Hamas ta shirya sakin duk fursunonin da ke hannunta a lokaci guda ƙarƙashin yarjejeniyar Gaza / Hoto: AA

Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025

1300 GMT — Wani babban jami'in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu a shirye take ta sako dukkan sauran mutanen da suka yi garkuwa da su a lokaci ɗaya a mataki na biyu na tsagaita wuta a Gaza.

Taher al-Nunu ya ce "Mun sanar da masu shiga tsakani cewa kungiyar Hamas a shirye take ta sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a tashi daya a kashi na biyu na yarjejeniyar, maimakon a dinga yin hakan a mataki-mataki, kamar yadda ake yi a matakin farko na yanzu."

2011 GMT — Isra'ila ta sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da ta kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da suka kai wasu yankuna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar kamfanin dillancin labaran WAFA.

Dakarun na Isra'ila sun tafi da Falasɗinawa shida a yankin Ramallah da al Bireh, a cewar kamfanin labaran.

Kazalika sun tafi da Falasɗinawa huɗu daga Jenin, ciki har da ƙananan yara biyu, kana sun ɗauke mutane uku a yankin Qalqiliya.

Ƙarin labarai 👇

0248 GMT — Lebanon ta gano gawawwakin mutane 23 bayan dakarun Isra'ila sun janye daga kudancin ƙasar

Rundunar tsaron fararen-hula ta Lebanon ta ce ta gano gawawwakin mutane 23 a wasu garuruwa da ke kudancin ƙasar bayan dakarun Isra'ila sun janye daga yakunan sakamakon yarjejniyar tsagaita wuta da aka amince da ita.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce tawagarta da ke kai ɗauki, wadda ke aiki da dakarun rundunar sojin Lebanon, ta gudanar da bincike a yankunan da lIsra'ila ta kai was hare-hare inda ta gano gawawwakin mutanen.

Tawagar ta ce ta gano gawawwakin mutum 14 a garin Meiss El Jabal, da gawwaki uku a garin Markaba, da gawawwaki uku a Kfarkela da kuma gawawwaki uku a Odaisseh.

TRT World