Ya kasance a matakin sauyi tare da mashahuri Muhammad Ali, wanda ya zamar masa wani abun koyi.
Ya jera kafada da kafada da Pele, ya dinga sharhi kan sana'ar kwallon kafa da aka dinga jefa kwallaye.
Ya bi sahu da diddigin sanannen dan kasar Kenya Kipchoge Keino tun daga lokacin da ya fara wasan tsalle-tsalle har zuwa sauyawar sa zuwa gagara-pbadau a duniya.
Tafiya ta yi tafiya, shekaru 60 tun bayan da labarinsa ya faro, dan kasar Turkiyya Orhan Ayhan mai shekara 85, na gaf da shiga tarihin kundin al'amuran ban mamaki na Guinness a matsayin mai sharhin wasanni da ya fi kowanne dadewa yana wannan sana'a a duniya.
Bulaguron Orhan na cike da ban sha'awa da karsashi, kamar yadda bakinsa ya rike sunayen gwanayen 'yan wasa shahararru.
Yana iya tuna yadda ya rikide daga mai dauko rahoto zuwa mai yin sharhi, wanda bai tsammanci faruwar hakan ba.
"Akwai sanyi sosai a wannan rana, ina iya tunawa," in ji Orhan yayin tattaunawarsa da TRT Afrika, inda yake tuno al'amuran da suka faru shekara 30 baya. "An soke tashin jirage, ga dusar kankara baje a ko ina."
Daga nesa, ana jiyo sautin magoya bayan kwallon kafa na tashi daga filin wasan kwallon kafa da ke Dolmabahce a birnin Istanbul, wanda a yanzu ake kira da Besiktas ko Vodafone Arena.
Filin na karbar bakuncin wasan daf da na kusa da na karshe na Gasar Zakarun Turai. Orhan da ya yi sana'ar ruwaito wasanni na tsawon shekara 30, a lokacin ba shi da masaniyar kaddararsa za ta sauya har abada.
"An riga an san ni a matsayin mai ruwaito wasanni, ina aiki da wata jarida da ake kira Tercuman Gazete," in ji shi. "Sun saka ni a jerin wasu masu sharhi guda hudu, wadanda dukkan su a lokacin mashahurai ne. Kawai na zaku."
Orhan bai bari zakuwarsa ta kassara shi ba, sai ya kalli wannan dama a matsayin abun da zai iya kai shi ga babban mataki.
Ya ce "An tsara kowannenmu zai yi sharhi da ruwaito wasan na mintuna 15. Ni ne na biyu, a lokacin da na fara, har shugabannin kungiyoyin ba sa son na daina. Na san abu da yawa game da kwallon kafa, ka gani - hakan ya sanya na wuce sauran!"
Farawa sannu-sannu
Fuskar Orhan na haske a lokacin da ya tuna da irin yadda ya yi nisa a wannan tafiya.
An haife shi a watan Janairun 1938, kuma babba a tsakanin 'yan uwansa uku, farkon rayuwarsa na cike da kalubale, kamar dai mahaifinsa - mai horar da 'yan wasa a wata kungiya - ya yi gwagwarmayar samun abun kula da kai.
"Na mayar da hankali wajen taimaka wa iyalina, wasanni ne hanyar hakan. Ina son duk wani abu da ke da alaka da wasanni, har da kwallon kafa, wadda ni ma na yi ta da kungiyoyin unguwata.
"Na kuma yi wasan kwallon kwando da na kokawa, wadanda ina son su duka," in ji Orhan. "Na fahimci wasanni za su taimaki rayuwata."
Shekara 60 baya, Orhan na da ma'ajiyar tunawa da bayanai inda yake da shaidar daukar rahotan wasanni sama da 15,000 a kwallon kafa da kokawa, da ma sauran nasarori.
Aikinsa ya kai shi nahiyoyi biyar don dauko bayanan manyan gasannin wasanni.
"A matsayin sa na mai son wasan kokawa, ta yaya ba za ka iya tuna ranar 30 ga Oktoban 1974 ba?" in ji shi, fuskarsa na cike da farin cikin bayar da bayani game da mashahurin "Rumble in the Jungle".
