Wata mata Bafalasdiniya tana wanke kaya a gidanta a kudancin Gaza a ranar 21 ga watan Maris din 2021. Hoto: Reuters Archive

Daga Shereena Qazi

A ranar 9 ga watan Oktoba, mutanen Gaza sun tashi da matsananciyar wahalar ruwa wadda ta shafi mutum fiye da 650,000.

Fanfunan ruwa sun daina zuba a yankin da aka yi wa kawanya jim kadan bayan da Ministan Makamashin Israel Katz ya sanar da datse musamman abubuwa kamar abinci da ruwa da kuma lantarki zuwa Gaza a matsayin wani martani ga harin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba.

Wani mazaunin Gaza Abdul Munim, mai shekara 23, ya ce lokacin da ya ji labarin, nan-take ya fara damuwa kan 'yan biyunsa maza 'yan wata shida.

"Yaya za mu samar da kwalabe idan ba mu da damar samun ruwa mai tsafta na sha?" kamar yadda Munim ya shaida wa TRT World.

Dauke wutar lantarki da Isra'ila ta yi ya sa Falasdinawa ba sa samun ruwa da sauransu.

Isra'ila ce take rike da ragamar ruwan Gaza. Yayin da aka yi wa Gaza kawanya, Isra'ila ta dakile hanyar ruwa da wajen sarrafa ruwan kwatami saboda daukewar wutar lantarki.

Kamar yadda hukumar ruwa (OCHA) wacce ita daya tilo ta rage kuma ta daina aiki a ranar 15 ga watan Oktoban saboda karanci man fetur, haka zalika sauran tsofaffin tashoshin sarrafa ruwan kwatami, abin da ke jawo karin ruwan kwatami shiga teku.

'Ba mu da zabi'

Isra'ila ta dawo da ruwa ga yankin kudancin Gaza na wani dan lokaci tsawon sa'a uku a ranar Litinin. Haka zalika kamar yadda hukumar agaji ta Majalisar Dinkin Duniya a Gaza ta ce mutum kaso 14 cikin 100 ne suka samu ruwan da aka bude.

Karancin man fetur da hare-hare ta sama ya jawo tankokin ruwa sun daina aiki, kuma ruwan roba yana karanci kuma ya yi tsada, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana. Galibin mutane suna samun ruwan sha ne daga 'yan ga-ruwa da suke amfani da hasken rana wajen tsaftace ruwan kuma ana rarraba ruwan.

Cikin zakuwa mutane suna tona rijiyoyi a garuruwan da ke gabar teku. Dubban Falasdinawa ne aka tilasta wa shan ruwan da ya gurbata kuma suna hadarin kamuwa da cututtuka da ruwa ke yadawa.

Yawancin mazauna Gaza suna dogaro ne da ruwan gishiri wanda ya gurbata da kwatami da ruwan teku. Ruwan kuma ya kunshi sinadarin Nitrates da ya samo asali daga takin zamani da kuma takin dabbobi. Akalla kaso 96 cikin 100 na ruwan ba ya shawuwa, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.

"Ba mu da wani zabi; me za ka yi? 'Ya'yana suna bukatar madara, suna bukatar abinci," in ji Munim.

"Me ya sa duniya ta yi tsit? Isra'ila ta hana mu manyan damarmakin rayuwa".

A cewar masana na Majalisar Dinkin Duniya, hana mutane ruwa laifin yaki ne saboda ya take dokokin jin kai na kasa da kasa da kuma Yarjejeniyar Geneva. Isra'ila ta yi ikirarin cewa ta dawo da ruwa a yankin kudancin Gaza da kuma bude Rafah don shigo da kayayyakin jin kai. Kamar yadda mazauna yankin suka bayyana, manyan motoci 20 ne dauke da kayan agaji ne suka shiga Gaza.

"Abin da ke faruwa a nan bai kamata a yi wa dan Adam ba, sannan kasashen duniya suna goyon bayan Isra'ila a siyance da ta fuskar karfin soja da ta kowace irin hanya," in ji Zayneb al Shalalfeh, wata jami'a a Palestinian Women Water Practitioners Network.

Al Shalalfeh ta yi bayani kan samar da ruwa inda ta ce ana samar da kaso biyar cikin 100 na bukatar ruwa da ake da shi, kuma yana ci gaba da yin kasa.

"Tashar ruwan Isra'ila ta Mekorot, tana samar wa Gaza kaso 13 cikin 100 na bukatar ruwanta ne, kimanin 53,000 m3 a kullum. Kodayake an samu tsaiko tsakanin ranar 9 ga Oktoba zuwa 15."

"Bugu da kari, akwai kamfanonin tace ruwan gishiri wanda ke samar, wanda yake karbin samar da kaso bakwai cikin 100 na ruwan Gaza, yanzu ba sa aiki. Wadannan matatun ruwa kanana suna iya tace ruwan gishiri tsakanin 18,000 zuwa 32,000 a kowace rana, amma suna bukatar lantarki da man fetur," in ji al Shalalfeh.

Ruwan roba a kasuwa zai karu. Farashin ruwan roba zai karu sosai, abin da zai sa iyalai masu matsakaicin karfi a Gaza ba za su iya saya ba.

Ruwa – wani makami na nuna karfin iko

A tarihi, karfe iko da ruwa ya kasance wani salo na masu mulkin mallaka don korar mutane daga kasarsu. An yi amfani da wannan salo a Gabar Yammacin Kogin Jordan, wanda Isra'ila ta mamaye tun shekarar 1967.

Kodayake an kafa yarjejeniyar Kwamitin Joint Water a shekarar 1995 tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, Isra'ila tana da iko cewa a'a kan shirin samar da tashar ruwa ta Falasdinawa. Babu iyaka kan adadin ruwan da Isra'ila za ta yi amfani da shi daga kasar da ta mamaye.

"Isra'ila ce take da iko da kaso 80 cikin 100 na albarkatun ruwa a Gabar Yammacin Kogin Jordan, kuma kamar yadda Yarjejeniyar Oslo ta tanada, ruwa zai ci gaba da kasancewa karkashin ikon Isra'ila," in ji Abdelrahman Tamimi, darakta a Palestinian Hydrology Group kuma malami a Jami'ar Arab American.

Tamimi ya yi karin bayanin cewa Bayahude dan kama wuri zauna a Gabar Yammacin Kogin Jordan yana amfani nunki shida na ruwan sha idan aka kwatanta da 'yan Falasdinu, lita 350 ga kowane mutum a kowace rana, yayin da Falasdinawa kowane mutum yana samun lita 60 ne a kowace rana, idan aka raba adadin ruwan da ake ba ta da yawan mutanenta.

"A tsawon shekara 55 na mamayar Isra'ila a Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza, Isra'ila ce take da iko da ruwan koguna da na karkashin kasa kuma ta hana bunkasa kamfanonin da matatun ruwan Falasdinawa, kuma tana amfani da albarkatun ruwa a Gabar Yammacin Kogin Jordan ga Yahudawa 'yan kama wuri zauna."

A Gaza, Munim ya bayyana yanayin da 'gudun yada kanin wani'.

"Idan karancin ruwa a jiki da yaduwar cutuka da gubataccen ruwa bai kashe ka ba, hare-hare ta sama zai kashe ka, saboda haka ina bakin kokari don kare iyalina da kuma tsira," in ji shi.

"Idan gurbataccen ruwa ya taimaka mana muka rayu yanzu, babu damuwa za a sha. Ba mu da wani zabi."

TRT Afrika