An ga motar kwana-kwana ta daukar marasa lafiya a gaban otel din. Hoto/AFP

Somalia ta ‘kawar’ da ‘yan ta’addan Al Shabab wadanda suka kai hari wani otel da ke gefen teku a Mogadishu babban birnin kasar.

“Jami’an tsaro sun samu nasarar kawar da mayakan da suke da alhakin kai harin ta’addanci otel din Pearl Beach da ke Lido Beach,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Somalia ya ruwaito a ranar Asabar.

“An ceto farar hula da dama a lokacin samamen.”

Babu karin bayani kan adadi ko kuma wadanda suka mutu sakamakon wannan harin wanda aka soma kaiwa a ranar Juma’a.

Otel din Pearl Beach yana kan titi daya da ofishin jakadancin Turkiyya haka kuma jami’an gwamnati da dama na yawan zuwa otel din.

Wani wanda ya shaida lamarin Hassan Abdirahman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa yana wurin sayar da abinci a lokacin da aka soma kai harin.

“Na ji karar harbe-harben bindiga wadanda suka fito daga hanyar bakin teku inda karar harbe-harben ta biyo da fashewa mai kara.”

Ya bayyana cewa ya tsere inda ya ga motocin da suka lalace a kan titin.

Wani wanda ya shaida lamarin Mulki Osman ya bayyana cewa shi da abokansa sun yi sauri sun boye cikin wani kantin sayar da abinci a lokacin da suka ji karar fashewar da harbin bindiga bayan karfe 8:00.

Annobar tsaro

Wannan harin na baya-baya ya nuna yadda matsalar tsaron ta zama annoba kuma ta ki ci ta ki cinyewa a kasar da ke Kusurwar Afirka a daidai lokacin da kasar ke kokarin farfadowa daga bala’i iri daban-daban da ta sha fama da su a baya.

Bakin tekun Lido na daya daga cikin wurare da suka fi suna a Mogadishu kuma akwai hada-hadar jama’a sosai a ranakun Juma’a da dare inda ‘yan Somalia ke hutun karshen mako ta hanyar ziyartar wuraren shan gahawa da madarar kankara ta askirin.

Tuni kungiyar Al Shabab da ke da alaka da Al Qaeda ta dauki nauyin kai wannan hari. Kungiyar ta Al Shabab wadda yawanci take kai hare-hare a Somalia ta yi kaurin suna wurin kai hare-hare a otel-otel da sauran manyan wurare a Mogadishu inda akasari suke somawa da kunar bakin wake.

Kungiyar Al Shabab ta kashe masu aikin wanzar da zaman lafiya 54 na kasar Uganda a wani hari da ta kai ofishin Kungiyar Tarayyar Afirka AU a garin Bulo Marer a watan da ya gabata.

AP