"Ga kuma sanannun 'yan wasan daga karafa masu nauyi su biyu da suke tare. Babu yadda za a yi na kubuce wa wannan wasa," yana cewa hakan game da Muhammad Ali-George Foreman.
Orhan ya je Zaire, Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a yau, don shaida wasan da ya shiga tarihi a matsayin wasan kokawa mafi shahara.
Ba wannan ne kadai abun da ya kai shi Afirka ba. "Na kuma samu damar ruwaito Kipchoge Keino, babban dan wasan tsalle-talle. Na shaida rayuwarsa ta wasanni tun yana matashi har zuwa samun daukakarsa."
Orhan ya halarci wasannin Olympics har guda shida. Muryarsa ta kuma albarkaci wasannin gasar kwallon kafa ta duniya da dama. Ya yi aiki da kusan duk wata kafar yada labarai ta Turkiyya, daga dauko rahoto da tace labarai da rubuta makalu da kuma yin sharhi tsawon shekaru.
Lokacin dadi da na wahala
Ranar 3 ga Yuni 2016, ta tsaya sosai a kwakwalwar Orhan a matsayin ranar bakin ciki ga wasanni da shi kansa. Ita ce ranar da Muhammad Ali ya rasu.
Ya ce "Ina bibiyar wannan mutum a dukkan tsawon rayuwarsa, ina kuma gina tawa da shi. Kuna kulla wata alaka. Sai ka ji kamar abokai ne ku."
A lokacin da a Phoenix, Arizona aka sanar da rasuwar shawararren dan wasan damben mai shekara 74, wani abu da ba a tsammani ba ya afku a rayuwar Orhan.
"An kira ni a waya. Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya samu labarin rasuwar Ali a cikin motarsa. Yana son sa. Ya san ni ma babban mai goyon bayansa ne. Ya tambayi mutanensa cewa su kira ni, mu tafi Amurka tare don halartar jana'izarsa."
Orhan ya bayyana wadannan a matsayin lokuta masu daci da kuma dadi. A yayin da yake murnar sanin sa da Shugaba Erdogan ya yi masa na tsawon shekaru, kuma ya ji radadin mutuwar Muhammad Ali, wanda ya tafi ya dakko rahoton jana'izar.
Kwanaki kadan baya, Orhan ya je wajen ta'aziyyar tare da tawagar shugaba Erdogan. "Shugabannin kasashe da sanannun mutane da shugabannin kungiyoyin farar hula da jaruman fina-finai.. akwai manyan mutane da yawa sun taru a wajen," in ji shi.
Kafa tarihi
A tsawon ayyukansa, Orhan ya shaida yadda aka dinga kafa tarihi. Ya ga na farko, ya ga wadanda suka fi gudu, ya ga manya-manya. ya ga labaran samun nasara, daukar kambi da matsayi, da ma kalubalen da ke tattare da harkokin wasanni.
Yanzu lokaci ne na murnar wannan nasara ta shekaru 60 a ayyukan ruwaitowa da sharhin labaran wasanni, wanda ke sanya shi zama a cikin shahararren littafin ajiye bayanai na "Guinness Book of Record", bayan marigayi dan kasar Hungary, Gyorgy Szepesi, wanda ya samu wannan kambi a 2006.
Nan da wasu 'yan watanni Orhan zai dauki wannan kambi a yayin da ya cika shekaru 61 a sana'arsa. Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ban mayar da hankali ba kan wannan abu a yanzu."
Ya kara da cewa "A shekaru na komai a yanzu albarka ne. Ina godiya ga Allah a kowacce rana idan na farka da cikakkiyar lafiya, da kuma ci gaba da yin abun da na ke so. Idan hakan na nufin na kafa tarihi, zan zama mai godiya. Bari mu ga me ya faru."
Dan gidan Orhan, Korhan Ayhan, na addu'a da ci gaba da sauraren zuwa watanni hudu da suka yi saura, da z asu do da abun da babu irin sa. An fara kirga kwanakin cika shekaru 61