Sosebee ya yi watsi da kudin goro da ake yi wa wasu al'amura ta hanyar jajircewarsa, musamman ga yaran Falasdinawa a fuskar zaluncin Isra'ila na tsawon shekaru da dama. / Hoto: TRT World

A watan Janairu, Steve Sosebee, wanda aka lullube shi da keffiyeh, ya karɓi lambar yabo ta TRT ta Nasarar Rayuwa na shekaru da yawa na ayyukan jinƙai a Falasdinu.

"Ba ku kadai ba ne cikin wannan halin," in ji shi, yana nufin Falasdinawa yayin da ya karbi lambar yabo don nuna godiya ga aikinsa.

Sosebee ya yi watsi da kudin goro da ake yi wa wasu al'amura ta hanyar jajircewarsa, musamman ga yaran Falasdinawa a fuskar zaluncin Isra'ila na tsawon shekaru da dama.

A shekarar 1991, tare da marigayiyar matarsa, Huda Al Masri, ya kafa Asusun Tallafa wa Yara na Falasdinu (PCRF) don ba da kulawar jinya, agajin jinƙai, da tallafi ga Falasdinawa.

A ci gaba da aikinsa, a cikin 2024, Sosebee ya kafa HEAL Palestine, wanda ke mayar da hankali kan Lafiya, Ilimi, Taimako, da Jagoranci don taimaka wa yara da iyalai masu bukata.

Ta kokarinsa na rashin gajiyawa, ya taimaka wa yara Falasdinawa sama da 2,000 don su sami kulawar ceton rai a kan iyakokin kasa da kasa.

"Kisan kiyashi na farkar da mutane su gane me ke faruwa," in ji shi a cikin wata tattaunawa ta musamman da TRT World, yayin da yake waiwaye kan ayyukansa, wato shirin HEAL Palestine, da kuma buƙatar gaggawa ta duniya.

An gina shi shirin HEAL Palestine a kan ginshiƙai huɗu masu muhimmanci: lafiya, ilimi, taimako, da jagoranci.

Kungiyar tana ba da tallafin kula da lafiyar kwakwalwa kuma tana gudanar da wani asibiti a Gaza, tana ba da tallafin karatu ga ɗalibai, kuma tana gudanar da wuraren dafa abinci waɗanda ke ciyar da dubban mutane.

Har ila yau, tana taka muhimmiyar rawa wajen isar da kayayyakin jinya da taimakon jin kai, musamman a arewacin Gaza.

TRT World ta zanta da Steve kuma ga yadda abin ya kasance.

TRT World: Ta yaya kuka fito da manufar kafa kungiyar ba da agaji ga yaran Falasdinu?

Steve Sosebee: Na fara ziyartar Falasdinu ne a shekarar 1988. A lokacin Intifada na farko ne. A matsayinmu na ɗaliban aikin jarida, mun zagaya a Yammacin Kogin Jordan da Gaza, kuma mun sadu da iyalai kuma muka ga yadda rayuwarsu ta kasance.

Na kamu da son al'adu da mutanen yankin lokacin da na ga gagarumar gwagwarmayarsu. Wannan tafiya ta sauya rayuwata.

Da farko, na yi aiki a matsayin ɗan jarida don ilimantar da Amurkawa game da ainihin abubuwan da ke faruwa a can—hakikanin da ba a san su ba a Amurka a lokacin.

Ba na jin yawancin Amurkawa sun san tsananin mamaya da kisan ƙabilanci da ake yi.

A gare ni, rayuwa ta ɗauki hanya dabam don isa ga al'umma ɗaya. Komai ya sauya sa’ad da na shirya kula da wani ɗan’uwa da ’yar’uwa da suka ji rauni a wani harin bam a Yammacin Kogin Jordan.

Na kawo su Ohio don jinya, kuma ya yi tasiri sosai - ba kawai a gare su ba, amma ga dukan al'umma.

Al'ummar Falastinu, al'ummar Larabawa, sun yi ƙoƙarin daukar matakan cigaba wajen kula da su. Lokaci ne na haɗin kan ɗan'adam.

