Tun bayan zangon baya-bayan nan na fadan Isra'ila da Falasdinawa, Gaza take fama da karancin kayan bukata. / Hoto: Reuters

Mazauna Gaza a hankali suna komawa amfani da amalanken dabbobi don sufuri, sakamakon matsanancin karancin makamashin mai.

Tun bayan zangon baya-bayan nan na fadan Isra'ila da Falasdinawa, wanda ya barke ranar 7 ga watan Oktoba, yankin Gaza yake fama da karancin kusan duka kayan bukatun rayuwa.

Isra'ila ta ki amincewa ta bari a shiga da man fetur cikin yankin.

Mazauna Gaza suna maneji duk da kangin da kawanyar Isra'ila take musu. / Hoto: Reuters

A kudancin Gaza, a birnin Khan Yunis, takunkumin ya tilasta wa tarin mazauna yankin sun bar amfani da motoci, suka koma amfani da amalanke.

Yara ma a kan amalanke ake kai su makaranta. / Hoto Reuters

Mohammed Barbach, wani mazaunin Gaza ya ce, "Kusan an kassara sufuri gabadaya.

Abin da mutane suke yi shi ne amfani da amalanken doki don tafiya inda za su. Wannan abu ne da ba a saba ba. Muna fama da wata irin wahala da ba mu taba gani a rayuwarmu ba".

Rafat Najjar, wanda ya mallaki amalanken doki ya ce: "Ala dole muke amfani da amalanken da dabbobi suke ja don daukar fasinja a cikin Khan Yunis.

Ba mu da motoci kuma ba mu da man dizal. Ba mu da komai."

Mazauna Gaza a yanzu suna tsoron abincin dabbobin ma zai iya karewa nan kusa. / Hoto: Reuters

Kamar mutane, su ma dokuna da jakai sun fara rashin abinci da magunguna, abin da yake janyo damuwa kan karewarsu.

"A yanzu amalanke ya fi mota kima. Idan wannan yanayin ya ci gaba, ta yiwu ba za mu samu dabbobin da ke da karfin jan kaya ba," in ju Muhammad Abu Aida, shi ma wani mai amalanke da ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani abin takaicin kuma shi ne, karancin mai ya janyo asibitoci a Gaza suna fama wajen kula da marasa lafiya, da wadanda suke jikkata daga hare-haren Isra'ila.

TRT Afrika