An shafe dare ana jin karar hare-hare ta sama a wajen Khartoum babban birnin Sudan inda kuma aka wayi garin Asabar da wannan kara, a yakin da ya shiga mako na shida ana gwabzawa.
Zuwa yanzu dai wannan yakin ya yi sanadin saka ‘yan kasar da dama cikin bala’i inda sama da mutum miliyan guda aka kiyasta sun rabu da muhallansu.
Yakin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar Rapid Support Forces ta RSF ya jawo rushewar doka da oda a kasar, lamarin da ya haddasa sace-sace inda kuma duka bangarorin biyu suke ganin laifin juna.
Tarin abinci da kudi da kuma ababen amfani na yau da kullum duk suna karewa. Wasu shaidu sun bayar da rahoton hare-hare ta sama a kudancin Omdurman da kuma arewacin Bahri, wadanda birane biyu ne da ke kan tekun Nilu daga Khartoum.
Wasu daga cikin hare-haren ta sama an kai su ne a kusa da kafar watsa labarai ta kasar da ke Omdurman,” kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya bayyana.
Wadanda suka shaida lamarin a Khartoum sun bayyana cewa an dan samu sauki, amma duk da haka ana jin karar bindiga ba kakkautawa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.
Karar makaman atilari da sanyin safiya
Rikicin wanda aka soma a ranar 15 ga watan Afrilu ya yi sanadin akalla mutum miliyan 1.1 sun rabu da muhallansu inda suka koma kasashen makwafta. An kashe wasu mutum 705 haka kuma akalla mutum 5,287 aka raunata, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Tattaunawar da Amurka da Saudiyya suka jagoranta a birnin Jeddah ba ta kawo wata maslaha ba, kuma duka bangarorin suna ta zargin juna da saba yarjejeniyar tsagaita wuta daban-daban.
“Mun ta fuskantar barin wuta na makaman atilari da safiyar nan, gidanmu gaba daya yana girgiza,” in ji Sanaa Hassan, wata ‘yar shekara 33 da ke zaune a unguwar al-Salha da ke Omdurman, kamar yadda ta shaida wa Reuters ta waya.
“Akwai tashin hankali, kowa ya boye a karkashin gado. Abin da ke faruwa tamkar wani mafarki ne,” in ji ta.
An bayyana cewa mambobin rundunar RSF suna cikin wuraren da al’umma suke, inda suke jawo karin hare-hare ta sama da sojojin ke yi.
A ‘yan kwanakin nan, an samu arangama da ake yi ta kasa a biranen Nyala da Zalenjei da kuma yankin Darfur.
Karuwar rikicin siyasa
Wani dan gwagwarmaya da ke Sudan ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya ji karar harbin bindiga ba kakkautawa a kusa da babbar kasuwar birnin da ke kusa da shelkwatar sojin kasar a safiyar Asabar.
Kusan mutum 30 ne suka rasu a wani rikci na kwanaki biyu da aka shafe ana yi, kamar yadda ya bayyana.
Rikicin ya barke ne a Khartoum bayan rashin jituwar da aka samu sakamakon yunkurin da rundunar sojin Sudan din ta yi na mayar da rundunar RSF din a cikinta, duk a kokarin da ake yi ko kuma shirye-shirye na mika mulki ga farar hula.
Wata alama ta karin rashin jituwar ita ce matakin da shugaban sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan ya dauka na korar mataimakinsa da ya zama abokin gaba wato Mohamed Hamdan Dagalo a ranar Juma’a.
Hamdan Dagalo shi ne kwamandan RSF, wadda ita ce rundunar da ke arangama da sojojin kasar. Bayan korar Dagalo, Janar Burhan ya nada mutum uku wadanda za su maye gurbinsa daga cikin rundunar sojin.
“Janar Burhan ya sanar da wata doka ta soji wadda ta ayyana Malik Agar a matsayin mataimakin shugaban kasa na majalisar mulkin soji,” kamar yadda majalisar ta bayyana a shafin Facebook.
Rundunar sojin ta kuma bayar da rahoton cewa Burhan ya sanar da Janar Shamsedding Kabashi a matsayin mataimakinsa, da kuma zabar wasu sojoji biyu masu biyayya a matsayin mataimakansa.
Agar, wanda tsohon shugaban ‘yan tawaye ne kuma gwamnan Jihar Blue Nile da ke iyaka da Sudan ta Kudu, ya saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Khartoum a 2020 kuma an saka shi a cikin majalisar mulkin sojin kasar a Fabrairun 2021.
Ya jagoranci kungiyar SPLM-North, wadda mayakan arewa suka kafa a 2011, kuma ta kai ga samun ‘yancin kan Sudan ta Kudu a shekarar.
Masu sharhi dai na ganin karin girman da aka yi wa Agar a matsayin wata alama wadda ake ganin ba lallai ta yi tasiri ba wurin gwagwarmayar mulki a kasa ta uku mafi girma a Afirka.