Marie Mutsuva: Matar da ta zama uwar marayun da yaki ya kashe iyayensu a DRC

Marie Mutsuva: Matar da ta zama uwar marayun da yaki ya kashe iyayensu a DRC

Matar, mai shekara 73, ta zama baya mai goya marayun da suka rasa iyayensu a yankin da yaki ya daidaita.
Marie Mutsuva ba ta taba yin aure ba / TRT Afrika

Marie Mutsuva ba ta taba yin aure ba, kuma ta ki yin auren ne tun lokacin da aka gano tana da wata lalura da ba za ta bar ta ta haihu ba.

Bayan shekaru masu yawa ne sai dattijuwa Mutsuva mai shekara 73 ta zama uwar gwamman yaran da yaki ya yi sanadin mutuwar iyayensu a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo.

Tun shekarar 2014 kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce, kungiyar masu tayar da kayar baya ta Allied Democratic Force (ADF) wacce Daesh ta bayyana a matsayin reshenta a tsakiyar Afirka, ta kashe fiye da mutum 4,000.

A yanzu dattijuwa Mari Matsuva ta zama baya mai goya marayun yaran da aka kashe iyayensu a rikicin. Kuma gidanta da ke birnin Beni ya zame musu wata mafaka ta samun nutsuwa.

“Yanzu shekara 43 kenan da na fara taimako da goya marayun yara, bayan da aka ce min ba zan taba iya haihuwa ba,” Mutsuva ta shaida wa TRT Afirka.

“A yanzu haka akwai yara marayu 58 da nake goyawa kuma da yawansu sun fito ne daga yankunan da ‘yan tawayen ADF suka kashe iyayensu.”

Fafutukar yau da gobe

Mutsuva kan tashi ne tun karfe 5 na asubahin kowace rana don ta shirya wa yaran abinci, wadanda suke ‘yan tsakanin wata tara zuwa shekara 18.

Tana tafiyar da harkokin kula da marayun nata ne da tallafin da take samu na kudi da kayayyaki daga abokan arziki.

Duk da cewa sai ta yi fafutuka wajen samar musu abubuwan bukatar rayuwa, amma Mtsuva ta ce farin cikin da take ji a kullum idan yaran na kiranta da “maman, maman…” kadai ya ishe ta gamsuwa da kuma ladan wahalarta.

“Muna shan wahalar samun abinci, da kula da lafiya da biyan kudin makaranta har ma da samun isasshen wajen bacci cikin nutsuwa,” ta ce.

“Gidan marayun nawa girmansa bai fi ya dauki mutum 20 ba kacal amma a yanzu haka ina da mutum 58… kuma za mu ci gaba da samun karin yaran idan har aka ci gaba da yakin nan.”

Mutsuva ta yi kokarin gano dangin yaran nan amma abin ya ci tura.

Wani gidan rediyo a garin yana ba ta dama ta yi magana a wani shiri sau daya a wata, inda take fadar sunayen yaran da take rikon da kuma wasu bayanai da ta sani a kansu.

Tun watan Satumban shekarar 2017 da aka gano dangin wata yarinya, ba a samun irin hakan ba.

“Na samu wata yarinya ‘yar shekara uku daga garin Eringeti mai nisan kilomita 69 daga Beni,” Mustuva ta ba da labari. Mako daya bayan nan, ta yi hira da gidan rediyon, “sai wata innar yarinyar ta kira ni, sai aka sada yarinyar da danginta.”

Sai dai kuma su ma yaran ba su damu da son ganin sun koma ga danginsu ba muddin dai suna hannun Mutsuva cikin kulawa da kuma soyayya.

“Ina jin kwarin gwiwa… don ina ci gaba da karatuna, don haka ina godiya ga uwata Marie Nutsuva,” a cewar Glory Somana mai shekara 14, a hirarsa da TRT Afirka.

“Nan gidanmu ne… dukkan marayun nan ina daukar su a matsayin kanne da yayyena. Idan na kammala karatu, zan taimaka wa Mama Marie wajen inganta rayuwar marayun,” a cewar matashin.

Alheri gadon bacci

Ga duk wanda ya san Mutsuva, ya san gwarzuwa ce kuma suna fatan gwamnatin Kongo za ta taimaka mata wajen ciyar da yaran da biyan kudin karatunsu da na kula da lafiyarsu.

Ko ni da iyalaina ba su da yawa da kyar nake ciyar da su amma ita tana daukar nauyin yara har 58… Allah Ya kara mata tsawon rai don ta cimma burinta,”in ji Muhindo Nzala, wani makwabcin Mutsuva.

Shi ma wani mai magana da yawun runduar sojin Kongo, Kaftin Antony Mwalushayi irin wannan ra’ayin ne da shi.

“Ya zama wajibi gwamnatin Kongo ta tallafa wa Mama Marie da abinci da magunguna saboda jarumar mace ce wacce take inganta rayuwar marayun da suka rasa iyayensu.

“Mata irin Marie Mutsuva, ina daukar su tamkar wasu wakilan mala’iku,” in ji Kaftin Mwalushayi a hirarsa da TRT Afirka.

“Sojojin Kongo na iya bakin kokarinsu wajen kawar da kungiyoyin masu tayar da kayar baya don yankin ya zauna lafiya. Wadanda wannan yaki ya fi tagayyarawa su ne mata da yara da ba za su iya tseratar da kansu ba a yayin hare-haren.”

A yayin da ake ci gaba da rikicin, yara na kara shiga cikin matsin lamba da fadawa bala’in da masu ta da kayar bayan suka jawo.

A ranar 22 ga watan Janairu, a kalla yara biyar ne suka rasa rayukansu daga cikin mutum goman da suka mutu sanadiyar wani harin bam da aka tayar a cocin Pentecostal a Kasindi da ke gabashin Kongo.

Wakiliyar Asusun Tallafa wa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF a Kongo, Grant Leaity ta ce a cikin wata sanarwa: “rikicin baya-bayan nan ya munana sosai kuma ya nuna yadda lamarin ke sake saka yara cikin halin ha’ula’i.

“Likitoci a babban asibitin Kasindi sun ce a kalla yara 16 ne suka ji rauni a harin bam din, kuma shida daga cikinsu munanan raunuka suka samu.”

Ta kara da cewa a kalla yara 40 ne suka rabu da iyalansu a rikicin wanda ya sa dumbin mutane yin gudun hijira a yankunan Djugu da Mahagi da kuma Aru.

“A yayin da muke yin Allah wadai da duk wani rikici da ke shafar yara, ba za mu daina aiki tukuru ba don ganin mun kare su da iyalansu,” a cewar Leaity

TRT Afrika