Mutane sun nuna tausayi kuma sun taru don sanin halin da yara ke ciki. Shi ke nan lokacin da na gane aikin jinƙai na iya zama abu mai ƙarfi don sauyin.

Wadannan yara, da a baya ba a fahimci suna cikin wadanda bala'in ke shafa ba, a yanzu halin da suke ciki ya bayyana ga mutane.

Labaran nasu sun dauki hankula. Kuma a karon farko, Amurkawa da yawa suna ganin yaran Falasdinawa a matsayin mutane - masu murmushi, dariya, masu rai, yara masu numfashi - kuma ba nau'in wulakantattun da a da suke gani ba a matsayin wadanda zai iya yin hadin gwiwa wajen aiwatar da kisan kare dangi.

TRT World: Yaya kuke kallon yadda kafafen yada labaran Yamma ke kallon Falasdinawa?

Sosebee: Sosebee: D gangan ake wulakanta Falasdinawa. Hanya guda daya tilo da za a iya aiwatar da kazamin zalunci ga yaran Gaza, ita ce idan mutane suka dauke su a matsayin ba 'yan'adam.

Kuma kafafen yada labarai sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da wannan fahimta.

Ko a yau, labaran da ake watsa na son rai ne. An ba da rahotanni iri ɗaya daban-daban ya danganta da wanda abin ya shafa, wato Isra'ilawa ko Falasɗinawa.

Kafofin watsa labarai na yau da kullum ko The New York Times ko CNN suna ci gaba da tace gaskiya tare da ƙara bincike na zahiri ga wata manufa: kashe yara ba daidai ba ne. Amma duk da haka akwai hujjar hakan a cikin manyan kafofin watsa labarai na Amurka.

Ko da yake yanayin kafofin watsa labarai sun sauya. Kuma tasoshi kamar TRT World, 'yan jarida masu zaman kansu, da masu ba da rahoto na ƙasa sun ƙyale mutane su ga ainihin gaskiya - wani abu da sauran kafafen watsa labarai ba sa tacewa ko kuma karkatarwa.

Don haka ne ake kai wa ‘yan jaridar Falasdinawa hari don nuna gaskiya. Suna cikin ainihin jaruman wannan rikicin, tare da likitoci, ma'aikatan jinya, da masu ba da amsa na farko.

TRT World: Ko akwai wani yaro ɗaya da ka yi aiki da shi wanda ya fita daban?

Sosebee: Akwai su da yawa. Amma akwai wani yaro da ya zo min a tunanina — wani ɗan shekara 11 daga Gara.

A 1991, wani bom da jirgin Isra’ila mai saukar angulu ya jefa ya sa ya rasa duka ƙafunsa da hannayensa. Kafin kafa PCRF, na tsara za a bashi kulawa a Los Angeles.

Ya koyi tafiya da kafufuwan roba, ya koma makaranta, sanna ya yi fice a wajen karatu. Hatta Bill Gates ma ya rubuta masa wasiƙar taya murna.

Baya wasu shekaru, ya koma Gaza, ya fara tara iyali sannan bai taɓa kallon kansa a matsayin nakasasshe ba.

Kullum tunaninsa mai kyau ne, koyaushe yana taimakon wasu. Mun shaku sosai, koyaushe muna aika wa juna saƙonni.

Na yi irin wannan abotar da yara da dama.

Amma tsawon watanni shida, ban ji daga gare shi ba. Ban sani ba ko yana raye. Wannan rashin tabbas ɗin yana karya min zuciya.

TRT World: Bayan ganin wahalhalu da dama, ta ya kake ci gaba da samun ƙarfin gwiwa da kuma kula da lafiyar ƙwaƙwalwarka?

Sosebee: Abu ne mai wahalar gaske. Gaza ta zama wani ɓangare na rayuwata ta daga 1988. Gaza tana da muhimmanci a wajena.

Ganinta an yi mata rugu-ruga har ta kai kusan da wuya a iya gane ta, abu ne mai tayar da hankali.

Na rasa abokai, da abokan aiki da yaran da na damu da su. Amma na ci gaba da zuwa saboda za mu iya samar da sauyi mai ma’ana.

