Mahukuntan Ethiopia sun kori mabiya addinin Kirista 80 da suka je kasar daga Uganda.
Mabiyan Cocin ‘Christ Disciples’ daga yankin Soroti na gabashin Uganda sun yi takkiya zuwa Ethiopia a watan Fabrairu, bayan da malamin Cocinsu ya yi ikirarin za su hadu da Yesu a kasar bayan sun yi azumin kwana 40, in ji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Uganda.
Mai magana da yawun ma’aikatar, Simon Mundeyi, ya shaida wa AFP cewa “Mun yi aiki da mahukuntan Ethiopia, mun tabbatar da sun dawo gida lafiya ba tare da wani abu ya same su ba.”
Mahukunta sun bayyana cewa jami’an tsaro da na leken asiri na hadin gwiwa sun saka sunan malamin Cocin Simon Opolot a jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo, kuma za a kamo shi.
Mundeyi ya ce mabiya cocin sun fito ne daga yankin Soroti a gabashin Uganda, kuma an fada musu su sayar da dukkan kadarorinsu saboda duniya ta zo karshe, sannan idan suka zauna da yunwa za a cece su a ranar gobe kiyama.
Mundeyi ya kuma ce “Suna azumi na kwana 40, inda a kwana na 41 ne za su hadu da Yesu Almasihu.”
Ya kara da cewa “Amma mahukuntan Ethiopia sun sami labarin zuwan su kasar, sai suka tare su tare da tsare su a waje guda har zuwa ranar da za a dawo da su zuw agida Uganda.”
Bayan mabiya Cocin sun fara tafiya Ethiopia ne aka sanar da gwamnatin Uganda game da abun da ke faru wa a Soroti.
Hakan na zuwa a lokacin da mahukuntan Kenya da ke makotaka da Uganda suka ciro jikkunan sama da mutane 280 da suke mambobin wata kungiya da suke azumin da ya wuce ka’ida.
Lamarin da ya girgiza kasar ya afku a yankin Kilifi da ke gabar teku.
Ana tuhumar shugabansu Paul Nthenge Mackenzie da laifuka da dama kan wannan lamari, tare da zargin sa da janyo mutuwar mabiyansa ta hanya yi musu wa’azin wai zama da yunwa ne kadai hanyar haduwa da Ubangiji.
A shekarar 2000, wasu mutane su 700 mabiya Darikar Umarnin Ubangiji 10 a Addinin Kirista sun kone kurmus a wani taron addininsu.
An rufe mambobin kungiyar da suka yi imanin duniya za ta zo karshe a karshen karni na 20.
An rufe taguna da kofofin wajen da suke, sannan sai aka bankawa dakin wuta. Lamarin ya faru a yankin Kanungu na kudu maso-yammacin Uganda.