru da manoma za su jira kafin sinadarin ruwan 'ya'yan itacen ya fara fitowa.
Taiwo Saruma, wani dan mai sana’ar kasuwancin karo tsakanin kasa da kasa, ya bayyana wani kalubale na daban.
“Akwai bukata ta mussamman kan irin dunkulen dankon karo mai daraja ta daya a kasuwa, shi aka fi bukata a kasashen waje kuma shi ne irin da Sudan ta fi samarwa, Nijeriya na da karancin irinsa, mu mai daraja ta biyu da ta uku kadai muke da su," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Kasar Senegal na samar da mai daraja ta daya na irin dankon karo, bishiyar Sayel tana samar da mai daraja ta biyu, sai kuma bishiyar Combretum da ke samar da iri mai daraja ta uku na karon.
An fi samun irin dankon karo na bishiyar Combretum ko itacen willow daga Yammacin Afirka, kuma ana siyarwa cikin farashi mai sauki.
Kasashen da ke shigowa da su don amfani kadana na kayayyakin abinci ba sa wani daukar da su da muhimmaci, idan aka kwatanta da irin na bishiyar acacia.
Karancin samun irin dankon karo na bishiyar acacia ya sanya Nijeriya a baya idan aka kwatanta da Sudan, wacce ke samar da dankon daga jikin kututturen bishiyar irin acacia na Senegal da Seyal acacia.
Bayanan da aka samu a taron Majalisar Dinkin Duniya kan kasuwanci da ayyukan ci gaba sun nuna cewa Nijeriya na samar da sama da tan 5,000 na dunkulen dankon karo a duk shekara, adadin da ke zama dan digo idan aka kwatanta da adadin da Sudan ke fitarwa a shekara na tan 88,000.
Saruma ya ce dole ne kasashen yammacin Afirka su dauki matakai da dama domin cike gibin da rikicin Sudan ya haifar.
"Abu ne mai sauki, muna bukatar karin wadannan nau'kan bishiyoyi irin Gradi na daya, da zarar mun yi haka, muna da kasuwa da ke jira mu a kasashen waje"
Hukumomin Najeriya za su iya bunkasa hanyoyin samar da kayayyakin ta hanyar kokarin inganta yanayin tsaro a yankunan da ake samar da danko karo da "ingantattun irin bishiyoyin", in ji masanin tattalin arziki Emmanuel.
Duk da cewa mafi yawan dankon karo ana samunsu ne daga arewacin Nijeriya, inda matsalar rashin tsaro ke kawo cikas a 'yan shekarun nan, ana samun nau'ukan da ake nema kamar su Acacia dudgeoni da Acacia gourmaensis da wasu nau'in iri na Acacia sieberiana da ake samu a wasu sassan Najeriya kamar kudu maso yamma.
"Dole ne gwamnati ta duba dukkan wasu bukatu na talakan manomi a Nijeriya, suna bukatar taki, kuma suna bukatar injunan noma na zamani, wadannan duk suna da muhimmanci wajen samar da adadi mai yawa na kasuwancin karo," in ji Emmanuel.
Hukumomin Nijeriya sun ce sun samar da iri daban-daban kusan miliyan 22 don ta da wani shiri da zai mai da hankali kan wannan sana’a ta karo har tsawon shekara 15.
Suna fatan ci gaba da samar da irin har miliyan 22 a duk shekara don dorewar wannan shiri da kuma bunkasa noman dankon na karo.
Kazalika akwai wasu kasashe a Afirka da ke da karfin noma wadanda suka hada da Mali da Senegal da Afirka ta Kudu da Kenya da Chadi da Kamaru da Somaliya da kuma Habasha da dai sauransu, kuma kowacce daga ciki na da irin nata kalubalen.
Yayin da bukatu daga kasashen duniya ke dada karuwa, ga Sudan na ci gaba da fama da rikici, a yanzu dai za a zuba ido wajen ganin kasar da za ta yi saurin amfani da wannan damar wajen samar wa kanta riba ta hanyar kulla yarjejeniyar kasuwancin dankon karo da ke da ribar gaske.