Hamas ta ɗage sakin fursunonin Isra'ila 'har sai baba ta gani' / Hoto: AA Archive

Litinin, 10 ga Fabrairun 2025

1602 GMT — Hamas ta yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra'ila na gaba "har sai baba ta gani".

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu ta ce an dauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra'ila ta yi.

1411 GMT — Falasdinawa ba su da 'yancin komawa gida ƙarƙashin shirin Gaza —Trump

Shugaba Donald Trump ya ce Falasdinawa ba za su sami 'yancin komawa Gaza ba a karkashin shirinsa na Amurka ta karbe yankin.

"A'a, ba za su yi ba, saboda za su sami mafi kyawun gidaje," Trump ya gaya wa gidan talabijin na Fox News Bret Baier lokacin da aka tambaye shi ko Falasdinawa za su sami 'yancin komawa.

"Wato ina maganar gina musu wuri na dindindin."

0814 GMT — Shirin Trump a kan Gaza 'la'antacce' ne — Hamas

Shugaban Hamas Khalil al Hayya ya ce shirye-shiryen Kasashen Yamma da Amurka da kuma shugaban Amurka Donald Trump a kan Gaza "tsinannen shiri ne".

"Za mu rusa su kamar yadda muka rusa ayyukan makamantan su da suka wuce," in ji shi yayin taron tunawa da zagayowar shekaru 46 na juyin juya halin Iran a Tehran.

Trump ya ce a ranar Lahadin da ta gabata ya ƙuduri aniyar sayewa da mallake Gaza amma zai iya barin wasu ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya su sake gina wasu sassan kasar da yaƙi ya ɗaiɗaita.

0938 GMT — Fadar Kremlin ta ce tana jiran karin bayani kan shirin Trump a kan Gaza

Fadar Kremlin ta ce tana jiran karin bayani kan shirin Shugaban Amurka Donald Trump na sayen Gaza, ra'ayin da ya janyo suka daga kasashe da dama.

Da aka tambaye shi ko Moscow ta amice da shirin Trump, sai kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya yi magana yana mai la'akari da mutum miliyan 1.2 da ke zaune a Gaza.

Peskov ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, "Yana da kyau a jira wasu cikakkun bayanai a nan idan muna magana ne game da wani tsari na aiki.

"Muna magana a kan Falasdinwa kusan miliyan 1.2 da ke zaune a can, kuma mai yiwuwa hakan ne babban batun," in ji Peskov.

Lahadi, 9 ga Fabrairun 2025

0717 GMT — Sojojin Isra'ila sun fara janyewa daga Netzarim da ke Gaza

Sojojin Isra'ila sun fara janyewa daga Netzarim da ke Gaza a wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Hamas.

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ruwaito cewa sojojin sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza.

Hoton tauraron ɗan’adam ya kuma nuna yadda Netzarim yake a yanzu, wani yanki na tsakiyar Gaza da sojojin Isra'ila suka fatattaki mutane bayan mamaye shi a ranar 20 ga Agusta, 2024.

0317 GMT — Jami'an diflomasiyyan Pakistan da Iran sun yi watsi da aniyar Trump kan Gaza

Manyan jami'an diflomasiyya daga Pakistan da Iran sun tattauna kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya tare da mayar da hankali kan yankin Gaza na Falasdinu, inda suka yi watsi da shawarar shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawa da zama abin damuwa da rashin adalci a cewar wata sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Islamabad ta fitar.

Ministan Harkokin Wajen Pakistan Ishaq Dar ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Iran Abbas Araghchi, inda suka tattauna halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza.

Da yake tsokaci kan shawarar Trump, Dar, wanda ke rike da mukamin mataimakin firaministan kasar, ya jaddada cewa kasar Falasdinu ta al'ummar Falasdinu ce, kuma hanya daya tilo da za ta dace kuma mai adalci ita ce samar da kasashe biyu, karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD.

TRT Afrika da abokan hulda