An sake samun sabuwar arangama a Senegal a ranar Asabar tsakanin masu goyon bayan ‘yan adawa da kuma ‘yan sandan kasar a Dakar babban birnin na Senegal.
‘Yan sanda a kasar sun ce adadin wadanda suka rasu sakamakon zanga-zangar wadda aka soma tun a ranar Alhamis ya kai 15, lamarin da ya sa wannan zanga-zangar ta zama mafi muni a ‘yan shekarun nan.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa daga cikin wadanda suka rasu har da jami’an tsaro biyu.
Bayan an shafe yini guda tarzomar ta dan lafa, sai kuma aka koma zanga-zangar kan tituna a yammacin Asabar, inda aka rinka saka shingaye tare da kona abubuwa a gundumar HLM ta Dakar.
‘Yan sanda a wurin da kuma unguwar Ngor sun harba hayaki mai sa hawaye duk a yunkurin tarwatsa fusatattun masu zanga-zangar.
An tafka sata a wani gidan mai da kuma wan babban kanti a ranar Juma’a. Haka kuma a gundumomi da dama, akwai duwatsu warwatse kan tituna da kuma konannun tayoyi.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Felic Abdoulaye Diome ya ce an kai hari a wani gidan ruwa a kasar.
Ya bayyana cewa ana tsare da sama da mutum 500 tun bayan da aka soma irin wannan zanga-zanga a 2021.
Sai dai abin da ya jawo wannan sabuwar zanga-zangar shi ne hukuncin daurin da aka yanke wa shugaban ‘yan adawa Ousmane Sonko kan zargin fyade.
Magoya bayansa sun bayyana cewa siyasa ce ta ja aka yi masa haka.
A ranar Alhamis, an wanke shi kan zargin na fyade sai dai an same shi da bata wadda ba ta mallaki hankalinta ba inda zai shafe shekara biyu a gidan yari.
Wannan hukuncin dai zai iya hana shi takarar shugabancin kasar a zaben kasar da ke tafe a watan Fabrairu.