A yanzu muna da yara 30 da aka ji musu ciwo suna samun kulawa a Amurka da ƙungiytafi ar Heal Palestine.

Mun buɗe wani asibitocin tafi-da-gidanka wanda ya kula da dubban mutane a Gaza a cikin watanni sha shida masu tsanani da suka gabata.

Mun buɗe makarantu. Mun buɗe wuraren girka abinci, mun ciyar da dubban mutane a Gaza.

Akwai takaci ka ga abin da ke faruwa, amma samun damar kawo ainihin sauyi shi ne yake ƙarfafa min gwiwa.

Ƙalubale mafi girma shi ne kasancewa cikin fata — wanda mu a matsayin mutane za mu iya taimaka wa waɗannan yaran, bayan duk abubuwan da suka gamu da shi.

Na ga yaran da suka rasa gaɓoɓi kuma suna buƙatar tiyata, sanna su girma zuwa matsa da suke kula da wasu, waɗanda suka fara tara iyali, waɗanda kuma suke cikakkiyar rayuwa. Wannan abin sa farin ciki ne.

Ganin yara suna girma zuna zama matasa da suke taimaka wa al’ummominsu — shi ne abin da yake ƙara min ƙarfin gwiwa.

Lokacin da na rasa matata ta fari, Huda Al-Masri saboda matsalar amosanin jini a 2009, na shiga mummunar damuwa.

Ina da ‘ya’ya biyu mata da zan kula da su, sannan abin da ya ƙar min ƙarfin gwiwa in ci gaba da rayuwa shi ne ganin cewa ina da wani muhimmin aiki a gabana wanda ya fi ne girma ni kai na — taimakon yaran Falasɗinawa. Wannan aikin shi ne abin da na sa a gaba.

Wasu daga cikin waɗannan yaran da na taimaka gomman shekaru da suka gabata a yanzu sun zama manya, suna da iyalai, har ma suna gudanar da kasuwanci, kuma suna taimakawa.

Irin wannan bunƙasar, da ci gaba da taimakawa suna ƙara min ƙarfin gwiwa na ci gaba da abin da nake yi, ko mai wahala kuwa.

TRT World: Ka karbi Kyauta daga TRT saboda sadaukarwar da ka yi tsawon rayuwarka. A jawabinka ka ce “Ba mu zo wajen nan don karɓar kyauta ba, sai dai don wata manufa.” Ko za ka yi mana ƙarin bayani?

Sosebee: Na yi farin ciki da aka karrama ni, amma kyauta ba ta da wani muhimmanci a nan. Taimakon mabuƙata, musamman ma lokacin kisan ƙare dangi, wani nauyi ne a kan ɗan’adam da ya kamata a ɗauke shi ba tare da jin wata isa ba, ba wai wani abu da ka yi don a karrama ka ba.

An haife ni ‘yantacce. Ban taɓa yin wata fafutuka don haƙƙoƙina ba, To amma wannan ‘yancin yana zuwa da wani nauyi na tsayawa waɗanda ba su da shi.

Waɗannan sun haɗa da Falasɗinawa, da kuma al’ummomin da ake dannewa a ƙasata, waɗanda suke fafutukar samun daidaito. Ina tare da su, ina kuma bibiyar waɗanda manufofin gwamnatocinsu suke shafarsu kai tsaye.

Amma duk da hak, batu ne na kawo sauyi mai ma’ana. Yanayin da ake ciki a Gaza ya haifar da yanayi mara daɗi — tashin hankali da karayar zuciya.

Amma shiga irin waɗannan yanayin bai isa ba. Ba tausayawarmu Falasɗinawa suke buƙata ba; suan buƙatar mu ɗauki mataki. Danna “like” a kafofin sada zumunta bai isa ba. Dole ne mu fuskantar da fushinmu zuwa aiki mai ma’ana.

Wannan ne ya sa na kafa HEAL Palestine. Idan bayan sadaukar da rayuwata ga wannan fufutuka, akwai wani abu ɗaya da na koya, shi ne wannan: za mu iya kawo sauyi, idan mun zaɓi hakan.

TRT World